Gwamnati ta karyata Lauyanta inda tace duka wadanda aka kama kananan yarane kuma za’a binciki jami’an tsaron da suka kamasu dan yi musu hukunci
Gwamnatin tarayya ta musanta ikirarin lauyanta da yace wadanda aka kai gaban kotu a Abuja ba yara bane.
idan dai ba'a mantaba a baya lauyan gwamnatin yace wasu ma daga cikin wadanda aka gurfanar na da aure wasu sun kammala jami'an, lamarin da ya jawo cece-kuce.
Saidai a sabuwar sanarwar da ministan yada labarai, Mohammed Idris ya fitar yace shugaba Tinubu yace a dakatar da duk wata shari'a da ake akan yaran a sakesu.
Sannan kuma yace dukansu yarane.
Yace za'a binciki duka jami'an tsaron dake da hannu a lamarin dan ganin ko akwai wanda ya aikata ba daidai ba dan a hukuntashi.
Sannan shugaban kasar ya bayar da umarnin kula da yaran da kuma mikasu hannun iyayensu da masu kula dasu cikin aminci.