Monday, December 23
Shadow

Duk Labarai

Sojan Najeriya ya dirkawa kanshi biinndiigaa ya muutuu

Sojan Najeriya ya dirkawa kanshi biinndiigaa ya muutuu

Duk Labarai
Sojan Najeriya dake aki a 14 Brigade Headquarters, Goodluck Ebele Jonathan’s Barrack, dake Ohafia, a jihar Abia ya kashe kansa. Sojan wanda aka bayyana sunan sa da Vitalis ya kashe kansa ne a kofar wajan aikinsa. Zuwa yanzu dai ba' san dalilinsa na aikatawa kansa wannan danyen aiki ba. Majiyoyi sun ce bincike ne kawai zai bayyana dalilin kashe kansa da wannan sojan yayi.
Obasanjo Ya Ziyarci Uwargidan Shugaban Kasa Bayan ‘Yan Kwanaki An Hange Shi Sanye Da Hula Kalar Tambarin Tinubu

Obasanjo Ya Ziyarci Uwargidan Shugaban Kasa Bayan ‘Yan Kwanaki An Hange Shi Sanye Da Hula Kalar Tambarin Tinubu

Duk Labarai
Obasanjo Ya Ziyarci Uwargidan Shugaban Kasa Bayan 'Yan Kwanaki An Hange Shi Sanye Da Hula Kalar Tambarin Tinubu Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ziyarci uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu domin murnar bikin Sallah, ranar Litinin a Legas. Mataimaki na musamman ga uwargidan shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Busola Kukoyi, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X tsohon shafin twitter. Ziyarar ta zo ne kwanaki bayan da aka ga tsohon shugaban kasar a wani taron sanye da hula da kayan adon da ya yi kama da tambarin da ke kan hular Tinubu. Wannan ci gaban ya haifar da martani daban-daban, yayin da wasu 'yan Najeriya ke tunanin ko Obasanjo ya koma goyon bayan Tinubu. A ci gaban zaben 2023, Obasanjo ya amince da Peter ...
Dan Wasa Mbappe Ya Ji Rauni A Karan Hanci A Wasan Da Suka Yi Da Austria

Dan Wasa Mbappe Ya Ji Rauni A Karan Hanci A Wasan Da Suka Yi Da Austria

Duk Labarai
Kylian Mbappe ya ji rauni a karan hanci a wasan farko da Faransa ta yi a cikin rukuni na hudu a Euro 2024, amma baya bukatar tiyatar gaggawa. Wadda ta yi ta biyu a kofin duniya a Qatar a shekarar 2022 ta yi nasarar cin Austria 1-0, bayan da Maximilian Wober ya ci gida a minti na 38 a karawar farko a cikin rukuni. An sanar da cewar ba sai an yi wa sabon dan kwallon Real Madrid tiyata da wuri ba, wanda ake fatan zai murmure a kan lokaci. Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta sanar cewar za ta samar da kariyar fuska ga kyaftin din, amma ba ta fayyace ko zai buga wasa na biyu da Netherlands ba. Mai shekara 25, sai sauya shi aka yi a wasan da Faransa ta yi nasarar cin Austria 1-0 a ranar Litinin. Ya kuma ji rauni ne sanadiyyar karo da ya yi da kafadar Kevin Danso, lokacin da suka ci...
Kano: Za mu bijirewa dokar ta-ɓaci – Kwankwaso ya zargi gwamnatin Najeriya da haddasa rashin tsaro

Kano: Za mu bijirewa dokar ta-ɓaci – Kwankwaso ya zargi gwamnatin Najeriya da haddasa rashin tsaro

Rabiu Musa Kwankwaso, Siyasa
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Ahmed Bola Tinubu da yiwa jami'an tsaron Kano zagon kasa sakamakon kin cire jami'an da ke gadin hambararren Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado. Bayero. Kwankwaso ya kuma zargi Gwamnatin Tarayya da yunkurin haifar da wani sabon salo na kungiyar ta’addanci da masu tayar da kayar baya a Arewacin Najeriya. Kwankwaso dai na mayar da martani ne kan halin da ake ciki a Kano inda ake zargin hukumomin tsaron gwamnatin tarayya na goyon bayan hambararren Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero. Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin gina titunan karkara mai tsawon kilomita 82 a mahaifarsa, Madobi, Sanata Kwankwaso ya ce al’ummar Kano za su bijirewa duk wani yunkuri na kawo cikas ga gwam...
Ba Za Mu Iya Shiru Mu Bar Makiya Su Lalata Zaman Lafiya A Jihar Kano Ba, Cewar Kwankwaso

Ba Za Mu Iya Shiru Mu Bar Makiya Su Lalata Zaman Lafiya A Jihar Kano Ba, Cewar Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso, Siyasa
Ba Za Mu Iya Shiru Mu Bar Makiya Su Lalata Zaman Lafiya A Jihar Kano Ba, Cewar Kwankwaso …ya zama dole mu bi hanyar da ta dace wajen ganin jihar Kano ta samu kyawawan tsari na zaman lafiya Daga Muhammad Kwairi Waziri Ɗan takarar shugabancin kasa a jami'yar NNPP Dr. rabiu musa kwankwaso ya bayyana hakan ne a mahaifarsa ta Madobi yayin ƙaddamar wata hanya mai tsawon kilomita 82. Yace "akwai wasu mutane ne da suke son suci zarafin mu da sunan siyasa wanda ba zamu lamunci hakan ba ko waye shi, dan haka kuma a shirye muke damu taka duk wanda yake da niyyar taka mu a siyasar jihar kano" inji kwankwaso.
Yau ake kammala aiki Hajji

Yau ake kammala aiki Hajji

Duk Labarai
A ranar Talatar nan ne mahajjata miliyan ɗaya da 800,000 suke ƙarƙare aikin Hajjin bana, bayan kammala jifan shaiɗan kamar yadda aka fi sani. Ana dai yin jifan ne a ranakun 10 da 11 da 12 inda mahajjatan ke tsintar ƙananan duwatsu guda bakwai a kowane domin jifan kowacce Jamrat daga jamrori uku. Sai dai wasu mahajjatan kan zaɓi ƙara kwana ɗaya kamar yadda addinin Musulunci ya ba su dama, inda sai zuwa ranar Laraba ne za su bar Mina zuwa Makka. Yayin da wasu alhazan sai sun koma Makka ne za su yi ɗawafi da sa'ayi, wasu kuwa za su wuce masauki ne kawai su samu su huta kasancewar sun gabatar da nasu tun ranar 10 ga watan na Dhul Hajji.
Ya kamata ƴan Najeriya su sauya halayensu – Tinubu

Ya kamata ƴan Najeriya su sauya halayensu – Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su sauya tunaninsu a kan kasa tasu. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa shugaban dai na magana ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga majalisar dokokin ƙasar waɗanda suka kai masa ziyarar barka da sallah,. Mista Tinubu ya ce "lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su sauya hali da tunaninsu ga Najeriya domin ciyar da ƙasar gaba". "Yan ƙasa da ke yawon neman wayar lantarki domin su cire da tuge titin dogo da dai sauran ayyukan ɓaagari, E, na amince akwai talauci, akwai wahalhalu. Amma ba mu kaɗai ne mutanen da muke shan wahala ba. Dole ne mu tunkari kalubalen da ke gabanmu." In ji Tinubu. Ya ƙara da cewa "akwai bukatar wasu ƴan ƙasar su sauya tunaninsu su kuma zama masu taimakawa wajen warware ƙalubalen da tattalin arziƙ...
Jadawalin wasannin Premier League makon farko

Jadawalin wasannin Premier League makon farko

Duk Labarai
Ranar Juma'a 16 ga watan Agusta Manchester United da Fulham Ranar Asabar 17 ga watan Agusta Ipswich Town da Liverpool Arsenal da Wolverhampton Everton da Brighton Newcastle United da Southampton Nottingham Forest da Bournemouth West Ham United da Aston Villa Ranar Lahadi 18 ga watan Agusta Brentford da Crystal Palace Chelsea da Manchester City Ranar Litinin 19 ga watan Agusta Leicester City da Tottenham Wasu mahimman batuwan da suka shafi Premier League 2024/25 Manchester City za ta buga wasa biyu daga bakwai kafin Champions League, wadda za ta yi uku a Etihad da Aston Villa da Arsenal da kuma Liverpool. Wasa mai nisa da za a buga shi ne mil 200 ranar 26 ga watan Disamba da Arsenal za ta ziyarci Newcastle United a St James Par. Mak...
Hoto: An kamasu sun yiwa matar aure da kawayenta fyade

Hoto: An kamasu sun yiwa matar aure da kawayenta fyade

Tsaro
Hukumar 'yansanda sun kama wadannan 'yan fashin a Abagana dake karamar hukumar Njikoka jihar Anambra. Rahoto yace mutanen sanannun masu yiwa mata fyadene. Sun shiga gidan wata mata inda suka sameta ita da kawayenta suka musu fyade sannan suka sa daya daga ciki ta tura musu kudi. Kakakin 'Yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargin sun amsa laifukansu. Sannan za'a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.