Kwamitin Majalisar Wakilai Ya Bada Shawarar Samawa Tinubu Da Shettima Sabbin Jiragen Sama
Kwamitin Majalisar Wakilai akan Tsaron Kasa da Tattara Bayanan Sirri ya bukaci gwamnatin tarayya ta sayawa Shugaban Kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sabbin jiragen sama.
Shawarar kwamitin na kunshe ne a cikin rahoton da kwamitin ya fitar bayan gudanar da bincike akan lafiyar jiragen saman fadar shugaban kasa.
A watan Mayun daya gabata, majalisar wakilan ta umarci kwamitin ya gudanar da cikakken bincike akan jiragen saman fadar shugaban kasar domin tantance lafiyarsu.
Shawarar ta biyo bayan kudirin da Dan Majalisa Satomi Ahmad ya gabatar, wanda aka tafka mahawara akan sa.
Wasu daga cikin 'yan majalisar sun bada shawarar cewar kamata yayi shugaban kasar ya rika shiga jirgin sama ko motar haya idan zai yi balaguro.
Kudirin na Satomi Ahmad ya biyo bayan rahoton s...