Kotun Ƙolin Amurka ta amince da amfani da ƙwayoyin zubar da ciki
Bakin Alƙalan Kotun Ƙolin Amurka yazo ɗaya wajen amincewa da amfani da ƙwayoyin zubar da ciki.
Wani lamari da ake gani a matsayin nasara ga masu fafutukar 'yancin zubar da ciki.
Kotun ta yi watsi da buƙatar ƙungiyoyin likitoci masu yaƙi da zubar da ciki da kuma 'yan gwagwarmaya da suke neman a taƙaita amfani da maganin Mifepristone.
Kotun kolin ta ce ƙungiyoyin likitocin ba su da 'yanci shigar da ƙara kan hakan, kuma sun gaza gabatar da hujjojin cewa maganin Mifepristone yana cutarwa.
Wannan ne babban hukuncin da kotun ta yanke, tun watsi da 'yancin zubar da ciki da kotun tarayyar ƙasar ta yi shekara biyu da suka gabata.