Saturday, May 9
Shadow

Duk Labarai

Legas da Kanone kan Gaba wajan yawan masu rijistar NIN

Legas da Kanone kan Gaba wajan yawan masu rijistar NIN

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa jihohin Legas da Kano ne kan gaba wajan yawan masu rijistar katin zama dan kasa NIN. Yawan wanda suka yi rijistar a Najeriya sun kai Miliyan 118.4. Legas ce kan gaba wajan yawan masu rijistar inda take da mutane miliyan 12.7 da suka yi rijistar. Sai kuma jihar Kano ta zo ta biyu inda take da mutane miliyan 10.4 kamar yanda hukumar kididdigar kasa ta NBS ta bayyana. Kaduna ce ta zo ta 3 da mutane miliyan 6.9 da suka yi rijista. Sauran jihohin na da mutanen da suka yi rijista kamar haka: Ogun mutane 4.9 million Oyo Mutane 4.5 million Katsina Mutane 4 million FCT Mutane 3.8 million Rivers 3.5 million Delta 3.2 million Jigawa 3.1 million. Imo 2 million Kwara 2 million Enugu 1.9 million Kogi 1.9 million Yobe 1.8 mill...
Gwamna Bago ya janye matakin da ya ɗauka akan samari masu tara gashin dada a Neja

Gwamna Bago ya janye matakin da ya ɗauka akan samari masu tara gashin dada a Neja

Duk Labarai
Gwamna Bago ya janye matakin da ya ɗauka akan samari masu tara gashin dada a Neja. Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya janye umarninsa na baya da ya bayar ga jami’an tsaro da su kama masu gashin dada da maza masu Kitso a Minna, babban birnin jihar. Bago, yayin da yake magana a wani taron tsaro tare da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati ranar Talata, ya umarci jami’an tsaro da su yanke gashin dada na mutanen da aka kama tare da cin tarar kudi. Ya ce: “Duk wanda kuka gani da Gashin Dada, ku kama shi, ku yanke masa gashi, sannan ku ci shi tara. “Babu wanda zai rika yawo da irin wannan gashi a cikin Minna. Na riga na ba da umarni ga jami’an tsaro,” in ji gwamnan. Sai dai a ranar Laraba, gwamnan ya janye wannan umarni bayan ya fuskanci suka daga 'yan Najeriya da dama. Yayin...
Kalli Bidiyo: Wata Sabuwar Masifa ta Shigo kafafen sada zumuntar Arewa inda ake cin zarafin malamai ta hanyar Amfani da AI asa su yi rawa

Kalli Bidiyo: Wata Sabuwar Masifa ta Shigo kafafen sada zumuntar Arewa inda ake cin zarafin malamai ta hanyar Amfani da AI asa su yi rawa

Duk Labarai
Wata sabuwar masifa da ta shigo kafafen sada zumuntar Arewa itace ta amfani da wani AI ana saka hotunan malamai ana sawa su yi rawa. Wannan AI a baya 'yan siyasa kawai akewa amfani dashi amma yanzu lamarin ya kai har kan malamai. https://www.tiktok.com/@sanusi_lauwali/video/7494342086968462647?_t=ZM-8vmO2enRDGw&_r=1 Wasu daga cikin Malam da muka ci karo an yi Amfani da wannan AI din an sa sun yi rawa sun hada da Marigayi Shaikh Jafar Adam, da Sheikh Bala Lau da Sheikh Maqari. https://www.tiktok.com/@sanusi_lauwali/video/7495429012479659319?_t=ZM-8vmO9SppUg9&_r=1 Wani abin takaici ma shine lamarin ya koma gasa tsakanin matasa mabiya akidu, idan wannan ta saka malamin wannan akida rawa, sai shima wancan ya rama. https://www.tiktok.com/@sanusi_lauwali/video/7494...