Thursday, December 18
Shadow
Ku tashu tsaye ku kare kanku, Babu maganar biyan kufin fansa ko Sulhu>>Gwamnan Jihar Naija, Umar Bago ya gayawa mutanen jihar

Ku tashu tsaye ku kare kanku, Babu maganar biyan kufin fansa ko Sulhu>>Gwamnan Jihar Naija, Umar Bago ya gayawa mutanen jihar

Duk Labarai
Gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya baiwa mutanen jiharsa shawarar su tashi tsaye su kare kansu. Yace matsalar garkuwa da mutane dan neman kudin fansa a jihar ya kai matakin yaki inda yace dole sai an tashi tsaye. Gwamnan yace, ba zai biya kudin fansa ba kuma babu maganar sulhu da 'yan Bindigar yace idan aka rika basu kudi, zasu mayar da abin kasuwanci. Gwamna Bago yace kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowane dan kasa damar kare kansa da Dukiyarsa.
Kalli Bidiyon:Yanda tsohon shugaban kasar Fransa Nicolas Sarkozy ya fara zaman gidan yari na shekaru 5 bayan da aka sameshi da laifin karbar kudin yakin neman zabe ta hanyar da bata dace ba

Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy ya fara zaman gidan yarin da aka yanke masa na tsawon shekaru 5. An sameshi da laifi ne na karbar kudin yakin neman zabe ba ta hanyar data dace ba. Wannan dauri da aka masa shine irinsa na farko a tsakanin shuwagabannin kasar ta faransa a cikin shekarun bayabayannan. Kalli Bidiyon anan https://www.youtube.com/watch?v=IEWMOqQs2pU?si=wl8g-yvmNRBuwenW
Kalli Bidiyo: Rykhichi ya kunno kai a kungiyar Izala inda aka samu wasu matasan malamai suka gayawa Sheikh Farfesa Sani Rijiyar Lemu maganganu marasa dadi

Kalli Bidiyo: Rykhichi ya kunno kai a kungiyar Izala inda aka samu wasu matasan malamai suka gayawa Sheikh Farfesa Sani Rijiyar Lemu maganganu marasa dadi

Duk Labarai
Rikicin cikin gida ya kunno kai a kungiyar Izala. Malam Ibrahim Matayassara ne ya fito ya ce yana jawo hankali ga Farfesa Sheikh Sani Rijiyar Lemu da cewa ya rika girmama malamai na zamaninsa ya daina tunanin shine ya fi owa ilimi. Sannan Yace shi fadakarwa ce yayi ga Sheikh Rijiyar Lemu ba rashin kunya ba. https://www.tiktok.com/@isah_bello_assalafy_garo/video/7563743936150310164?_t=ZS-90m2FmtZd9l&_r=1 Saidai lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu malamai suka fito suka yi Allah wadai da wadannan kalamai nasa https://www.tiktok.com/@sheikmurtala01/video/7564029374526196999?_t=ZS-90m1xKLFhJo&_r=1
Abubuwa na ci gaba da kankama, Kalli Bidiyon yanda akawa Maiwushirya da ‘YarGuda gwaji a Asibiti

Abubuwa na ci gaba da kankama, Kalli Bidiyon yanda akawa Maiwushirya da ‘YarGuda gwaji a Asibiti

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana inda aka ga yanda akawa Maiwushirya da 'YarGuda Gwaji a Asibiti a ci gaba da shirin aurensu. https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7564102158837091604?_t=ZS-90m17FI9oP3&_r=1 Hakanan an ga sun je ofishin shugaban Hisbah na Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa inda ya fati matakan da za'abi a kai ga auren. Kotu dai tace nan da kwana 90 za'a daura auren.
Kalli Bidiyon: Abin Kunya, wasu ‘yan Najeriya suka rika rokon ‘yan kwallon kafar kasar Africa ta Kudu abinci a jihar Ogun

Kalli Bidiyon: Abin Kunya, wasu ‘yan Najeriya suka rika rokon ‘yan kwallon kafar kasar Africa ta Kudu abinci a jihar Ogun

Duk Labarai
Bidiyon abin kunyar da ya faru a jihar Ogun na ta yawo a kafafen sadarwa inda aka ga 'yan Najeriya na rokon 'yan kwallon kafar kasar Africa ta Kudu abinci. 'Yan kwallon wanda suka je filin kwallo na MKO Abiola dake Abeokuta dan wasa da Remo Stars sun rika jefawa 'yan Najeriyar sauran abincin da suka ci suka rage. Da yawa dai sun yi Allah wadai da mutanen. Kalli Bidiyon anan https://www.youtube.com/watch?v=cq1Y4xEJEDo?si=MlWRJFlqZGtx8RYH
Kalli Bidiyo: Tauraruwar Tiktok Habiba Dorayi ta fito ta bayar da hakuri game da Bidiyon da aka ga tana Bhatsaa a ciki wanda ya yadu sosai

Kalli Bidiyo: Tauraruwar Tiktok Habiba Dorayi ta fito ta bayar da hakuri game da Bidiyon da aka ga tana Bhatsaa a ciki wanda ya yadu sosai

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Habiba Dorayi ta fito ta bayar da hakuri game da Bidiyon ta na batsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta. Habiba a Bidiyon data wallafa a shafinta na Tiktok tace hukumar tace fina-finan Kano ta nusar da ita cewa abinda ta yi bai dace ba. Tace dan haka tana baiwa duk masoyanta hakuri kuma hakan ba zai sake faruwa ba.
A karin farko, An ga Sauro a kasar Iceland

A karin farko, An ga Sauro a kasar Iceland

Duk Labarai
Rahotanni sun ce a karin farko an ga Sauro a kasar Iceland. Kasar Iceland dai itace daya tilo da babu sauro a Cikin a tsakanin kasashen Duniya. Dalili kuwa shine kasar na da tsananin sanyi wanda sauro baya iya rayuwa a ciki. Sannan kuma basu da ruwa dake kwanciya sosai wanda shima hakan na taimakawa wajan tara sauro. Saidai duk da haka gashi a karin farko a yanzu an ga sauro a kasar.