Wednesday, December 25
Shadow
Kwamitin Majalisar Wakilai Ya Bada Shawarar Samawa Tinubu Da Shettima Sabbin Jiragen Sama

Kwamitin Majalisar Wakilai Ya Bada Shawarar Samawa Tinubu Da Shettima Sabbin Jiragen Sama

Siyasa
Kwamitin Majalisar Wakilai akan Tsaron Kasa da Tattara Bayanan Sirri ya bukaci gwamnatin tarayya ta sayawa Shugaban Kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sabbin jiragen sama. Shawarar kwamitin na kunshe ne a cikin rahoton da kwamitin ya fitar bayan gudanar da bincike akan lafiyar jiragen saman fadar shugaban kasa. A watan Mayun daya gabata, majalisar wakilan ta umarci kwamitin ya gudanar da cikakken bincike akan jiragen saman fadar shugaban kasar domin tantance lafiyarsu. Shawarar ta biyo bayan kudirin da Dan Majalisa Satomi Ahmad ya gabatar, wanda aka tafka mahawara akan sa. Wasu daga cikin 'yan majalisar sun bada shawarar cewar kamata yayi shugaban kasar ya rika shiga jirgin sama ko motar haya idan zai yi balaguro. Kudirin na Satomi Ahmad ya biyo bayan rahoton s...

Ana warkewa daga ciwon zuciya

Ciwon Zuciya
Ya danganta da irin ciwon zuciyar daya kamaku, mun yi bayani akan kalolin ciwon zuciya da ake dasu, Alamomin ciwon zuciya Idan ciwon zuciyar Coronary artery disease ne ya kamaka, maganar gaskiya ta masana kiwon lafiya sun ce ba'a warkewa daga kalar wannan ciwon zuciya. Yanda zaka san kalar ciwon zuciyar da ya kamaka shine ka yi magana da likitanka ko kuma ka karanta takardar sakamakon gwajin da aka maka. Da zarar likitoci sun tabbatar da cewa wannan kalar ciwon zuciyar ne kake dashi to bai da magani, saidai akwai hanyoyin da ake bi dan kada wasu sauran matsaloli irinsu bugun zuciyar farat daya ya kama mutum. Masana sun ce idan irin wannan ciwon zuciya ya kamaka, yana da kyau ka rika kula da cin abinci me gina jiki, ba komai zaka rika ci ba. Motsa jiki akai-akai shima yana ta...

Alamomin ciwon zuciya

Ciwon Zuciya, Duk Labarai
Ciwon zuciya ya danganta da irin zuciyar, akwaishi kala-kala. Dan haka bari mu bayyana alamomin ciwon zuciya daban-daban. Akwai wanda ake kira da Coronary artery disease: Wannan kalar ciwon zuciya ne dake taba hanyoyin dake baiwa zuciyar jini. Wannan kalar ciwon zuciya shine wanda yafi kama mutane kuma yakan kai ga Bugawar Zuciya da ke iya kaiwa ga mutuwa, Yakan kuma kai ga ciwon kirji, ko shanyewar rabin jiki. Alamomin wannan ciwon zuciya ya banbanta a tsakanin mata da maza, misali, idan ya kama maza, zasu iya fuskantar ciwon kirji, yayin da idan ya kama mata, zasu iya fuskar Ciwon kirjin da karin wasu matsaloli da suka hada da numfashi sama-sama, da yawan zazzabi da safe da kuma matsananciyar kasala. Ga dai alamomin ciwon zuciya na Coronary artery disease dake damun maza d...

Kumburin kafa ga mai ciki

Haihuwa, Laulayin ciki
Mai ciki zata yi fama da kumburin kafa, musamman idan cikin ya fara girma. Hakan na faruwane saboda nauyin abinda ke cikinta. Hakan nasa jini ya rage gudana a kafarki, Musamman idan ana yanayim zafi ko kuma kin dade a tsaye. Bayan girman da abinda ke cikinki yake yi, a yayin da kike da ciki, yawan ruwan dake jikinki yana karuwa. Hakan kuma nasa ciwon kafa. Kafa da gwiwoyinki da tafin kafa da yatsu duk zasu iya kumbura. Yayin da cikinki ke kara girma, kumburin shima zai rika karuwa a hankali. Saidai wannan kumburi idan dai ba ya wuce lissafi ba, bashi da cutarwa ga Mahaifiya ko abinda ke cikinta. Alamomin dake nuna kumburin me ciki me cutarwane kuma yana bukatar kukawar likita Idan lokaci guda kumburin ya karu a fuska, hannu da tafin kafa. Idan ciwon kai me tsa...

Alamomin cikin wata tara

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 9, abinda ke cikinki na da cikakkiyar halittar Idanu kuma za'a iya cewa ya cika mutum. A wata 9, abinda ke cikinki ya kai tsawon 12 inches ko ace 30 cm Idanun sun yi kwari sosai zasu iya kallon komai. Gashin da ya lullube jikin jaririn kusan za'a iya cewa ya gama zubewa. Hakanan fatar jikin jaririn ta yi kwari. Yayin da cikin ki ya kai wata tara, zai ci gaba da yi miki nauyi. Alamomin daukar ciki, irin su nankarwa, Rashin lafiyar safe, Kasala, kasa rike fitsari, da sauransu zasu ci gaba har zuwa a haihu. Abinda ke cikinki zai iya yowa kasa, wanda hakan zai rage miki wahalar yin kashi da zafin kirji ko zuciya. Saidai cikin wasu matan bai yo kasa har sai nakuda ta tashi.
Cutar Amai da gudawa ta barke a Najeriya, mutane 65 sun kamu, 30 sun mu-tu

Cutar Amai da gudawa ta barke a Najeriya, mutane 65 sun kamu, 30 sun mu-tu

Tsaro
Daga watan Janairu na shekarar 2024 zuwa 14 ga watan Yuni Mutane 65 ne suka kamu da cutar amai da gudana inda guda 30 suka mutu. An samu cutarne a kananan hukumomi 96 da ke jihohi 30 a fadin Najeriya kamar yanda hukumar kula da cututtuka ta kasa, NCDC ta bayyanar. Hukumar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ranar Alhamis dan ankarar da mutane kan lamarin inda tace a yi hankali saboda zuwan ruwan sama.
Hoto: Wannan matashin ya yi garkuwa da kansa ya karbi Naira Miliyan 5 daga gurin mahaifinsa

Hoto: Wannan matashin ya yi garkuwa da kansa ya karbi Naira Miliyan 5 daga gurin mahaifinsa

Tsaro
Wannan wani matashine dan kimanin shekaru 20 wanda ya yi garkuwa da kansa. https://www.youtube.com/watch?v=QMoREHNRpDM?si=Z_vLHKGDPEAc2llB Matashin dai ya jada baki da wanine inda aka kamashi aka daure aka kuma rika dukansa. An nemi mahaifinsa ya biya Naira Miliyan 50 wanda daga baya aka ce ya biya Miliyan 5 ta hanyar Bitcoin. Bayan biyan kudin, asirin matashin ya tonu:

Alamomin cikin wata takwas

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 8, abinda ke cikinki ya kai tsawon 11 inches. A daidai lokacinne wani gashi me laushi dake lullube da abinda ke cikinki zai fara zubewa. Idan namiji ne, a wannan lokacinne marainansa zasu zazzago kasa. A wannan watanne zaki rika jin gajiya, sannan zaki rika nishi da kyar. Jijiyoyi zasu iya fitowa rado-rado musamman a kafarki. Zaki iya samun nankarwa. Zafin kirji ko zafin zuciya na iya ci gaba, hakanan zaki iya ci gaba da fama da wahala wajan yin kashi. Fitsari zai iya zubowa yayin da kika zo yin atishawa ko kuma kike dariya. Wadannan abubuwanne zaki yi fama dasu yayin da cikinki ya kai watanni 8.

Alamomin cikin wata uku

Laulayin ciki
Idan cikinki ya kai watanni 3 zai zama yana da tsawon 2–3 inches ko kuma a ce 6–7.5 cm. Yatsun hannuwa dana kafa zasu warware. Kasusuwan abin cikinki zasu fara yin karfi. Fata da farata zasu fara fitowa. Alamun jinsin abinda ke cikinki zasu fara bayyana. Koda zata fara samar da fitsari. Alamun sweat glands zasu bayyana. Ido zai zama a kulle. Duka alamun daukar ciki daga wata na 2 zaki ci gaba da ganinsu a wata na 3 kuma zasu ma iya kara tsanani. Zaki ci gaba da fama da rashin lafiya da safe. Nonuwanki zasu ci gaba da girma. Kan nononki zai kara girma ya kuma kara baki. Nauyinki ba zai karu ba sosai a wata na 3. Mafi yawancin barin ciki na farko-farko ana yinshine a wata na 3.

Alamomin cikin wata biyu

Haihuwa, Laulayin ciki
A sati na 5 zuwa 6, abinda ke cikinki zai fara canjawa inda zai shiga matakin Embryo wanda daga wannan mataki ne za'a fara halitta. Zai dunkule a waje daya wanda zai zama kamar zuciya amma bai gama zama zuciyar ba. Idan aka duba a ma'aunin Ultrasound za'a iya jin yana motsi kamar zuciya. Alamun fitowar hannuwa da kafafu zai bayyana. Halittar da Kwakwalwa, jijiyoyi da sauran manyan sassan jiki zasu fita daga ciki zata bayyana. Alamar bindi zata bayyana. Ya yin da cikin ya cika sati 8, watau wata biyu daidai, zuciya zata bayyana Yatsun hannu da na kafa zasu fara bayyana. Ido, kunne, marfin ido ko fatar ido zasu fara bayyana. Da leben sama. A wata na biyu, har yanzu alamomin daukar ciki suna nan tare dake kamar su zafin nono, kasala, yawan fitsari, zafin kirji ko zuciy...