Friday, October 30
Shadow
Allah yawa Me kiran Sallah na masallacin Makkah Rasuwa

Allah yawa Me kiran Sallah na masallacin Makkah Rasuwa

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Saudiyya na cewa, Allah yawa me kiran Sallah na masallacin Makkah, Sheikh Ibrahim Adel Al-Madani rasuwa. An haifeshi a shekarar 1397 bayan Hijira, wadda za'a iya cewa a shekarar 1976 a shekarar bature, a garin Madina, kuma kakansa mahaddacin Qur'ani ne wanda hakan yayi tasiri sosai a rayuwarsa. Ya fara kiran sallah yana da shekaru 15 a masallacin Unguwarsu kuma ya ci gaba har ya kammala jami'a. A shekarar 1439 bayan Hijira ne aka nadashi a matsayin me kiran Sallah na masallacin Makkah. Ya rasune da safiyar yau 11 Rabi Al Thani 1448. Muna fatan Allah ya jikansa da Rahama. https://twitter.com/MakkahUpdate/status/2101890875202637855
Kalli Bidiyon: Dan takarar Gwamnan jihar Ogun  karkashin jam’iyyar APC na shan Allah wadai saboda raba Garin Kwaki

Kalli Bidiyon: Dan takarar Gwamnan jihar Ogun karkashin jam’iyyar APC na shan Allah wadai saboda raba Garin Kwaki

Duk Labarai
Dan takarar gwmanan jihar Ogun a karkashin jam'iyyar APC, Adeola Yayi na shan suka saboda raba karamin Bubun Garin Kwaki. Bidiyon garin Kwakin nasa ya karade kafafen sada zumunta inda ake ta Allah wadai da hakan wasu 'yan jihar na cewa su ba mayunwata bane. https://twitter.com/RealQueenBee__/status/2101753954719981908
Hafsat Kamal tace Saleem Goje ya saketa

Hafsat Kamal tace Saleem Goje ya saketa

Duk Labarai
'Yar Amurka da Saleem Goje ya aura, Hafsat Kamal ta bayyana cewa, Saleem din ya saketa. Ta bayyana hakane a sakon data fitar ta shafinta na sada zumunta. A baya dai an ji dambarwar data faru a gidan Saleem Goje inda suka yi rigima da matar tasa Hafsat. Hafsat ta Godewa masoyanta a kafafen sada zumunta da suka rika nuna mata soyayya duk da basu santa ba.