Kalli Bidiyon: Tauraron dake fadakarwa a Tiktok, Dr. Hussain Kano ya bayyana cewa yana son Tauraruwar mawakiya, Fati Nijar da aure
Tauraron dake fadakarwa a kafafen sadarwa, Dr. Hussain Kano ya bayyana cewa, yana son Tauraruwar mawakiyar Hausa, Fati Nijar
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo daya wallafa inda yace indai tana sonsa, to shima yana sonta.
Yace tuni ya aika mata sakon soyayya kuma yana jiran amsarta.
https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7622380031565729031?_r=1&_t=ZS-958CXOwUaMj&sp_source=7537614245375297080








