Saturday, December 13
Shadow
Kalli Bidiyo: Cikin sahabban Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) babu wanda ya rika cewa shi Ahalussunnah ne ya rika kafirta sauran sahabbai>>Inji Digital Imam

Kalli Bidiyo: Cikin sahabban Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) babu wanda ya rika cewa shi Ahalussunnah ne ya rika kafirta sauran sahabbai>>Inji Digital Imam

Duk Labarai
Malamin addinin Islama, Digital Imam ya bayyana cewa, a cikin Sahabban Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam babu wadanda suka rika ikirarin Ahlussunah suka rika kafurta sauran Sahabbai. Malam yace ikirarin Ahlussunah daga baya ya fito. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7551058248858619143?_t=ZS-8zqp1hX5n05&_r=1
Kalli Bidiyo: Ta aikawa Malam ya baiwa Mijinta Hakuri bayan da ya hanata kudin anko da kudin gudummawar zuwa bikin kawarta amma ta sayar da buhun shinkafa ta tafi

Kalli Bidiyo: Ta aikawa Malam ya baiwa Mijinta Hakuri bayan da ya hanata kudin anko da kudin gudummawar zuwa bikin kawarta amma ta sayar da buhun shinkafa ta tafi

Duk Labarai
Wata mata da mijinta ya ki bata kudin gudummawa dana Anko zuwa wajan bikin kawarta ta sayar da buhun shinkafa ta yi hidimar bikin. Saidak bayan data dawo daga wajan bikin, ya dauke mata duka kayanta inda yace sai ta shekara 2 tana saka wadannan kayan kamin ya fito mata da kayanta. Tace ta gayawa mahaifinta kuma yace mijin yayi daidai. Shine ta aikawa malam ya baiwa mijin hakuri. https://www.tiktok.com/@mariamelhadjigomb/video/7550917552537423126?_t=ZS-8zqnVya4ktN&_r=1
Kalli Bidiyon yanda rikici ya barke tsakanin mawaki 442 da wata data zargi cewa watakila Baturiyar da yace ya musuluntar ba da gaske bane, Neman Trending ne

Kalli Bidiyon yanda rikici ya barke tsakanin mawaki 442 da wata data zargi cewa watakila Baturiyar da yace ya musuluntar ba da gaske bane, Neman Trending ne

Duk Labarai
Tauraron mawaki, 442 ya nuna bacin randa bayan da wata ta zargi cewa baturiya da yace yana son musuluntar da ita ba gaskiya bane. 442 dai yace wata baturiya da aka gansu tare tace tana son musulunta. Wata me suna Jaruma ta fito tace watakila neman trending ne 442 yake amma ta bashi shawarar ya kai baturiyar Masallaci a musuluntar da ita https://www.tiktok.com/@hassana.jaruma/video/7550586198067072278?_t=ZS-8zqFeG3rKFM&_r=1 Wannan magana ta batawa 442 rai inda yace da gaske ne maganar musuluntar Baturiyar. https://www.tiktok.com/@mr442_/video/7551398969784503570?_t=ZS-8zqFjb9psXJ&_r=1
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara jihar Kaduna, Gobe Juma’a

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara jihar Kaduna, Gobe Juma’a

Duk Labarai
Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara jihar Kaduna a gobe, Juma'a idan Allah ya kaimu. Shugaban zai halarci daurin auren dan Sanata Abdulaziz Yari me suna Nasirudeen Yari da amaryarsa, Safiyya Shehu Idris. Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar 18 ga watan Satumba. Hakanan sanarwar tace shugaban kasar zai kuma kaiwa matar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari ziyara. Sannan a Ranar Juma'ar dai ne shugaban zai koma Abuja.
Atiku Abubakar ya hadu da Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya, ya ce ya dauki nauyin karatunta

Atiku Abubakar ya hadu da Nafisa Abdullahi data lashe gasar Turanci ta Duniya, ya ce ya dauki nauyin karatunta

Duk Labarai
Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya gana da Nafisa Abdullahi wadda ta lashe gasar Turanci ta Duniya. Yace ganawar ta kasance a gidansa dake Abuja insa yace ya dauki nauyin karatunta dana sauran wanda suka ci yo gasar tare. Hakan na zuwane bayan da aka ga daliban an basu kyautar naira dubu dari biyu a ma'aikatar ilimi ta tarayya
Kalli Bidiyon ganawar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da wani Inyamuri da suka yi magana da Hausa, Abin ya dauki hankula

Kalli Bidiyon ganawar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da wani Inyamuri da suka yi magana da Hausa, Abin ya dauki hankula

Duk Labarai
Bidiyon Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a wani gidan mai tare da wani Inyamuri ya dauki hankula. A Bidiyon an ji Kashim Shettima na magana da mutumin da Hausa inda yake ce masa babu maganar Biafra kuma babu wanda zai koreshi daga Arewa. https://twitter.com/masuzafi/status/1968580980609798564?t=Ry_c8NdIQeG2Xo8ha2VMLQ&s=19
Gwamnatin Najeriya ta mayar da darasin tarihi a firamare da sakandare

Gwamnatin Najeriya ta mayar da darasin tarihi a firamare da sakandare

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta sake mayar da darasin tarihi a matsayin darussan dole da ɗalibai za su dinga yi makarantun firamare da sakandare na ƙasar. Wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta fitar a ranar Laraba ta ce an ɗauki matakin ne domin "ƙarfafa kishi, da haɗin kai tsakanin 'yan ƙasa". "A karon farko ɗaliban Najeriya za su fara yin darasin tarihi tun daga aji 1 na firamare zuwa aji 3 na ƙaramar sakandare [JSS3], yayin da 'yan aji 1 zuwa 3 [SS1 zuwa SS3] za su dinga yin darasin ilimin rayuwa da tsatso [Civic and Heritage Studies]," in ji sanarwar da ta wallafa a shafukan zumunta. "'Yan aji 1 zuwa 6 na firamare za su san asalin Najeriya, da gwanayenta, da shugabanni, da al'adu, da siyasa, da addini, da mulkin mallaka, da kuma mulki bayan samun 'yancin kai. "Ɗaliban JSS1-3 za su naza...
Kalli Bidiyon yanda aka gano irin abinda larabawa manyan masu kudi kewa ‘yan Matan da ake kaiwa Dubai da sunan yin aiki

Kalli Bidiyon yanda aka gano irin abinda larabawa manyan masu kudi kewa ‘yan Matan da ake kaiwa Dubai da sunan yin aiki

Duk Labarai
Wani bincike da BBC ta yi ya gano yanda ake kai 'yan mata daga Afrika Dubai suna karuwanci. Binciken yace ba karuwanci kadai ake kai 'yan matan yi ba, hadda ci musu zarafi ta hanyar yin futsari da kashi a jikinsu. Hakan ya fara fitowa fili ne tun bayan da wata da aka kai ta yi irin wannan abu tace ba zata yi ba inda ta kwammace ta fado daga Bene ta mutu. Daya daga cikin irin wadannan 'yan matan da aka kai da aka yi hira da ita tace ko sun kira 'yansanda basa daukar wani mataki akan lamarin. BBC tace ta yi kokarin tuntubar 'yansandan amma basu bata hadin kai ba. https://www.tiktok.com/@abis_fulani/video/7551156980916751638?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7551156980916751638&source=h5_m&tim...