Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

ILMI KOGI: Nan Gaba Mutane Za Su Iýà Bacewa Kamar Àĺjàñù, Inji Shêikh Imam Habibi

ILMI KOGI: Nan Gaba Mutane Za Su Iýà Bacewa Kamar Àĺjàñù, Inji Shêikh Imam Habibi

Duk Labarai
Shugabaɲ Kungiyar Malamai Masana Ilimin Taurári na Nájeriya, Shéikh Imam Habibi Abdallah Assufiyyu ya bayyana cewa "mun gano céwa kowanne ɗan Adam yana ɗauke da wata lambar sirri wacce Ubaɲgiji ya halicce shi da ita, da mutane za su iya tantance nasu da kowa zai iya bacéwa kamar yadda jinsin aljannu ke bacewa, kuma da kowa zai iya magana da dan uwansa ba tare da kiran waya ba ko haduwa ta zahiri a ko'ina suke a doran kasa " Shehin Malamin ya kara da cewa "da yiwuwar hakan zai fara kasancewa a shekaru masu zuwa". Me za ku ce?
Saboda matsalar tsaro: Gwamnatin tarayya ta umarci ministan tsaro da shuwagabannin sojoji su koma Sokoto da zama

Saboda matsalar tsaro: Gwamnatin tarayya ta umarci ministan tsaro da shuwagabannin sojoji su koma Sokoto da zama

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta umarci shuwagabannin sojoji da su koma jihar Sokoto da zama. Hakan na zuwa ne yayin da matsalar tsaro musamman ta garkuwa da mutane ke kara kamari a yankin arewa maso yamma. Sanarwar hakan na kunshene a cikin bayanan da sakataren yada labarai, Henshaw Ogubike ya fitar. Yace wannan kokari ne na kawar da matsalar ta'addanci da garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro da ake fama dasu a yankin. Gwamnatin ta bayyana takaici da matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a yankin na Arewa maso yamma inda tace wannan mataki alamu ne na daukar matsalar da muhimmanci da gwamantin ta yi.
Sojoji Śun Ķashe ‘Ýan Ța’àďda 1,166, Yayin Da Suka Kama 1,096, Inji Hedikwatar Tsaro

Sojoji Śun Ķashe ‘Ýan Ța’àďda 1,166, Yayin Da Suka Kama 1,096, Inji Hedikwatar Tsaro

Duk Labarai
Daga Bello Abubakar Babaji Hedkwatar tsaro (DHQ) tace jami’anta sun kashe ƴan ta’adda guda 1,166 tare da tsare wasu 1,096 acikin kwana 29 a faɗin Nijeriya. Daraktan watsa labarai na ofishin, Manjo-Janar Edward Buba ya faɗi hakan a Abuja, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai kan ayyukan jami’an tsaro, a ranar Alhamis. Ya ce, jami’an sun yi nasarar ceto mutane 721 da aka yi garkuwa da su. Sannan, sun kuma ƙwato makamai 391 da wasu nau’ukan bindigu da kayan yaƙi da adadinsu ya kai 15,234 acikin wata guda. Ya ƙara da cewa, sun yi nasarar kamo manyan ƴan ta’addan da kwamandodinsu a yayin gudanar da ayyukansu cikin watan. Waɗanda aka kama a yankin Arewa-maso-Gabas sun haɗa da; Munir Arika, Sani Dilla (aka Ɗan Hausawan Jibilarram), Ameer Modu, Ɗan Fulani Fari Fari, Bakour...
Masana’antar Kannywood Ta Samu Ƙaruwar Galleliyar Sabuwar Jaruma Daga Jihar Bauchi

Masana’antar Kannywood Ta Samu Ƙaruwar Galleliyar Sabuwar Jaruma Daga Jihar Bauchi

Duk Labarai
Jarumar mai suna Sadiya Abdulƙadir wacce aka fi sani da (Sareena) sabuwar Jaruma ce duk da cewa ta ɗan kwana biyu a masana'antar ta Kannywood ana damawa da ita a fagen shirya fina-finan Hausa wadda ƴar asalin Jihar Bauchi ce ƙaramar hukumar Azare. Fim na farko da ta fara yi tun bayan shigowarta masana'antar fim ne mai dogon zango mai suna (Aliya) wanda ake haska shi a (Youtube Channel) na Ali Jita, wato (Ali Jita Multimedia). Yanzu haka dai Jarumar ta faso gada-gadan da zafinta domin cigaba da aikinta na faɗakarwa cikin fina-finan Hausa domin inganta tarbiyyar al'umma. Photo Credit: Dk Photography Wane fata zaku yi mata ?
Hotuna: An kamasu suna yiwa karuwai Fashi da makami

Hotuna: An kamasu suna yiwa karuwai Fashi da makami

Duk Labarai
An kama wadannan mutanen da zargin yiwa karuwai 3 fashi da makami. Lamarin ya farune a titin Adeniran Ogunsanya dake Bode Thomas a Surulere ta jihar Legas. Ranar 23 ga watan Augusta ne dai wanda ake zargin suka dauki karuwan 3 da niyyar zasu je su yi lalata dasu. Ko da suka shiga wani wuri sai suka tsayar da motarsu suka kwace musu wayoyi da kudade. Karuwan dai sun kai kara wajan 'Yansanda inda suka ce sun gane fuskokin wanda suka musu satar. Kuma an kamasu. Kakakin 'yansandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarun.
Kalli Bidiyo: ‘Yan Shi’a sun koka kan cirewa matansu hijabi da ‘yansanda suka yi a Abuja

Kalli Bidiyo: ‘Yan Shi’a sun koka kan cirewa matansu hijabi da ‘yansanda suka yi a Abuja

Duk Labarai
Kungiyar 'yan uwa musulmi da aka fi sani da shi'a aun koka kan cirewa matansu Hijabi da 'yansanda suka yi a Abuja. Kungiyar tace wannan cin zarafine da kuma batanci ga addinin musulunci. Wakiliyar mata ta kungiyar 'yan uwa musulmi, Maryam Sani ta bayyana a wata sanarwa data fitar cewa zasu yadawa duniya wannan lamari a gani. https://www.tiktok.com/@asmat.muhd/video/7408970047680498950?_t=8pKCn6Pj8sg&_r=1 Kuma zasu kai maganar kotu. Bidiyo dai ya bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ga 'yansanda na cirewa matan 'yan shi'ar Hijabi ta karfin tsiya.

Ji yanda Dan shekaru 32 ya kashe kansa a Najeriya

Duk Labarai
Wani magidanci dan shekaru 32 ya kashe kansa a garin Kemta dake Abeokuta jihar Ogun. Lamarin ya farune da misalin karfe 10 na daren ranar Laraba kamar yanda kakakin 'yansandan jihar, Omolola Odutola ya tabbatar. Matar mamacin ce ta iskeshi a rataye ba rai. 'Yansanda sun so su yi bincike amma iyalan mamacin suka kwace gawar suka ce zasu binne saidai hukumar 'yansandan tace tana bibiyar lamarin.