Thursday, December 18
Shadow
Wannan Tsabar Muguntace, Inji Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu bayan da Dangote ya rage farashin man fetur dinsa zuwa Naira 740 aka kowace lita

Wannan Tsabar Muguntace, Inji Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu bayan da Dangote ya rage farashin man fetur dinsa zuwa Naira 740 aka kowace lita

Duk Labarai
Kungiyar 'yan Kasuwar man fetur masu zaman Kansu PETROAN ta yi Allah wadai da rage farashin man fetur da Dangote yayi zuwa Naira 740 akan kowace lita. Dangote ya rage farashinne daga yanzu har zuwa watan Fabrairu. Inda 'yan kasuwar suka ce hakan zai sa su rasa Kwastomominsu dakuma tafka asarar Naira Biliyan 100. Kungiyar tace sabawa doka ne ace mutum daya ne zai rika kayyade farashin man fetur a Najeriya. Tace a su kadai wannan lamari zai shafa ba haddashi Dangoten.
Kalli Bidiyon da Duminsa: Yanda Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, FCDA karkashin Wike ta kutsa da karfi cikin Ginin River Park duk da Umarnin Kotu

Kalli Bidiyon da Duminsa: Yanda Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, FCDA karkashin Wike ta kutsa da karfi cikin Ginin River Park duk da Umarnin Kotu

Duk Labarai
Hukumar babban birnin tarayya, Abuja FCDA ta rushe wani sahe na River Park sannan ta kutsa da karfi cikin ginin duk da umarnin kotu na hana hukumar shiga ginin. An ga Bidiyon faruwar lamarin wanda ya baiwa mutane mamaki. https://twitter.com/NigeriaStories/status/2001222213177933853?t=pvI_aZuJCsTxvX5Mbx_UrQ&s=19 https://twitter.com/ruffydfire/status/2001219785388966102?t=RFckjyKTTNVW2MVN0HEwfA&s=19
Ba gudu ba ja da baya sai mun yi zàngà-zàngàr da muka shirya>>Inji Kungiyar Kwadago bayan ganawa da shugaba Tinubu

Ba gudu ba ja da baya sai mun yi zàngà-zàngàr da muka shirya>>Inji Kungiyar Kwadago bayan ganawa da shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa, babu gudu ba ja da baya ta shirya tsaf dan ci gaba da zanga-zangar data shirya ayau. Hakan na zuwane bayan ganawar da kungiyar ta yi da shugaba Tinubu a daren ranar Talata. Shuganan NLC, Joe Ajaero ya bayyana wa manema labarai a hedikwatar NLC cewa zasu fita zanga-zangar da suka shirya yau ba fashi. Tuni hukumar 'yansandan Najeriya ta sanar da kai jami'an ta na musamman gurare daban-daban dan hana bata gari shiga zanga-zangar su batata.
Kalli Bidiyon: A matsayina na sarkin Wakar kasar Hausa, Daga yanzu duk wanda zai saurari waka saida Umarnina>>Inji Rarara

Kalli Bidiyon: A matsayina na sarkin Wakar kasar Hausa, Daga yanzu duk wanda zai saurari waka saida Umarnina>>Inji Rarara

Duk Labarai
Tauraron Mawakin Hausa da akawa Nadin Sarkin Wakar Qasar Hausa, Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa, daga yanzu ko sauraren waka sai da izininsa. Rarara yace idan mutum ya saurara sau daya biyu sai ya dakata ya nemi izininsa. https://www.tiktok.com/@ibrahimwisdomtv/video/7584542635965123861?_t=ZS-92I3mW6yftB&_r=1
Kalli Bidiyon: Kalaman Dr. Hussain na cewa yana son shiga Aljannah ba tare da ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba Jahilci ne da Hauka>>Inji Baffa Hotoro

Kalli Bidiyon: Kalaman Dr. Hussain na cewa yana son shiga Aljannah ba tare da ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba Jahilci ne da Hauka>>Inji Baffa Hotoro

Duk Labarai
Baffa Hotoro yawa Dr. Hussain Kano wankin babban bargo kan kalaman da yayi na cewa yana son shiga Aljannah ba tare da ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba. Baffa Hotoro yace wannan magana akwai wauta, Hauka, da Jahilci a cikinta. Ya bayyana hakane a wani Bidiyon martani da yawa Dr. Hussain Kano. Yace ko Annabi Ibrahim AS sai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ceceshi, duk da kasancewar Annabi Ibrahim AS badadin Allah ne Yace dan haka kuskurene tunanin wai me laifi ne kadai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) zai ceta a ranar tashin qiyama ko kuma ace wanda suka cancanci shiga wutane kadai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) zai ceta a ranar tashin qiyama. Yace dan haka suna baiwa Dr. Hussain Kano shawarar ya daina wa'azi, ya koma yayi karatu tukuna. https://www...
Da Duminsa: Najeriya ka iya fadawa Duhu kwanannan saboda karancin gas da kamfanonin samar da wutar lantarki ke samu

Da Duminsa: Najeriya ka iya fadawa Duhu kwanannan saboda karancin gas da kamfanonin samar da wutar lantarki ke samu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanonin dake samar da wutar lantarki na Najeriya na fama da karancin gas wanda ake amfani dashi wajan samar da wutar. Dalilin haka kuwa Najeriya na iya fadawa cikin duhu a yi bukukuwan kirsimeti babu wutar lantarki. Kamfanonin rarraba wutar na Enugu da Fatakwal sun sanar da abokan hukdarsu cewa sun rage yawar wutar da suka baiwa mutane saboda wannan matsala. Wata majiya ta tabbatarwa da Jaridar Punchng da wannan labarin. Hakan na faruwa ne saboda gazawar gwamnati waja biyan bashin da kamfanonin iskar gas din ke bi wanda rahoton yace idan ba'a biya ba ka iya sa kasar ta fada Duhu.