Sunday, January 19
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo: An kama barawon Akwatin zabe a kasar Amurka

Kalli Bidiyo: An kama barawon Akwatin zabe a kasar Amurka

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} An kama wani dan kasar Amurka, Larry Savage saboda zargin satar kuri'a da lalata kuri'ar da cin amanar kasa. Larry Savage dan takara majalisar tarayyar Amurka ne daa Indiana saidai bai ci zaben ba. Lamarin ya farune a yayin da aka gudanar da zaben gwaji a Madison County dake Indiana. An tara kuri'u ana shirin zabe sai aka ga babu guda biyu, ko da aka duba kyamara sai aka hango Larry ya saka kuri'un guda biyu cikin aljihunsa. Larry ya sace kuri'un ne baya...
Ji yanda ta kaya bayan da Sanata ya cewa daya daga cikin ministocin da suke tantancewa tana da kyau

Ji yanda ta kaya bayan da Sanata ya cewa daya daga cikin ministocin da suke tantancewa tana da kyau

Duk Labarai
Sanata Osita Ngwu dake wakiltar mazabar Enugu West a majalisar dattijai ya yabi kyawun Bianca Odumegwu-Ojukwu wadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aike da sunanta majalisar dan a tantance ta a matsayin karamar Ministar harkokin kasashen waje. A yayin da ya tashi zai mata tambaya, ya fata cewa kyakkyawa, Bianca. Nan take kuwa kakakin majalisar, Godswill Akpabio ya taka masa burki inda yace ya daina yabon kyawunta dan babu inda ta rubuta cewa ita kyakkawan ce a cikin takardunta. Hakan yasa an fashe da dariya a majalisar.
Shugaba Tinubu ya nada shugaban sojoji na rikon kwarya

Shugaba Tinubu ya nada shugaban sojoji na rikon kwarya

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa. Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da riƙe muƙamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai koma ƙasar. Kafin naɗa shi a muƙamin, Oluyede ne kwamandan runduna ta 56 da ke Jaji a jihar Kaduna. Tun a makon da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa Janar Lagbaja yana jinya a wani asibiti a ƙasar waje bayan ta musanta rahotonnin da ke cewa ya rasu, tana mai cewa Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim ne ya maye gurbinsa a matakin riƙon ƙwarya. Daga baya hedikwatar tsaro ta Najeriya ta musanta batun, inda ta ce "babu wani batun muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa" a tsarin aikinta.
Kalli Bidiyon yanda aikin gyaran wutar lantarkin Arewa ke gudana

Kalli Bidiyon yanda aikin gyaran wutar lantarkin Arewa ke gudana

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana da ya nuna yanda ake ta kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace. Yau Kwanaki 10 kenan cif ba wutar lantarki a Arewa bayan da wasu bata gari suka lalata wutar. Lamarin ya jefa jihohi da yawa a yankin cikin duhu sannan ya sanya mutane da yawa tafka asara ta miliyoyin kudade a wasu Rahotannin ma har rayuwa an rasa. https://twitter.com/DOlusegun/status/1851505945152549093?t=hQXXb7qapmDDPO_IyFYxAw&s=19 Hukumar TCN dai tace ranar Lahadi 3 ga watan Nuwamba za'a kammala gyaran wutar lantarkin.
Kotu ta hana CBN baiwa jihar Rivers rabonta na kudaden shiga daga gwamnatin tarayya

Kotu ta hana CBN baiwa jihar Rivers rabonta na kudaden shiga daga gwamnatin tarayya

Duk Labarai
Babbar Kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta hana babban bankin Najeriya, CBN ci gaba da turawa jihar Rivers kudadenta na shiga da gwamnatin tarayya ke aikawa kowace jiha. Mai Shari'a, Joyce Abdulmalik ce ta yanke wannan hukunci bisa dalilin cewa gwamnan jihar Sim Fubara baya bin doka wajan kashe kudaden da ake turawa jihar. Dan hakane tace kada a sake turawa jihar wadannan kudade. Wasu masu sharhi da yawa dai sun bayyana wannan mataki da cewa ba ya rasa nasaba da rashin jituwa dake tsakanin Gwamna Sim Fubara da Nyesome Wike.
Majalisar tarayya ta fara tantance sabbin ministoci

Majalisar tarayya ta fara tantance sabbin ministoci

Duk Labarai
Majalisar tarayya ta dakatar da duk wani aikin da take a ranar Laraba inda ta fara tantance sabbin ministocin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mika mata sunayensu. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya aikewa da majalisar sunayen sabbin ministocin da ya nada bayan da yawa majalisarsa ta zartaswa garanbawul, inda ya hade wasu ma'aikatun sannan ya kirkiri wasu ya kuma kori wasu ministoci sannan ya nada wasu sabbi. Senator Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da fara tantance ministocin sannan sanata Abba Moro ya goya masa baya. Daga nan ne sai aka karanto sunayen sabbin ministocin da za'a tantance wanda ciki akwai Dr. Nentewa Yilwatda a matsayin ministan jin kai da rage talauci, Sai kuma Muhammad Maigari Dingyadi a matsayin ministan ayyuka da kwadago, Sai kuma Bianca Odinaka Odume...
Muna ci gaba da kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace kuma zuwa yanzu mun kashe Naira Biliyan 29 a wajan gyaran>>Gwamnatin Tarayya

Muna ci gaba da kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace kuma zuwa yanzu mun kashe Naira Biliyan 29 a wajan gyaran>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta hannun kamfanin samar da wutar lantarki na kasa, TCN ta bayyana cewa zuwa yanzu ta kashe Naira Biliyan 29.3 a wajan gyaran wutar Lantarkin data lalace. Karafunan wutar lantarkin 266 ne aka lalata a duka fadin Najeriya. Ciki hadda wanda ya faru kwanannan wanda ya shafi wasu jihohin Arewa. Rahotanni dai sun bayyana cewa, Najeriya na tafka asarar Dala Biliyan 26 duk shekara saboda matsalar lalacewar wutar lantarki. A baya dai irin wannan matsala ta faru a jihohin Abuja, Lagos, Kano, Enugu, Bauchi, Port Harcourt, da yankin Benin.
‘Yan ta’adda sun kwace iko da sansanin horas da soji mafi girma a Najeriya

‘Yan ta’adda sun kwace iko da sansanin horas da soji mafi girma a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan Bindiga sun kwace iko da sansanin horas da soji na Nagwamase Military Cantonment dake karamar hukumar Kwantagora a jihar Naija. Hakanan aun kuma kori mutanen kauyukan dake kusa da sansanin. Majalisar jihar Naija ce ta bayyana hakan inda ta ti kira ga gwamnati data ta kawo karshen ayyukan 'yan ta'addan. Jimullar Kauyuka 23 ne dai 'yan Bindigar suka kwace iko dasu. Dan majalisar jihar dake wakiltar Kwantagora, Abdullahi Isah ne ya kai maganar zauren majalisar ranar Talata inda yace sansanin horas da sojin dake da girma wanda yake a cikin karamar hukumar Kwantagora har zuwa karamar hukumar Mariga a yanzu yana hannun 'yan Bindigar. Ya bayyana cewa kasancewar 'yan Bindigar a cikin sansanin yana a matsayin wata barazanane ga jama'ar yankin inda yac...