Tuesday, April 21
Shadow

Kalli Bidiyon: Ashe Ministan Kudi, Wale Edun, Karyata shugaba Tinubu yayi shiyasa aka saukeshi

A dazune dai hutudole ya kawo muku rahoton cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sauke ministan kudi, Wale Edun daga mukaminsa.

Gwamnati dai bata bayyana dalilin sauke shi daga mukamin nasa ba a hukumance.

Lamarin ya zowa mutane da mamaki duk da yake cewa a kwanakin baya an yi ta rade-radin cewa, Ministan yayi fama da rashin lafiya.

Saidai a yanzu a kafafen sada zumunta, ana ta yada wani Bidiyo daya nuna shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana cewa sun cimma yawan kudin shiga da suke nema a shekarar 2025.

Saidai a wani Bidiyo daban kuma, an ga Ministan kudin, Wale Edun na cewa Tiriliyan 40 suke nema a shekarar 2025 amma kudin shiga Tiriliyan 10 kacal suke tsammani.

Karanta Wannan  Akwai yiyuwar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai fasa yafewa Maryam Sanda bayan da cece-kuce yayi yawa akan yafiyar da aka ma

Wannan magana ta ci karo data shugaban kasa, wadda wannan yasa wasu ke ta hasashen cewa, dalili kenan da yasa shugaban ya sauke Wale Edun daga mukaminsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *