Da Duminsa: Farashin kayan Masarufi a sauka>>Inji Hukumar NBS
Hukumar kula da kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa, farashin kayan masarufi ya sauka sosai.
Hukumar ta bayyana hakane a cikin bayanan watan Nuwamba da ta fitar ranar Litinin a shafinta.
Tace idan ak kwatanta da shekarar data gabata, alkaluman farashin kayan Masarufin na kan maki 16.05 wanda kuma a yanzu suna kan makin 14.45.








