Monday, December 15
Shadow
Akwai yiyuwar in koma jam’iyyar APC, dan majalisa, Abdulmumin Jibrin bayan ganawa da Shugaba Tinubu

Akwai yiyuwar in koma jam’iyyar APC, dan majalisa, Abdulmumin Jibrin bayan ganawa da Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jiya. Bayan ganawar tasu a yayin da yake ganawa da manema labarai an tambayeshi ko haka na nuna cewa zai koma APC ne? Sai ya kayar da baki yace Yanzu ba lokacin wannan maganar bane, ya je ya gaishe da shugaba Tinubu ne sannan aun gana akan lamuran kasa, saidai yace abune mai yiyuwa ya iya komawa APC din. Ya kara da cewa hadin kai da zaman lafiyar Najeriya shine gaba da komai kuma ba abin mamaki bane ganinsa a fadar shugaban kasar.
Ku Daina Zagin Mahaifinsa in kuna yi bana jin dadi>>Inji Dan Gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai

Ku Daina Zagin Mahaifinsa in kuna yi bana jin dadi>>Inji Dan Gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan Gidan Tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai ya roki mutane da su daina zagin mahaifinsa inda yace idan ana yi baya jin dadi. Bashir Ya bayyana hakane a shafinsa na X. https://twitter.com/BashirElRufai/status/1950779372383723541?t=jVCVrXrS5CNdm0pMP-44Ng&s=19 Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na daga cikin 'yan siyasar da suka fi shan suka a Najeriya.
Ma’aikatan jinya sun fara yajin aiki a Najeriya

Ma’aikatan jinya sun fara yajin aiki a Najeriya

Duk Labarai
Ƙungiyar ma'aikatan jinya da unguzomomi ta Najeriya ta fara yajin aikin gargaɗi na mako guda a faɗin ƙasar. Ƙungiyar mai mambobi aƙalla 25,000 ta ca ta fara yajin aikin ne domin nuna rashin jin daɗinta kan rashin albashi mai kyau da ƙarancin ma'aikata da rashin biyansu alawus da kuma rashin kariya a wajen ayyukansu. Shugaban ƙungiyar, Morakinyo Rilwan ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa sun yanke shawarar fara yajin aikin ne bayan ƙarewar wa'adin kwanaki 15 da ƙungiyarsu ta bai wa gwamnati. Yajin aikin dai ya shafi ma'aikatan jinya da ungozomomin da ke aiki a asibitocin gwamnatin tarayya a cewar shugaban ƙungiyar. Mataƙin ma'aikatan jinyar na zuwa ne yayain da ake ci gaba da takun saƙa tsakanin ƙungiyar likitocin ƙasar da gwamnatin tarayya kan walwalar likitocin....
IMF tace tattalin arzikin Najeriya zai samu habaka

IMF tace tattalin arzikin Najeriya zai samu habaka

Duk Labarai
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta hasashensa kan bunƙasar tattalin arzikin Najeriya na shekarar 2025 da 2026. IMF ya bayyana sabon hasashen a watan Yulin da muke ciki wanda a ciki ya yi ƙiyasin samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Najeriya. Asusun ya yi hasashen samun jarin bunƙasar tattalin arzikin Najeriya da kashi 3.4 a 2025, ƙari a kan hasashen kashi 3.0 da ya yi a watan Afrilu. Haka kuma IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai samun ƙarin baunƙasa da kashi 3.2 a 2026, saɓanin hasashen kashi 2.7 da ya yi a watan na Afrilu.
Kalli Bidiyo: ‘Yan Najeriya sun makance ga ci gaba karara amma basa gani>>Inji Ministan Ilimi, Tunji Alausa

Kalli Bidiyo: ‘Yan Najeriya sun makance ga ci gaba karara amma basa gani>>Inji Ministan Ilimi, Tunji Alausa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yanda ga ci gaba Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na kawowa amma 'yan Najeriya da yawa basa gani. Ministan ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Yace Najeriya a yanzu tafi baya ci gaba sannan a yanzu an samu tsaro fiye da da. Ya kara da cewa tattalin arziki na bunkasa wanda har kasashen Duniya sun shaida hakan. https://twitter.com/lindaikeji/status/195046987...
Kalli Bidiyo: Na bayar da kaina Kyauta ba sai ta biya kudi ba, Ummi Nuhu ta daukeni ‘yar Aiki>>Inji Murja Kunya

Kalli Bidiyo: Na bayar da kaina Kyauta ba sai ta biya kudi ba, Ummi Nuhu ta daukeni ‘yar Aiki>>Inji Murja Kunya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraruwar Tiktok, Murja Kunya ta bayyana cewa, ta bayar da kanta kyauta, Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu ta dauketa 'yar aikin gida. Ta bayyana hakane a shafinta na Tiktok inda ta ke nuna goyon bayanta ga Ummi Nuhu. https://www.tiktok.com/@murjakunya0/video/7533012273762209080?_t=ZS-8yTlHZ6H9qD&_r=1 Ummi Nuhu dai ta dauki hankula sosai bayan hirar da Hadiza Gabon ta yi da ita inda ta bayyana halin matsin rayuwar da take ciki.
Kalli Bidiyon yanda aka yiwa su Mansurah Isa Ba daidai ba a wajan taron siyasa hadda cire kaya a bainar Jama’a

Kalli Bidiyon yanda aka yiwa su Mansurah Isa Ba daidai ba a wajan taron siyasa hadda cire kaya a bainar Jama’a

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana yanda aka wulakantasu a wajan taron siyasa na Sanata Barau I Jibrin. Mansurah Isah a wani Bidiyo data wallafa a shafinta na sada zumunta ta bayar da labarin yanda aka gayyacesu wajan taron siyasar amma da suka je daya daga cikin jami'an tsaron yace fuskar daya daga cikinsu bata mai ba dan haka ya hanasu shiga. Tace saboda cin mutunci hadda tubewa wata kaya a bainar Jama'a. Mansurah ta nemi da sanata Barau I Jibrin ya kwato musu hakkinsu. Kalli Bidiyon anan A wani Bidiyo da ta sake wallafawa kuma, Mansurah Isah tace Barau Jibrin ya mata Alkawarin daukar mataki da kwato mata hakkinta ita da sauran abokan tafiyarta. Mansurah ta bayyana godiyarta da Farin ciki kan kulawar Sanatan. Kalli Dayan Bidiyon anan
Ki yi watsi da masu cewa wai laifin da kika yi a bayane yasa kika shiga rayuwar Wahala, Ba haka bane>>Babiana Ta karfafi Ummi Nuhu

Ki yi watsi da masu cewa wai laifin da kika yi a bayane yasa kika shiga rayuwar Wahala, Ba haka bane>>Babiana Ta karfafi Ummi Nuhu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraruwar Tiktok, Babiana ta bayyana shawararta ga tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu da ake cece-kuce akan rayuwarta. Babiana tace ba lallai wai irin rayuwar data aikata a bayane yasa ta shiga halin fata shiga ba. Tace wanda Allah ke so ne ma yake Jarabarsa da ya kara matsawa kusa dashi. Kalli Bidiyonta a kasa: https://www.tiktok.com/@queenofthenorth64/video/7532837479620087045?_t=ZS-8yT1P7iL2jh&_r=1
NNPCL ya musanta sayar da matatar mai ta Fatakwal

NNPCL ya musanta sayar da matatar mai ta Fatakwal

Duk Labarai
Babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya musanta raɗe-raɗin sayar da matatar mai ta birnin Fatakwal. Shugaban kamfanin Bashiru Ojulari ne ya bayyana haka a wani taron tuntuɓa da kamfanin ya shirya a shalkwatarsa da ke Abuja. Ojulari ya ce NNPCL ba shi da aniyar sayar da wata matata mallakinta, sai dai ma ƙoƙarin gyara su domin yin daidai da zamani. An fara raɗe-raɗin sayar da matatar ne bayan wata hira da shugaban kamfanin ya yi a taron OPEC a birnin Vienna na ƙasar Austria a farkon watannan. A lokacin Ojulari ya yi wata hira da jaridar Bloomberg, kan batun sayar da matatar inda ya ce “komai zai iya faruwa”. Tun daga wancan lokacin ne aka yi ta maganganu game da makomar matatar.
Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu kuɗin gina titin jirgi daga Maiduguri zuwa Aba

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu kuɗin gina titin jirgi daga Maiduguri zuwa Aba

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu duka kuɗin gudanar da aikin gina layin dogo daga birnin Maiduguri na jihar Borno zuwa garin Aba na jihar Abiya. Ministan Sufuri Saidu Alkali ne ya bayana hakan a yau yayin wani taron bita da ake gudanarwa a Kaduna, kamar yadda wata sanarwa daga ofishinsa ta bayyana. "Layin dogon mai tsawon kilomita 1,443 zai ratsa jihohin Borno, da Yobe, da Gombe, da Bauchi, da Filato, da Kaduna, da Nasarawa, da Binuwai," in ji sanarwar da kakakin ministan Rabiu Ibrahim ya fitar. Sai dai sanarwar ba ta bayyana inda gwamnatin ta samo kudin ba. Akasarin manyan ayyuka masu tsada kamar wannan akan yi su ne ta hanyar bashi ko kuma lamuni. Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gyara layin dogo na dakon kaya tsakanin Legas zuwa Kano.