Saturday, February 21
Shadow

Duk Labarai

‘Yar Haya ta fasawa me gida kai bayan da ya bata notice na tashi

‘Yar Haya ta fasawa me gida kai bayan da ya bata notice na tashi

Duk Labarai
Wata mata dake zaune a gidan haya ta fasawa me gida kai bayan da ya bata notice ta tashi daga gidansa. Me gidan wanda matashine kuma marayane ya bukaci matar ta tashi. Lamarin ya farune a garin Umugbabe Ovoko dake karamar hukumar Igbo-Eze ta jihar Enugu. Wani dan jarida daga jihar ne me suna, Chijinkem Ugwuanyi ya bayyana hakan inda yace tuni jami'an 'yansansa sun kama matar da 'ya'yanta 2.
Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargadi ga ‘yan Najeriya bayan da aka samu bullar cutar Ebola A kasar Uganda

Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargadi ga ‘yan Najeriya bayan da aka samu bullar cutar Ebola A kasar Uganda

Duk Labarai
Hukumar kula da cutuka ta kasa, NSCDC ta bayyana gargadi ga 'yan kasa bayan da cutar zubar da jini, Ebola ta sake bayyana a kasar uganda. Shugaban hukumar ta NCDC, Jide Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar. Cutar Ebola dai tana yaduwa ne a tsakanin Al'umma ta hanyar taba jikin me ita ko jininsa ya taba naka ko sauran ruwan dake fita daga jikin dan Adam. Jide Idris yace duk da yake cutar bata kai ga zuwa Najeriya ba amma suna kokarin ganin bata shigo kasar ba inda suka hada hannu da hukumomin da abin ya shafa.
Dan Allah kada ku sake zaben jam’iyyar PDP ta shugabanci Najeriya>>Jam’iyyar APC ta roki ‘yan Najeriya

Dan Allah kada ku sake zaben jam’iyyar PDP ta shugabanci Najeriya>>Jam’iyyar APC ta roki ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta bayyana Jam'iyyar hamayya ta PDP da cewa Jam'iyya ce wadda aka kusa mantawa da ita saboda irin rikice-rikicen da Jamhuriyar ke fama dasu na cikin gida. APC ta yi roko ga 'yan Najeriya da cewa, kada su bari PDP ta dawo kan mulki musamman saboda la'akari da irin lalata kasarnan da suka yi a shekaru 16 da suka yi suna mulki. Me magana da yawun Jam'iyyar ta APC, Bala Ibrahim ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da jaridar Punchng inda yace har yanzu barnar da PDP tawa Najeriya bata kare ba. Jam'iyyar bata iya gudanar da komai ba hadda ma gudanar da kanta kamar yanda Bala Ibrahim ya fada inda yace abin dariya yake basu a APC.
An yiwa dan shekaru 60 tiyata dan ciro hodar IIbliss da ya hadiya dan kaiwa kasar waje a biyashi

An yiwa dan shekaru 60 tiyata dan ciro hodar IIbliss da ya hadiya dan kaiwa kasar waje a biyashi

Duk Labarai
Dan Najeriya, Chijioke Igbokwe me shekaru 59 da yayi ikirarin yin kasuwancin Sayar da kaya an kamashi da hadiyar daurin hodar Iblis har guda 81. Ya hadiyi wannan kwayane da niyyar kaita kasar Lebanon inda aka masa alkawarin idan ya kai za'a bashi dala $3000. Saidai an yi sa'a hukumar NDLEA ta kamashi inda kuma ya kasa yin kashin daurin da ya hadiya kamar yanda aka saba. Sai da ta kai ga an yi masa tiyata aka samu ciro guda 57 daga cikin 81 daya hadiya. Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana haka inda yace sun ajiye mutumin tsawon kwanaki 5 amma dauri 24 kadai ya iya yin kashinsu daga cikin 81 da ya hadiya wanda hakanne yasa dole aka yi masa tiyata.
Ku shirya zamu kara kudin wutar lantarki>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa ‘yan Najeriya

Ku shirya zamu kara kudin wutar lantarki>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya tace tana shirye-shieryen kara kudin wutar lantarki nan da wasu watanni kadan masu zuwa. Me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar makamashi, Olu Verheijen ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da kafar Bloomberg a birnin Darussalam na kasar Tanzania. A shekarar data gabata dai, an kara kudin wutar nunki 3 ga wadanda suke kan tsarin Band A na wutar.
Kalli Bidiyo yanda ‘yan Bìndìgà da suka tuba suka koma zikiri da salatin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)

Kalli Bidiyo yanda ‘yan Bìndìgà da suka tuba suka koma zikiri da salatin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)

Duk Labarai
Shugaban 'yan Bindiga me suna Kachalla Bugaje ya bayyana a baya cewa, ya tuba daga yin garkuwa da mutane inda yace mutane guda 50 da yayi garkuwa dasu, ya sakesu ba tare da karbar kudin fansa ba. Bayan nan ne kuma aka ganshi yana jagorantar mayakansa suna zikiri da salatin Annabi. Bugaje ya bayyana nadama sosai bisa abinda ya aikata tare da jawo hankalin sauran shuwagabannin 'yan Bindiga da su ajiye makamansu su koma ga Allah. Ganin bidiyon har yanzu da makamai a hannunsu shi da yaransa yasa da yawa suke zargin cewa ba da gaske yake maganar ajiye makaman ya daina yaki ba. Kalli Bidiyon anan
Subhanallahi kalli Bidiyo: Duk da kkashe na farko da aka yi, an kara samun wasu sun yi bikin kona Qur’ani a kasar Ingila

Subhanallahi kalli Bidiyo: Duk da kkashe na farko da aka yi, an kara samun wasu sun yi bikin kona Qur’ani a kasar Ingila

Duk Labarai
Biyo bayan kashe Salwan Momika da ya kona Qur'ani a bainar jama'a, an sake samun wasu da yawa sun sake kona Qur'anin inda suka rika saka hotunan wannan lamari a shafukansu na sada zumunta. Wani me sunan DigitalVagrant a kafafen sada zumunta ya bayyana cewa, zai maye gurbin Salwan Momika inda ya fita fili ya kona Qur'ani a Manchester dake kasar Ingila. Tuni dai mahukunta a birnin suka kamashi saboda yunkurin kawo fitina. Akwai da yawa da ake samu suna cin zarafin addinin Musulunci ta hanyoyi daban-daban dan tsananin nuna kiyayya.
Bana munafurci a siyasa>>El-Rufai

Bana munafurci a siyasa>>El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, baya munafurci a siyasa. El-Rufai bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yake martani ga wani da yace ya karanta littafinsa na accident civil servant kuma ya fahimci cewa, El-Rufai bai iya munafurci ba. El-Rufai ya tabbatar da hakan inda yace bai iya wasan kwaikwayo irin na 'yan film ba.
Da Duminsa: Matatar Man fetur din Dangote ta rage farashin man

Da Duminsa: Matatar Man fetur din Dangote ta rage farashin man

Duk Labarai
A wani yanayi da zai iya kawo sauki ga matsin rayuwa musamman ga talakawan Najeriya, Matatar man Dangote ta rage farashin litar mai da ake dauka a Depot daga Naira 950 zuwa Naira 890 akan kowace lita. Matatar man ta ce ta rage kudinne saboda saukar farashin danyen man fetur a Kasuwar Duniya. Me magana da yawun matatar man fetur din, Anthony Chiejina ne ya bayyana haka inda yace kamar yanda a ranar 19 ga watan Janairu da ya gabata suka kara farashin litar man fetur din saboda tashin farashin danyen man fetur din hakanan a yanzu tunda farashi ya sauka shine suma suka rage farashin. Matatar tace wannan rage farashin zai kawo saukin hauhawar farashin kayan masarufi da saukin rayuwa a tsakanin 'yan Najeriya.
Kalli Yadda Gwamna Zulum Ke Rushe Gidajen Talakawan Jihar Bornon

Kalli Yadda Gwamna Zulum Ke Rushe Gidajen Talakawan Jihar Bornon

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Abunda Gwamna Zulum yake yi wa talakawan jihar sa na rushe gidajen su sam bai dace ba koda kuwa local dillalai ne suka cuce su na saida musu filayen da bana su ba. Na tabbata akwai wadanda da yawa ba su da masaniyar yadda abun yake kuma hakan zai iya zama silar talaucewar mutane da yawa. Ya kamata Gwamnatin jihar ta kama dukkannin dillalan da suka cuci al'umma domin su biya wa 'yanda suka saidawa wurin hakkokinsu, haka zalika Gwamna Zulum shima ya ragewa wa 'yanda hakan ya shafa ...