‘Yansanda sun tarwatsa matasa a Zoo Road Kano da suka yi yunkurin fasa shaguna
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, 'yansanda sun tarwatsa matasa da suka yi yunkurin fasa shaguna a Kano dan yun sata.
Rahoton Daily Trust yace tuni aka fasa tagogin wasu daga cikin shagunan amma kamin akai ga yin satar jami'an tsaro sun isa wajan.
Saidai a wani bangare na garin kuma an samu zanga-zangar ta lumana.