Da Duminsa: Gwamnonin Arewa zasu Gana a Kaduna game da matsalar tsaron da ta addabi yankin
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Arewacin Najeriya zasu gana a Kaduna saboda tattaunawa matsalar tsaro da ta addabi yankin.
Rahoton yace hadimin gwamnan jihar Gombe, Ismaila Misilli ne ya bayyanawa manema labarai na Punchng hakan inda yace gwamnan Gomben shine ya kira wannan taron a matsayinsa na shugaban Gwamnonin Arewan.
Yace idan dai ba an canja ba, a yau, Asabar ne za'a yi wannan taro a Kaduna kuma matsalar tsaron yankin ce babban abinda za'a tattauna.








