Sunday, December 22
Shadow

Duk Labarai

Yanzu-Yanzu: An kama wadanda suka Kàśhè janar din soja a Abuja, Kalli hotunansu

Yanzu-Yanzu: An kama wadanda suka Kàśhè janar din soja a Abuja, Kalli hotunansu

Tsaro
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, an kama 'yan fashin da suka kashe janar din soja mai ritaya a Abuja. An kama mutanen su 4 wanda aka bayyana sunayensu kamar haka: Ibrahim Rabiu, 33; Nafiu Jamil, 33; Aliyu Abdullahi, 47; Mohammed Nuhu, 28 Rahoto yace dukansu suna zaunene a Apo Primary school. Kuma duka sun amsa laifin da ake tuhumarsu dashi. Sunce aun kashe Brig.-Gen. Uwem Udokwere Ne bayan da suka ga ya fito da Bindiga yana shirin harbinsu. Kuma sun sace wayarsa da sauran wasu kayan amfani a gidan nasa. Ranar Asabar data gabata ne dai maharan suka yi wannan mummunar ta'asa wadda ta dauki hankula a Najeriya.
Cin bashin da ƴan Najeriya ke yi ya ƙaru saboda matsin rayuwa – CBN

Cin bashin da ƴan Najeriya ke yi ya ƙaru saboda matsin rayuwa – CBN

Siyasa
Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da rahoton cewa, ƴan Najeriya sun koma cin bashi daga bankuna da manhajojin karɓar bashi saboda tsananin tsadar rayuwa domin samun biyan buƙata. CBN ya ce an samu ƙaruwar masu ciyo bashi da kashi 12 cikin 100, inda ya kai kusan tiriliyan ₦3.9 a watan Janairun 2024. An danganta wannan ƙaruwar ciyo bashin da hauhawar farashin kayan masarufi. Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ruwaito cewa hauhawar farashin kaya ya kai kashi 33.95 cikin 100 a watan Mayu. Hakan ya sa babban bankin ƙasar ya ƙara yawan kuɗin ruwa a jere zuwa kashi 26.25 bisa 100. Hauhawar farashin kaya ya jefa ƴan Najeriya cikin wani mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya ƙara tsadar rayuwa. Wani bincike da SBM Intelligence ya gudanar ya nuna cewa k...
Hotuna: Jami’an tsaro sun kama wannan matar da daruruwan àlbárusan bìndìga za ta kai yankin Yantumaki dake cikin karamar hukumar Dan’musa a Jihar Katsina , tace yunwa ce tasa ta shiga wannan sana’a

Hotuna: Jami’an tsaro sun kama wannan matar da daruruwan àlbárusan bìndìga za ta kai yankin Yantumaki dake cikin karamar hukumar Dan’musa a Jihar Katsina , tace yunwa ce tasa ta shiga wannan sana’a

Tsaro
Hakika Maķàsañ Al'ummar Arewa Suna Tare Da Su Daga Bashir Babandi Gumel Jami'an tsaro sun kama wannan matar da daruruwan albarusan bindiga za ta kai yankin Yantumaki dake cikin karamar hukumar Dan'musa a Jihar Katsina kamar yadda ta bayyana yayin da Jami'an tsaron suke yi mata tambayoyi. Wannan kamu yana zuwa ne kwana daya da kaiwa wani mummunan harin ta'addanci a garin Maidabino dake karamar hukumar ta Danmusa wanda ya yi sanadiyar kashe mutane 9 da kona motoci, gidaje, da satar kayakin masarufi da mutane sama da hamsin wadanda aka tafi dasu daji da sunan garkuwa dasu. Allah ka kawo mana karshen munafuka da masu yin zagon kasa ga harkokin tsaro da ke cikinmu tare da wannan masifa ta matsalolin tsaro da muke fama da su a yankin Arewa da kasa baki daya.
Akalla mutum 1,301 ne suka mutu a yayin aikin Hajjin bana – Saudi Arabia

Akalla mutum 1,301 ne suka mutu a yayin aikin Hajjin bana – Saudi Arabia

Duk Labarai
Mahukunta a Saudi Arabia sun ce akalla mutum 1,301 ne suka rasu a yayin aikin Hajjin bana, kuma yawancinsu wadanda suka je ta barauniyar hanya ne da ke tafiyar kafa mai nisan gaske a cikin tsananin zafin da aka yi fama dashi a lokacin aikin Hajjin. An gudanar da aikin Hajjin bana a cikin yanayi na tsananin zafi inda zafin a wasu lokuta kan zarta digiri 50 a ma’aunin selshiyos. A cewar kamfanin dillancin labarai na SPA, fiye da rabin wadanda suka mutum ba su da cikakkun takardun da ke nuna cewa alhazai ne da suka je kasar ta Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana.Kuma wahala da tsananin zafi ne ke sanya su galabaita saboda basu da wajen fakewa ma’ana inda ake tanadarwa alhazai. Kamfanin dillancin labaran y ace yawancin wadanda suka mutun tsofaffi ne ko kuma masu fama da wat acut...
Ƴan majalisar wakilai 50 sun buƙaci a sako Nnamdi Kanu, sun aike da takarda ga Tinubu

Ƴan majalisar wakilai 50 sun buƙaci a sako Nnamdi Kanu, sun aike da takarda ga Tinubu

Duk Labarai
Ƴan majalisar wakilai 50 sun buƙaci a sako Nnamdi Kanu, sun aike da takarda ga Tinubu Kimanin ƴan majalisar wakilai 50 daga sassa daban-daban na Najeriya da jam’iyyun siyasa, wadanda aka fi sani da ‘Concerned Federal Lawmakers for Peace and Security in South East’, sun roki shugaba Bola Tinubu da ya yi amfani da sashe na 174 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, 1999 (kamar yadda gyara) da kuma sashe na 107 (1) na dokar shari’a ta 2015 domin sakin jagoran ‘yan asalin yankin Biyafara, Nnamdi Kanu daga tsare shi don taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a yankin kudu maso gabas. Ƴan majalisar, wadanda suka fito daga jam’iyyun siyasa daban-daban da kuma shiyyoyin siyasa a fadin kasar nan, sun kuma yi kira ga shugaba Tinubu da ya fara shirin zaman lafiyar shugaban kasa domin magance duk wasu ...
MASHA ALLAH: Maryam Kenechi Kenan, Ƴar Ķabilar Ibo Da Ta Karɓi Mùśùluñci

MASHA ALLAH: Maryam Kenechi Kenan, Ƴar Ķabilar Ibo Da Ta Karɓi Mùśùluñci

Duk Labarai
MASHA ALLAH: Maryam Kenechi Kenan, Ƴar Ķabilar Ibo Da Ta Karɓi Mùśùluñci "Zuwa ga 'yan uwana da abokaina da na ɓatawa rai bayan na koma addínin mùśùluñci ina mai ba su haƙuri, na zaɓi na rasa komai akan bin tafarkin Allah. "Da yardar Allah zan mùťù ina musulmà, ìnji Maryam Ķenechi, kamar yadda ta rubuta a shafinta na facebook. Daga Abubakar Shehu Dokoki
Matashi dan Najeriya yayi gàŕkùwa da kansa inda ya nemi mahaifinsa ya biya kudin fansa har dala $700,000

Matashi dan Najeriya yayi gàŕkùwa da kansa inda ya nemi mahaifinsa ya biya kudin fansa har dala $700,000

Tsaro
Wani matashi dan kimanin shekaru 20 a Legas yayi garkuwa da kansa inda ya nemi mahaifinsa ya biya kudin fansa har dala $700,000. Matashin shi da abokansa mata 4 sun kama gida ne suka boye a ciki inda yawa mahaifinsa karyar an yi garkuwa dashi. Saidai da bincike yayi tsanani an gano dabarar tasu. An kamasu ana kan bincike. Hukumar 'yansanda ta jihar Legas din ta tabbatar da lamarin da kama wanda ake zargi me suna Collins Ikwebe.
A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

labaran tinubu ayau, Siyasa
Gwammatin tarayya a karkashin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen da shugaban kasar ke amfani dasu a cikin watanni 11 da suka gabata. Hakan na zuwane a yayin da majalisar tarayya ta amince a sayowa shugaban kasar sabbin jirage 2. Kudin da za'a kashe wajan siyo sabbin jiragen sun kai Naira Biliyan 918.7 ko kuma dala Miliyan 623.4, kamar yanda kwamitin majalisar ya bayyana. Rahotanni dai sun bayyana cewa, jiragen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa,Kashim Shettima ke amfani dasu sun tsufa sosai suna bukatar a canjasu.