Tuesday, February 17
Shadow

Duk Labarai

Babban Lauya, Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da aka kama da kuma basu ilimi kyauta, Sannan yace kotun ma bata da hurumin yi musu Shari’a

Babban Lauya, Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da aka kama da kuma basu ilimi kyauta, Sannan yace kotun ma bata da hurumin yi musu Shari’a

Duk Labarai
Babban lauya,Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da gwamnatin Tinubu ta gabatar a gaban kotun tarayya dake Abuja a kotu bisa zargin cin amanar kasa. Femi Falana wanda lauyane na kare hakkin bil'adama ya bayyana cewa kotun bata da hurumin tuhumar yaran. Yace kotun ta gaggauta sakinsu sannan kuma gwamnati ta dauki nauyin karatunsu akalla zuwa sakandare ko jami'a. Yace ko da sun aikata laifi, ba tare da manyan mutane za'a yanke musu hukunci ba dolene a kaisu inda ake yankewa yara hukunci.
Bazan taba bayar da kudi dan yiwa mutane auren gata a mazabata ba saboda bana son ganin karin yara da yawa>>Inji Dan majalisar Tarayya, Bello El-Rufai

Bazan taba bayar da kudi dan yiwa mutane auren gata a mazabata ba saboda bana son ganin karin yara da yawa>>Inji Dan majalisar Tarayya, Bello El-Rufai

Duk Labarai
Dan majalisar wakilai ta tarayya kuma da a wajan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya bayyana cewa ba zai taba biyan kudi a yiwa mutane auren gata a mazabarsa ba. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yo dashi wadda hutudole ya bibiya. Yace dalilinsa kuwa baya son ganin karin yawan yara. Yace a yanzu haka a Arewa yawanmu ya wuce kima amma kuma bamu da isashshen ilimi. https://twitter.com/IU_Wakilii/status/1852740532964855995?t=ZXKaUEF7mQX2zUghhpdiIg&s=19 Lamarin yawa da almajirci na kananan yara dai a bayyane yake a Arewacin Najeriya.
Allah Sarki kalli bidiyon yawabi me sosa Zuciya na Sheik Makari akan Kananan yaran da gwamnatin Tinubu ta kai Kotu

Allah Sarki kalli bidiyon yawabi me sosa Zuciya na Sheik Makari akan Kananan yaran da gwamnatin Tinubu ta kai Kotu

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama kuma Limamin masallacin Abuja, Sheikh Makari ya bayyana takaici da kama yaran da gwamnatin Tinubu ta yi ta kai kotu da sunan sun ci amanar kasa. Babban malamin yace babu inda ake irin haka a Duniya. Yace zasu dauki nauyin kula da yaran kamin a sakosu sannan kanana daga ciki zasu dauki nauyin karatunsu. https://twitter.com/Realoilsheikh/status/1852706767139946625?t=5MbxAjpwwcIeKYmpbOe1mQ&s=19 Malamin ya bayyana a wani faifan bidiyo ne a wajan karatu inda aka jishi yana jawabin
Wata Sabuwa: Kananan yaran da gwamnatin tarayya ta gabatar a kotu bisa zargin cin amanar kasa na iya fuskantar hukuncin kìsà

Wata Sabuwa: Kananan yaran da gwamnatin tarayya ta gabatar a kotu bisa zargin cin amanar kasa na iya fuskantar hukuncin kìsà

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa hukuncin kisa na daga cikin hukuncin da kananan yara da gwamnatin tarayya ta gabatar a kotu a Abuja zasu iya fuskanta. Yaran dake da shekaru 14 zuwa 17 su 29 ko 32 a wasu rahotannin sun baiwa mutane tausa yi sosai bayan ganinsu cikin tashin hankali,yunwa da rashin lafiya. Yaran sun rika yanke jiki suna faduwa saboda yunwa bayan da aka gabatar dasu a kotu, saidai Hukumar 'yansandan Najeriya tace duk karya suke kawai dan su jawo cece-kuce ne. Saidai duk wanda ya ga yaran yasan suna cikin tashin hankali dan idanuwansu sun yi zuru-zuru ga kasusuwan hakarkarinsu duk a waje ga jikinsu ba alamar kuzari duk dai alamun yunwa sun bayyana a tattare dasu. Rahoton VOA yace yaran zasu iya fuskantar hukuncin kisa saboda shine hukuncin laifin cin amanar kasa da ake z...
Kalli Hotuna da Bidiyo: Wani mutum ya binne surukinsa a akwatin gawa na Naira Miliyan dari da talati, 130M a Najeriya

Kalli Hotuna da Bidiyo: Wani mutum ya binne surukinsa a akwatin gawa na Naira Miliyan dari da talati, 130M a Najeriya

Duk Labarai
Wani dan kasuwa, Dr. Ugonna Osinachi Cliff Orabuchi, (Ikenga Ogberuru) daga jihar Imo ya saiwa surukinsa akwatin gawa na Naira Miliyan 130. Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin na da kyakkyawar ma'amala da surukin nasa tun yana da rai inda har gida ya sai masa dama wasu dake kusa dashi. Lamarin dai ya dauki hankula da baiwa mutane mamaki musamman ganin yawan kudin da mutumin ya kashe.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yace cikin yaran da gwamnatin Tinubu ta kai kotu jiya akwai ‘yan Kano kuma zai dawo dasu gida

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yace cikin yaran da gwamnatin Tinubu ta kai kotu jiya akwai ‘yan Kano kuma zai dawo dasu gida

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an jawo hankalinsa game da kananan yaran da gwamnatin tarayya ta gurfanar a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu ta hanyar zanga-zanga. Gwamnan a sanarwar da ya fitar ta kafar X, ya bayyana cewa, ya baiwa kwakishinan Shari'a umarnin gaggauta yin abinda ya dace kan lamarin. Ya karkare da cewa insha Allahu zai dawo dasu gida Kano.
Sumar da yaran da muka kama suka yi a kotu duk karyace kawai dan su ja hankalin mutanene>>Inji Shugaban ‘yansandan Najeriya

Sumar da yaran da muka kama suka yi a kotu duk karyace kawai dan su ja hankalin mutanene>>Inji Shugaban ‘yansandan Najeriya

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya bayyana cewa, sumar da matasa 6 suka yi a kotu karyace kawai dan su jawo hankalin mutanene. Saidai yace duk da haka an baiwa matasan taimakon gaggawa wanda hakan ke nuna kokarin 'yansanda wajan ganin sun baiwa wanda suke tsare dasu kulawa. Yace kuma maganar shekarun yaran idan dai mutum ya kai shekarar aikata laifi karancin shekarunsa basa hana a hukuntashi kuma haka dokar take koda a kasar Ingila ne. Yace wasu daga cikin laifukan da ake zargin yaran da aikatawa sun hada da lalata dukiyar 'yan kasa da kuma barazana ga tsaron kasa. Ya kara da kira ga mutane da kada su nuna goyon bayan wani bangare kuma hukumar 'yansanda zata tabbatar ta bayyana duk abinda ke faruwa ba tare da boye komai ba. Sanan ya bayar da tabbacin cewa ...
Hotuna: Matar aure ta càkàwà mijinta wuka ya mùtù bayan da gardama ta barke tsakaninsu

Hotuna: Matar aure ta càkàwà mijinta wuka ya mùtù bayan da gardama ta barke tsakaninsu

Duk Labarai
Wata matar aure me suna Comfort Olajumoke Olalere Tinubu ta kashe mijinta ta hanyar caka masa wuka ya mutu bayan da gaddama ta barke a tsakaninsu. Lamarin ya farune a Gbeyi dake yankin Adegbayi a Ibadan jihar Oyo da misalin karfe 10 na daren Laraba, 30 ga watan October 2024. Shekaru 3 kenan da aurensu kuma suna da yara 2. TheNation ta ruwaito cewa matar me shekaru 33 ta kulle mijinta, Olusegun a dakinsu bayan da suka yi fada wanda daga baya abin ya kazance da ya kai ga har ta caka masa wuka ya mutu. Zuwa yanzu dai 'yansanda na bincike akan lamarin.
Kalli Bidiyo: Yanda matar aure ta jewa mijinta tsìràrà bayan sun yi fada dan dai kawai ta shawo kansa

Kalli Bidiyo: Yanda matar aure ta jewa mijinta tsìràrà bayan sun yi fada dan dai kawai ta shawo kansa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wata matar aure ta dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan da ta jewa mijinta tsirara, Tumbur bayan sun yi fada dan ta shawo kansa. An ga Bidiyon yanda matar ke daukar kanta da kuma abinda mijin yayi bayan ya ganta. https://twitter.com/Postsubman/status/1852590947869024357?t=xNDKNAB5f75CCZ_eyuBSxQ&s=19 Saidai matsalar da yarbanci suke magana.
Babu kananan yara a cikin wadanda muka kai kotu, duk manyan mutanene wasunsu ma suna da aure>>Gwamnatin Tarayya

Babu kananan yara a cikin wadanda muka kai kotu, duk manyan mutanene wasunsu ma suna da aure>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu kananan yara a cikin wadanda ta gabatar a kotu da take zargi da cin amanar kasa ta hanyar kifar da gwamnatin shugaban kasa,Bola Ahmad. Lauyan Gwanatin, Rimazonte Ezekiel ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai. Ya kara da cewa, laifin su shine suna kiran sojoji su kwace mulki da daga tutar kasashen waje da kuma tayar da hankula. https://twitter.com/channelstv/status/1852450588178460769?t=9Ads0XRv52vEALHwdLs_Mg&s=19 Saidai da yawa sun kalubalanceshi da cewa maganar tasa ba gaskiya bane musamman tunda gashi mutane na gani yara ne suka gabatar. A baya dai hutudole ya kawo muku yanda kakakin 'yansandan Najeriya ya kare kama yaran inda yace doka tace ko da shekaru 7 za'a iya kaishi kotu. Ya kara da cewa kuma cikin yaran da...