Sunday, November 22
Shadow

Duk Labarai

Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau, Juma’a

Farashin dala a kasuwar Chanji ta yau, Juma’a

Duk Labarai
Farashin dala a kasuwar Chanji ta Gwamnati a yau, Juma'a, 31 ga watan Yuli ta kamane akan Naira ₦1,379 akan kowace dala. Masana kasuwar sun ce a yau Farashin zai kamane akan tsakanin Naira ₦1,379–₦1,384 A kasuwar bayan fage ta garuruwan Kano, Abuja, Lagos da Fatakwal kuwa, Farashin dalar ya kamane akan Naira ₦1,409 zuwa Naira 1,420 Ya danganta Mutum saye ko sayarwa zai yi.
Kalli Bidiyon: Yanda ‘yar Takarar Gwamna ta jam’iyyar AAC ke jaraba saboda an ce ta biya Naira Miliyan 150 kudin harajin saka fastar yakin neman zabenta

Kalli Bidiyon: Yanda ‘yar Takarar Gwamna ta jam’iyyar AAC ke jaraba saboda an ce ta biya Naira Miliyan 150 kudin harajin saka fastar yakin neman zabenta

Duk Labarai
Wannan 'yar takarar Gwamna ce a karkashin jam'iyyar AAC a jihar Abia. An ce ta biya kudin harajin saka fastar yakin neman zabenta na naira Miliyan 150. Saidai ta je gaban Hukumar kula da tallace-tallace ta jihar tana ta musu masifa tana cewa ina taga Naira Miliyan 150? Tace zata yi yakin neman zaben ta babu fasta. https://twitter.com/i/status/2082855522936504585
Da Duminsa: An samu baraka a tafiyar su Kwankwaso da Peter Obi ta OK

Da Duminsa: An samu baraka a tafiyar su Kwankwaso da Peter Obi ta OK

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, an samu baraka a tafiyar Kwankwaso da Peter ta OK. Wasu ne aka samu suka balle suka ce sun kori shuwagabannin tafiyar irin su Dr John Ughulu inda suka ce sun nada sabon shugaba me suna High Chief Peter Ameh a matsayin sabon shugaban tafiyar. Saidai bangaren Dr John Ughulu yace basu koru ba har yanzu shine shugaban Tafiyar. Hakanan Sabbin wanda suka kawo tarnaki a tafiyar sun ce sun kori shugaban gudanarwar tafiyar, Dr Yunusa Tanko amma yace bai koru ba, kamar yanda kafar Daily post ta ruwaito.
Bidiyon Sule Naci da Sayyada Sakina

Bidiyon Sule Naci da Sayyada Sakina

Duk Labarai
Wannan ne Bidiyon Sule Naci da Sayyada Sakina da ya jawo cece-kuce sosai da zazzafar Muhawara a kafafen sadarwa. https://www.tiktok.com/@celentaraba3354/video/7668005803244195093?_r=1&_t=ZS-98SvgXtNE17 Me Dina collection ta zargi cewa da gangan Sule Naci ya saki Bidiyo Nanaye da suka yi da Sayyada Sakina dan ya bata mata suna. Tace dan yaga tana daukaka tana yabon Nana Fadima(AS) shiyasa ya mata haka Dan haka tace zata dauki matakin Shari'a a kansa sai ta kwatarwa Sayyada Sakina hakkin bata suna da ya mata. Ga wadanda basu sani ba, An san Sayyada Sakina da Yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Kwatsam sai aka ga Bidiyon nanaye da waka da barkwanci da suka yi ita da Sule Naci suna tattaba juna. Rahotanni sun ce Sule Naci ne ya fitar da Bidiyon wanda hakan ya jawo...