Monday, December 23
Shadow

Duk Labarai

Bidiyo da Hotuna Da Duminsu: Harin ‘Yan Ďabà A Kano Ya Yi Silar Muťùwàr Mutum Daya Tare Da Raunata ‘Yan Sanda Biyu

Bidiyo da Hotuna Da Duminsu: Harin ‘Yan Ďabà A Kano Ya Yi Silar Muťùwàr Mutum Daya Tare Da Raunata ‘Yan Sanda Biyu

Kano, Tsaro
Harin 'Yan Ďabà A Kano Ya Yi Silar Muťùwàr Mutum Daya Tare Da Raunata 'Yan Sanda Biyu. Dama dai wasu na kokawa da cewa an jibge 'yan daba a fadar Sarkin Kano dake Kofar kudu inda wasu ke ganin hakan ka iya zama barazanar tsaro ga al'ummar dake kewaye da yankin. https://twitter.com/Musaddiqww/status/1803537550876815767?t=zFtVr6QilV2yJF7TI9xRQQ&s=19 An dai jawo hankalin jami'an tsaro kan wannan lamari: https://twitter.com/Musaddiqww/status/1803678430346530884?t=ARnpwjVzoX22x5VVfi-_sA&s=19 Jihar Kano dai ta kasance cikin rashin tabbas akan rikicin masarautar jihar tsakanin Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero.
Na sadaukar da kaina a turani zuwa Duniyar wata a matsayin dan Najeriya na farko>>Sanata Ben Murray Bruce

Na sadaukar da kaina a turani zuwa Duniyar wata a matsayin dan Najeriya na farko>>Sanata Ben Murray Bruce

Siyasa
Sanata Ben Bruce ya jinjinawa gwamnatin tarayya kan sakawa yarjejeniyar zuwa duniyar wata hannu tsakanin Najeriya da kasar Amurka. A jiya ne dai hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya ta tabbatar da cewa, an sakawa yarjejeniyar hannu kuma za'a tura dan Najeriya na farko zuwa sararin samaniyar. https://twitter.com/benmurraybruce/status/1803543591341662332?t=VOMxw7MsbkJf_xDOf49lzw&s=19 Sanata Bruce yace ya sadaukar da kansa a matsayin dan Najeriya na farko da zai fara zuwa Duniyar watar. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta.
Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci

Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci

Duk Labarai
Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci. Shahararriyar Manhajar haƙo sulalla ta Tapswap ta hanyar TON Blockchain ta ce ta jinkirta ranar bajakolin kasafin sulalla ga masu amfani da shi zuwa wani lokaci da ba su sanar ba, yayin da ma'aikantan su ke kokarin neman karin hanyoyin da za su inganta shi domin amfanar mutane da yawa. Shugaban sashen sadarwa na Tapswap John Robbin ne ya bayyana hakan a dandalin sadarwarsa na X ranar Laraba. Dandalin wanda ke buƙatar masu amfani da shi da su rika danna alamar da ke tsakiyar manhajar Tapswap a Telegram don hakar sulalla a kwanan nan ya samu karbuwa a tsakanin 'yan Najeriya inda suke duƙufa wajen latsa fuskar wayarsu don neman kudi, kuma ya tara mutane sama da Miliyan 50 tun bayan da aka kaddamar da shi a ranar 15 g...
Nnamdi Kanu na duba yiwuwar yin sulhu da gwamnatin Najeriya

Nnamdi Kanu na duba yiwuwar yin sulhu da gwamnatin Najeriya

Siyasa
Lauyoyin jagoran ƙungiyar Ipob mai rajin kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu sun bayyana cewa akwai yiwuwar su tuntuɓi gwamnati domin neman sasanci a wajen kotu game da shari'ar da ake yi masa. Ana tuhumar Nnamdi Kanu ne da laifukan da suka jiɓanci ta'addanci a matsayinsa na jagoran ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra ta Ipob. Ƙungiyar na ƙoƙarin ganin yankin kudu maso gabashin Najeriya ya ɓalle ne tare da kafa ƙasa mai zaman kanta. Tuntuni gwamnatin Najeriya ta ayyana ƙungiyar a matsayin ta ƴan ta'adda. Aloy Ajimakor, wanda shi ne jagoran lauyoyin da ke kare Kanu, ya shaida wa kotu cewa kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar da ta kafa Babbar kotun tarayya sun bayar da damar sasantawa a wajen kotu kan duk wani rikici tsakanin mutum da mutum ko kuma wani mutum da gwamnati. Sai ...
Da ace tintuni da sabon taken Najeriya ake amfani da ba’a samu matsalar tsaron da ake fama da ita ba>>Inji kakakin majalisar tarayya Akpabio

Da ace tintuni da sabon taken Najeriya ake amfani da ba’a samu matsalar tsaron da ake fama da ita ba>>Inji kakakin majalisar tarayya Akpabio

Siyasa
Kakakin majalisar tarayya, Godswill Akpabio ya bayyana cewa, da tuntuni da sabon taken Najeriya ake amfani, da ba'a yi fama da matsalar 'yan Bindigar da ake fama da ita ba. Ya bayyana hakane a wata ziyara da ya kai wata tsangayar karatun Dimokradiyya a Abuja ranar Talata. Ya kara da cewa saboda idan aka lura da taken yana sawa mutum soyayyar makwabcinsa wanda idan mutum na son makwabcinsa ba zai cutar dashi ba. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya canja taken Najeriya daga wanda aka sani zuwa wannan sabon wanda ya jawo cece-kuce sosai.
Da Duminsa: A karin Farko Gwamnatin tarayya tace zata tura dan Najeriya na farko zuwa duniyar wata

Da Duminsa: A karin Farko Gwamnatin tarayya tace zata tura dan Najeriya na farko zuwa duniyar wata

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da kudirinta na son tura dan Najeriya na farko zuwa Duniyar wata. Shagaban hukumar kula da sararin Samaniya ta Najeriya, Mathew Adepoju ne ya bayyana haka ranar Laraba a Abuja. Ya bayyana cewa tuni Nigeria ta kulla yarjejeniya dan cimma wannan matsayi. Ya bayyana cewa, Wannan ba karamin ci gaba zai kawowa Najeriya ba ta fannin bincike da kimiyya a sararin samaniya.
APC ta Kano ta yi kira da a kama Kwankwaso

APC ta Kano ta yi kira da a kama Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso, Siyasa
APC ta Kano ta yi kira da a kama Kwankwaso Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta bukaci a kama jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma dan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. A wata Sanarwa da Abdullahi Abbas Shugaban APC a Kano ya fitar, jam’iyyar ta zargi Kwankwaso da yin zarge-zarge marasa tushe ga Gwamnatin Tarayya. Dimokuradiyya TV ta ruwaito cewa, a yayin bikin kaddamar da aikin gina Titi mai tsawon kilomita 85 a garin Madobi, Kwankwaso ya ce Gwamnatin APC karkashin jagoranci Gwamnatin Tarayya na yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a Kano. Amma Abbas yace ba wata barazana da Kwankwaso zai iya yi wa Gwamnatin Tarayya. Muna so mu yi kira ga jami’an tsaro da kakkausar murya da su kamo Kwankwaso, domin ya tona asirin wadanda ya kira makiyan Jihar Ka...