Amfanin gishiri a gaban mace
Gishiri na maganin cututtuka wanda bature ke cewa Bacteria.
Dan haka ana amfanin dashi wajan magance kaikan gaba na mata kuma yana aiki sosai, wasu ma nan take suke samun saukin kai kayin.
Saidai kada a shafa gishiri kai tsaye a kan gaban mace, sannan a lura kada a yi amfani da shirin kwata-kwata idan akwai ciwo a gaban mace.
Yanda za'a yi amfani dashi.
Idan kina fama da kaikan gaba, ki zuba gishiri a ruwa, idan so samu ne a samu ruwa me dumi, sai a zuba gishiri, kadan.
A wanke gaban dashi, kada a zuba ruwan cikin farji.
Hanya ta biyi shine, a samu ruwan dumi a zuba madaidaicin gishiri a ciki, sai a zauna a cikin ruwan na tsawon mintuna 15.
Da yardar Allah ana samun sauki nan take, wani kuma yakan dan dauki lokaci.
Baya ga maganin kaikan gaba, amfani da ruwan gishir...