Hotuna: Hukumar Hisbah A Jihar Kano Ta Cafke Shahararren Dan TikTok Mai Rawa Da Mata Lawancy
Hukumar Hisbah A Jihar Kano Ta Cafke Shahararren Dan TikTok Mai Rawa Da Mata Lawancy.
A ci gaba da sumamen tsaftace kafafen sada zumunta da Hukumar Hisbah ta jihar Kano ke yi, ta cafke matashin nan Rabi'u Sulaiman da aka fi sani da Lawancy.
Hisbah na zarginsa da ci gaba da raye-rayen baɗala da riƙe hannun mata a bidiyo.
Idan za ku iya tunawa ko a shekarar 2023 ma Hisbah ta taɓa kama shi, amma ya nemi afuwa ya ce ya tuba.