Wannan matar me suna Aisha Isah Yelwa, ta mayar da Naira Miliyan 330 da aka tura bankinta bisa kuskure.
Tana zaunene a Lapai, Jihar Naija.
Da yawa sun jinjina mata da wannan namijin kokari.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito kofar gidan Gwamnatin jihar Kano inda ya karbi masoyansa da suka je dan tayashi murnar shiga sabuwar shekarar 2026.
An ganshi yana dagawa masoyansa hannu a saman mota.
https://twitter.com/Noble_Hassan/status/2006519668509651005?t=NuyV3ytmCDY9G0n0RBMcvg&s=19
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yace shi da iyayensa duk musulunta suka yi.
Yace ya taso a matsayin Kirista kuma ya je makarantar Kiristoci.
Sannan yace a da sunansa Samuel amma aka ce ya je ya shiga Musulunci ya koma Mohammed, sannan yace mahaifiyarsa ma tana cikin matan zumunta amma daga baya duk sun musulunta.
Saidai yace a gidansu raba kafa aka yi, wasu suka zama musulmai, was suka zama Kirista ta yanda duk inda ta fadi sha.
https://twitter.com/OzorNdiOzor/status/2006458422951379229?t=aEfZBD7hjtLPnTHEV2ENmQ&s=19
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sakawa kasafin kudin shekarar 2026 hannu a yau, Laraba.
Kasafin kudin na Naira Tiriliyan 1.4 ne wanda hakan ya samu halartar manyan jami'an Gwamnatin Kano.
Saidai rashin ganin mataimakin Gwamnan jihar a wajan ya jawo cece-kuce.
Dama dai wata majiya tace Gwamna Abba shi kadai zai koma APC ba tare da mataimakin gwamnan ba.
Hakanan a dazu ne muka ga Abba ya gana da shuwagabannin jam'iyyar APC na jihar Kano.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya koma jam'iyyar ADC.
Atiku Abubakar ya tayashi murna inda yake cewa, yana masa maraba da shigowa jam'iyyar ta ADC.
Atiku yayi fatan zasu hada hannu dan ciyar da Najeriya gaba.
Wannan budurwar ta bayar da labarin yanda saurayinta da take so sosai ya rabu da ita ba tare da ta masa wani Laifi ba.
Ta bayar da labarin cikin kuka da bacin rai inda tace ba zata sake soyayya ba.
https://www.tiktok.com/@mardee410/video/7589667265516162324?_t=ZS-92gQt73w0O0&_r=1
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben shakerar 2023 a jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya koma jam'iyyar ADC.
Peter Obi ya koma ADC ne a wani taron jam'iyyar da aka gudanar a jihar Enugu.
Yace ba zasu bayar da damar yin magudin zabe a shekarar 2027 ba.
Peter Obi kuma ya koma jam'iyyar ta APC ne tare da wasu jiga-jigai na kusa dashi da suka hada da masu rike da mukaman siyasa.
u
Tauraron mawakin Arewa, Soja Boy ya bayyana cewa, Bai Taba Rike Miliyan 10 ba tashi amma ya Samu Naira Miliyan 100 a show daya da yayi sanadiyyar waka.
Ya bayana hakane a wata Hira da aka yi dashi.
Ya kuma ce sanadiyyar Waka yana taimakawa 'yan Gidansu sosai.
https://www.tiktok.com/@sojaboygarkuwayanarewa/video/7589945293890702603?_t=ZS-92gN7ETneN7&_r=1
Daya daga cikin yaran Peter Obi me suna Blessing Chimezie Ezeokoli ya bayyana cewa, Atiku ya haura da takara ya barwa Peter Obi yayi takarar a zaben shekarar 2027.
Ya bayyana cewa da yawa 'yan APC na yayata cewar wai Peter Obi ya hakura zai zama mataimakin Atiku.
Yace amma avinda basu sani ba shine, Atiku ya hakura da takara, ya barwa Peter Obi.
Watch how all APC accounts are tweeting "Obi settled for VP ticket" 🤣🤣 without knowing that Alhaji Atiku already stepped down for Okwute
They are praying for Obi not to pick the ticket so they can run riot 😂
But God pass them
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da shuwagabannin jam'iyyar APC na jihar ta Kano.
An ganshi da su Alhassan Ado Doguwa da shugaban jam'iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, da sauransu.