Karanta Jadawalin Jihohin Arewa 8 da suka kulle makarantu
A makon da ya gabata ne Najeriya ta yi fama da hare-hare mafi muni kan makarantu cikin ƙanƙanin lokaci.
A ranar litinin ƴan bindiga sun far wa makarantar kwana ta ƴan mata da ke garin Maga a jihar Kebbi, tare da sace ɗalibai 25.
Kwanaki ƙalilan bayan nan, a ranar juma'a, wasu ƴan bindiga a kan babura suka shiga makarantar kwana da St Mary da ke garin Papiri a karamar hukumar Agwara da ke jihar Neja, suka sace ɗalibai da malamai da ake hasashen sun kai 300.
Ƴan ƙasar na ci gaba da bayyana fushin su kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwar hare hare a makarantu da sace ƙananan yara.
Sai dai har yanzu gwamnatin ƙasar na nanata cewa ta na ɗaukar matakan dawo da waɗanda aka sace, amma har yanzu ba ta kai ga nasara ba, sai dai akwai waɗanda rahotanni suka bayyana cewa sun tsere.
Wan...








