Sunday, June 28
Shadow

Duk Labarai

Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 – NLC

Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 – NLC

Siyasa
Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 - NLC Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta ce gwamnonin jihohin ƙasar za su iya biyan foye da naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, idan suka rage cin hanci da rashawa da kuɗin da suka kashewa wajen gudanar da mulki a jihohinsu. Aranar Juma'a ne dai ƙungiyar gwmanonin ta fitar da wata sanarwar da a ciki take cewa gwamnonin jihohin ƙasar 36 ba za su iya biyan naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata ba. To sai dai a cikin martanin da ta mayar ƙungiyar ta NLC, ta yi Allah wadai da sanarwar gwamnonin. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NLC, Benson Upah,ya fitar ya ce idan gwamnaonin suka mayar da hankali babu abin da zai hana su biyan mafi ƙarancin albashin. ''Koda nawa ne mafi ƙa...
Shugaba Tinubu yace yana sane da halin matsin da ‘yan Najeriya ke ciki inda ya bayyana matakan kawo sauki da zai dauka

Shugaba Tinubu yace yana sane da halin matsin da ‘yan Najeriya ke ciki inda ya bayyana matakan kawo sauki da zai dauka

Siyasa
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sake jaddada cewa yana sane da halin matsin rayuwa da 'yan ƙasar ke fama da shi. Yayin da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamar da aikin titin Guzape Lot II, a Abuja babban birnin ƙasar ranar Asabar, shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin sauƙaƙa wa 'yan ƙasar halin matsin rayuwar da suke fuskanta. “Wannan lokaci ne mawuyaci a ƙasarmu,Har yanzu muna ƙoƙarin saisaita tsarin tattalin arzikin ƙasar, domin kawo sauƙi da ingantuwar tattalin arzikin ƙasarmu,'' in ji Shugaba Tinubu. Shugaban ƙasar ya ce kammala aikin titin alama ce ta abin da za a iya yi, ta hanyar abin da ya kira ''kyakkyawan tsari da haɗin kai da kuma aiki tare''. Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa ministan Abuja, Nyesom Wike, kan ƙoƙari da jajircewar da ya nun...
Bidiyo: Kasa karanta sabon taken Najeriya da ‘yan Kwallon Najeriya suka yi ya jawo cece-kuce

Bidiyo: Kasa karanta sabon taken Najeriya da ‘yan Kwallon Najeriya suka yi ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Bidiyon 'yan kwallon Najeriya a filin wasan da suka buga wasa da kasar Africa ta kudu ya jawo cece-kuce. Bidiyon ya nuna 'yan kwallon na Najeriya sun ki rera sabon taken ko kuma ince sun kasa rerashi. Saidai za'a iya cewa, har yanzu mutane da yawa basu kai ga iya taken ba. https://www.youtube.com/watch?v=9IGhoqFJoFM Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya bayyana cewa, canja taken na daya daga cikin muhimman ayyukan da yake son yi a Najeriya.
Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa

Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa

Siyasa, Tarihi
Yau Tsohan Shugaban Kasa Na Mulkin Soja Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Cif Da Rasuwa. A ranar 8 ga watan Yuni 1998 Allah Ya yi wa tsohan shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, Janar Sani Abacha rasuwa; Yau shekara ashirin da shidda da ke nan. Da Wadanne Irin Ayyukan Alheri Ku Ke Tunawa Da Shi? Allah Ya Jikansa Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa
Dole a samar da inshola ga masu haƙar ma’adanai – Gwamnatin Najeriya

Dole a samar da inshola ga masu haƙar ma’adanai – Gwamnatin Najeriya

Siyasa
Gwamnatin Najeriya ta tilastawa kamfanonin haƙar ma'adanai yin inshola ga ma'aikatan su, domin bayar kariya gare su idan wani haɗari ya faru. Ministan ma'adanan ƙasar, Dele Alake, ya daga yanzu gwamnati ba za ta sake amincewa da lasisin duk wani kamfanin haƙar ma’adanai da bai nuna ƙwaƙwarar shaidar cika ƙa'idojin gudanar da aiki ba. Ministan ya na magana ne lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya da jaje a jihar Neja, inda ƙasa ta rufta da masu haƙar ma'adanai a ƙauyen Galkogo na ƙaramar hukumar Shiroro. Ya ce gwamnati za ta tabbatar da bin duk hanyar da ta dace domin kare afkuwar irin wannan matsala a nan gaba, dmin haka ta faraɓullo da irin wannan mataki. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja a Najeriya (NSEMA) ta ce kimanin mutum 30 ne ake fargabar sun mutu sakamakon za...
Majalisar Dinkin Duniya ta saka Kasar Israela cikin masu kisan kananan yara

Majalisar Dinkin Duniya ta saka Kasar Israela cikin masu kisan kananan yara

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Siyasa, Yakin gaza da isra'ila
Majalisar Dinkin Duniya ta saka kasar Israela cikin kasashe masu kisan kananan yara. Hakan ya biyo bayan kisan sa kasar kewa Falas-dinawa a zirin gaza. Wakilin Israela a Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan ne ya bayyana haka. Inda yace an sanar dashi matakinne ranar Juma'a. Hakanan ministan harkokin kasashen waje na kasar Israela, Katz ya bayyana cewa, zasu dauki mataki kuma wannan abu da majalisar ta yi zai canja dangantakar dake tsakaninsu da Israela.
Sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zai sauko a Najeriya>>IMF

Sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zai sauko a Najeriya>>IMF

Siyasa
Hukumar bada lamuni ta Duniya, IMF ta bayyana cewa, sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zasu sauko kasa. Tace ta yi hasashen farashin kayan masarufin zai sauko da kaso 15 cikin 100 nan da shekarar ta 2029. A yanzu dai, Alkaluman kayan masarufi a Najeriya sun kai maki 33.69 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana. Tun dai bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ne dai aka shiga tsadar rayuwa wadda har yanzu babu alamar zata kare. Ko da a jiya, saida Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, zata sake daukar matakai masu tsauri wanda ka iya kara jefa 'yan Najeriya cikin halin matsi. Saidai Gwamnatin tace wadannan matakai da take dauka kokarine na tada komadar tattalin arziki.
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira dubu sittin da biyu (62,000) a matsayin sabon tayin mafi karancin Albashi

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira dubu sittin da biyu (62,000) a matsayin sabon tayin mafi karancin Albashi

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira Dubu sittin da biyu a matsayin sabon tayinafi karancin Albashi ga kungiyar Kwadago. Hakanan Sabon rahoton ya bayyana cewa, kungiyar kwadago ta NLC ta sauko daga matsayin ta na cewa gwamnati ta biyata Naira dubu dari hudu da chasa'in da hudu(494,000) inda a yanzu tace a biyata Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000). Tuni dai kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta amince da tayin na gwamnatin tarayya watau dubu 62,000.