Allah Sarki: A karin farko tun bayan tsareshi, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi magana
Bidiyon Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na jawabi ya bayyana.
Hakan na zuwane a karin farko tun bayan da ICPC da EFCC suka tsareshi bayan da ya amsa gayyatarsu.
Me magana da yawun Malam Nasiru ne ya wallafa Bidiyon jawabin nasa a shafinsa na X.
An jishi yana jawo hankalin mutane da su rungumi hanyar Lumana ta warware matsala, idan wata rashin jituwa ko wani abin damuwa ya samu, a kaiwa Hukuma, kamar yanda yace.
https://twitter.com/i/status/2028215253205467568
Saidai da Alama an dauki Bidiyon ne tun kamin ya shiga hannun EFCC amma sai yanzu aka sakeshi.








