Monday, December 15
Shadow
Ba gaskiya bane, Ban ce zan janye wa kowa daga takarar shugaban kasa ba>>Atiku Abubakar

Ba gaskiya bane, Ban ce zan janye wa kowa daga takarar shugaban kasa ba>>Atiku Abubakar

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya musanta rahotanni dake yawo cewa wai yace zai janye wa matashi yayi takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC. Atiku ta bakin me magana da yawunsa, Paul Ibe yace wannan magana ba gaskiya bace. Yace a hirar da yayi da BBC babu inda yace zai janyewa wani dan takara, yace abinda ya fada shine idan aka yi zaben fidda gwani kuma matashi yayi nasara a zaben zai goya masa baya. Atiku yayi kira ga 'yan Jarida su daina fassara labari ba yanda ya kamata ba.
Ku hadani da Yahya Haifan, Naji yana cika bakin a cikin mintuna 5 zai iya kare Malam Lawal Triumph>>Inji Malama Jamila Abubakar

Ku hadani da Yahya Haifan, Naji yana cika bakin a cikin mintuna 5 zai iya kare Malam Lawal Triumph>>Inji Malama Jamila Abubakar

Duk Labarai
Malama Jamila Abubakar ta nemi a hadata da Malam Yahya Haifan su yi maqabala. Malama ta bayyana hakane inda take tuhumar Haifan kan cewa a cikin mintuna 5 zai warware zargin da akewa Malam Lawal Triumph. Malama Jamila ta zargi 'yan Izala da Ta'addanci. Kalli Bidiyon jawabinta anan https://vt.tiktok.com/ZSDK5XaTt
Soke Faretin Sojoji na ranar ‘yanci ya bani damar yin bacci da cin abincin safe da kyau>>Inji Shugaba Tinubu

Soke Faretin Sojoji na ranar ‘yanci ya bani damar yin bacci da cin abincin safe da kyau>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, soke faretin sojoji na ranar 'yanci ya bashi damar yin bacci da kyau da kuma in abincin safe da kyau. Shugaban ya bayyana hakane yayin bude wani dakin kimiyyar zane-zane da aka sakawa sunan Wole Soyinka. Fadar Shugaban kasa tun kamin ranar 'yanci ta sanar da cewa, babu faretin sojoji da aka saba yi.
DJ ya dakatar da kida bayan da aka hanashi Abinci a wajan taro

DJ ya dakatar da kida bayan da aka hanashi Abinci a wajan taro

Duk Labarai
Wani DJ me saka kida, ya dakatar da kida a wajan bikin da ya je bayan da aka hanashi abinci yayin da ake ta baiwa sauran mutanen abinci. DJ din ya dakatar da kidan sannan ya kashe Janareta dan ya nuna fushinsa. A wani Bidiyonsa da ya watsu a kafafen sada zumunta, an ga DJ din yana kumfar baki da fadin cewa, ba'a masa adalci ba. Saidai daga baya an bashi baki inda aka masa alkawarin samar masa da abinci da zai ci.
Maza sun yi karanci dole mata su hakura a rika auren 4>>Inji Tauraruwar fina-finan Kudu, Bimbo Akintola

Maza sun yi karanci dole mata su hakura a rika auren 4>>Inji Tauraruwar fina-finan Kudu, Bimbo Akintola

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Kudu, Bimbo Akintola ta bayyana cewa, maza sun yi karanci dan haka dolene mata su hakura a rika yin auren mata 4. Tace hakan ne zai kawo saukin dadewar mata da suke yi a gidajen iyayensu ba tare da aure ba. Ta bayyana cewa, bayan haka ma auren mace fiye da daya al'adar Yarbawa ce dan haka ya kamata a ci gaba da dabbaka wannan al'ada.