Saturday, January 18
Shadow

Duk Labarai

Gwamnonin Arewa sun bukaci gwamnatin tarayya ta saki kananan yara da aka kama ake zargi da cin amanar kasa

Gwamnonin Arewa sun bukaci gwamnatin tarayya ta saki kananan yara da aka kama ake zargi da cin amanar kasa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kano dana Bauchi da kungiyar Dattawan Arewa ta ACF sun nemi gwamnatin tarayya ta saki kananan yara da ake zargi da cin amanar kasa. Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf tuni ya baiwa babban lauyan jihar umarnin daukar mataki akan lamarin. Hakanan kuma A bangaren gwamnan jihar Bauchi shime ya bayyana takaici da abinda ya faru. Suma bangaren dattawan Arewa na ACF sun nemi gwamnati data saki yaran da gaggawa sannan kuma ta yi bincike kan tsaresu da aka yi ba bisa ka'ida ba.
Wani Kamfanin mai daga kasar waje ya zo kusa dani ya kama hayar matatar man fetur dan ya rika tace man fetur da bashi da inganci>>Dangote

Wani Kamfanin mai daga kasar waje ya zo kusa dani ya kama hayar matatar man fetur dan ya rika tace man fetur da bashi da inganci>>Dangote

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Matatar man Dangote ta koka da cewa wani kamfani daga kasar waje ya kama hayar guri a kusa da ita dan ya rika tace man da bashi da inganci. Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin me kula da Sadarwa na matatar ta Dangote, Anthony Chiejina inda yace hakan kamar zagon kasa ne garesu su da suke kokarin yin abu dan ci gaban Najeriya. Matatar ta Dangote ta bayyana cewa a irin wannan yanayi yawanci kasashe kan dauki mataki na ganin ta baiwa kamfanonin ta na cikin gida kariya. M...
Babu Mutumin Da Yake Da Ikon Hargitsa Mana Kasa Saboda Gwamnati Ta Cire Tallafin Man Fetur, Cewar Dr Jalo Jalingo

Babu Mutumin Da Yake Da Ikon Hargitsa Mana Kasa Saboda Gwamnati Ta Cire Tallafin Man Fetur, Cewar Dr Jalo Jalingo

Duk Labarai
Babu mutumin da yake da ikon hargitsa mana Kasa a Shari’ance saboda Gwamnati ta cire tallafin man petur, ko saboda hauhawar farashin kayayyaki, ko saboda tsadar rayuwa, ko saboda ba dan Arewa ba ne yake yin mulki, ko saboda ba wanda yake so ba ne yake yin mulki, ko saboda hauhawar jahìĺçìnsa a fùskar addini. Masu rinjaye cikin ‘yan Nijeriya suna da ikon kawar da mulkin APC a zaben 2027, kamar yadda suka taba kawar da mulkin PDP a 2015, wannan kuma ba wani abu ba ne sabo a irin wannan tsarin mulki da wannan Kasa tamu take kansa. Muna kara nanata cewa sam ba daidai na a samu wasu sakarkaru cikin samari su karya doka da oda su wulakanta ramzin Kasa, ko su lalata dukiyar Gwamnati, ko su lalata dukiyar daidaiku, sannan kuma hukuma ta kama su domin hukunta su, sai kuma a samu wasu da za su...
20 daga Yaran da Gwamnatin tarayya ke tsare dasu bisa tuhumar cin amanar kasa zun kwanta rashin lafiya

20 daga Yaran da Gwamnatin tarayya ke tsare dasu bisa tuhumar cin amanar kasa zun kwanta rashin lafiya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa akalla 20 daga cikin yaran da gwammatin tarayya ke tsare dasu bisa zargin cin amanar kasa sun kwanta rashin lafiya. Rahoton yace tuni aka garzaya da yaran zuwa Asibiti. Tun da fari dai da aka kai yaran gidan yarin Kuje dake Abuja,hukumomin gidan yarin sun ki amincewa su ajiyesu. Hakan yasa dole hukumar 'yansandan Najeriya suka koma suka ci gaba da tsare yaran a inda suke tsare da manyan mutane. Zuwa yanzu dai ba'a san wane asibitine aka kai yaran dan kulawa dasu ba. Shuwagabannin zanga-zangar Take it back Movement dai sun je dan kaiwa yaran abinci da kayan sawa amma sai guda 6 kawai suka tarar a tsare inda aka sanar da su cewa sauran suna Asibiti. A baya dai hutudole ya kawo muku cewa, shugaban 'yansandan Najeriya yace faduwar da yaran suka yi a...
Dole sai mun dauki matakai na shan wahala kamin a samu gyara a kasarnan>>Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu

Dole sai mun dauki matakai na shan wahala kamin a samu gyara a kasarnan>>Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan ci gaban yankunan kasarnan, Abubakar Momo ta bayyana cewa dolene sai Gwamnatin ta dauki matakan shan wahala kamin a samu warware matsalolin kasarnan. Ministan yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana nufin Najeriya da Alherine. Ya bayyana hakane a Akure wajan kaddamar da rabon kayan tallafi ga jihohin Yankin Naija Delta. Ministan yace kwanannan za'a ga amfanin gyare-gyaren da gwammatin Tinubun ke kawowa. Yace idan dai ana son kawo gyara sai an dauki matakan shan wahala tukuna.
Ji Sautin Murya dake alamta cewa Hukumar ‘yansanda ta jihar Kano ce ta kama yarannan da aka kai Kotu a Abuja sannan kuma Gwamnatin jihar Kano ma tasan da maganar

Ji Sautin Murya dake alamta cewa Hukumar ‘yansanda ta jihar Kano ce ta kama yarannan da aka kai Kotu a Abuja sannan kuma Gwamnatin jihar Kano ma tasan da maganar

Duk Labarai
Wani sautin muryar Rahoton BBC ya bayyana da ya ruwaito kakakin 'yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa na cewa sun kama mutane 76 sun kaisu Abuja saboda cin amanar kasa ta hanyar daga tutar kasar Rasha yayin zanga-zangar yunwa. Idan dai ba'a manta ba, jimullar mutanen da aka kai kotu ranar Juma'ar data gabata 76 wanda daga cikinsu 32 kananan yara ne. Hakanan a cikin Rahoton na BBCHausa an ji muryar kwamishinan Shari'a na jihar Kano yana tabbatar da cewa suna sane da kama wadannan yara. https://twitter.com/jarmari01/status/1852792794475061401?t=oLLGzdsy6cc-uFDh2TMihQ&s=19 Lamarin gurfanar da wadannan yara a gaban kotu dai ya dauki hankula a ciki da wajen Najeriya inda akaita Allah wadai. Zuwa yanzu dai Babban Lauyan gwamnati ya karbi maganar shari'ar yaran kuma ana t...
Kalli Bidiyo: ‘Yansanda sun kama ‘yan kasar China 80 suna ayyukan damfarar yanar gizo a Abuja

Kalli Bidiyo: ‘Yansanda sun kama ‘yan kasar China 80 suna ayyukan damfarar yanar gizo a Abuja

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na cewa, hukumomin 'yansandan Najeriya sun kama 'yan kasar China 80 suna laifukan damfarar yanar gizo. A wani Bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga yanda aka kama 'yan kasar ta China da yawa. https://twitter.com/dipoaina1/status/1852988641968009268?t=0Sep3Y_JEQLY_OUapdGZ_A&s=19 An kuma kwace kwamfutoci da wayoyi da dauransu.
Tinubu dan uwanmu ne Bayerabe mun fi kowa sanin halinsa shiyasa bamu zabeshi ba a zaben 2023>>Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta magantu

Tinubu dan uwanmu ne Bayerabe mun fi kowa sanin halinsa shiyasa bamu zabeshi ba a zaben 2023>>Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta magantu

Duk Labarai
Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta magantu kan salon mulkin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke yi a Najeriya. Kungiyar tace salon mulkin na Tinubu da tsare-tsare na mugunta sun sa mutane miliyan 14 sun tsunduma a cikin talauci a gwamnatinsa. Kungiyar tace a shekarar 1999 ta goyi bayan Bola Ahmad Tinubu ya zama gwamnan Legas kuma ta ga irin salon mulkinsa dan hakane yasa tace babu dalilin da zai sa da ya fito takarar shugaban kasa ta goyi bayansa. Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban kungiyar ta Afenifere Ayo Adebanjo, ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Justice Faleye. Kungiyar ta kuma yi kira ga Tinubu da ya gyara nuna fifiko da yakewa Yarbawa wajan bayar da mukaman gwamnati a mulkinsa.