Thursday, March 26
Shadow
Kalli Bidiyon: Wallahi, Wallahi, Wallahi ban taba yin Zynq ba amma wata matar aure ta yaudareni na aikata alfasha da ita

Kalli Bidiyon: Wallahi, Wallahi, Wallahi ban taba yin Zynq ba amma wata matar aure ta yaudareni na aikata alfasha da ita

Duk Labarai
Wani matashi ya aikawa Sheikh Abdulfatahi Gadon kaya wasika inda yace wata matar aure ta yaudareshi sun aikata zina. Yace shi bai taba aikatawa ba, wannan ne karon farko. Yace ji yake kamar ya fita daga Musulunci. Ya nemi malam ya bashi shawarar yanda zai tuba. https://www.tiktok.com/@nijar.maradi.gida3/video/7548918678033566983?_t=ZS-8zrYVtw6V9M&_r=1
Kalli Bidiyon Sultana ta BBNaija dake ikirarin ita Musulmace daga Arewa, yanda ta, chire kayan jiqinta, ta yi Tumbur Haihuwar uwarta a tsakiyar ‘yan BBNaija din, ta sake jawo cece-kuce sosai, da yawa na cewa suna kokwanton Musuluncin ta

Tauraruwar BBNaija, Sultana wadda 'yar Asalin Jihar Adamawa ce ta sake jawo cece-kuce. Sultana ta jawo cece-kuce ne bayan Bidiyon ta da aka ga tana rawa tsirara a gaban abokanta da suke yin BBNaija din tare. Wasu dai musamman daga kudu sai jinjina mata suke suna cewa ta iya rawa amma wasu na mamakin ashe dama 'yan matan Arewa sun iya sheke aya haka? https://twitter.com/wendysmith2468/status/1968821971950489994?t=zlPysUOLNXZLrp2IfR6fLA&s=19 https://twitter.com/_sultanafarida/status/1968822203182379416?t=uvXqzJ3TUEQQcl95uEkNCg&s=19 Sultana dai ta taba bayar da labarin cewa mahaifinta Musulmine amma mahaifiyarta kirista ce daga kudancin Najeriya. Tace ta taso tana Sallah kuma tana zuwa coci amma dai daga baya ta zabi ta zama musulma.
Kalli Bidiyon: Shugaba Tinubu ya je gaishe da matar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau A’isha a Kaduna

Kalli Bidiyon: Shugaba Tinubu ya je gaishe da matar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau A’isha a Kaduna

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya je gidan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya gaishe da matarsa, A'isha. Shugaban ya gaishe da A'isha ne inda yace mata zai ci gaba da tabbatar da irin tsare-tsaren shugaban kasa, Muhammadu Buhari. https://twitter.com/Abdool85/status/1969016925066858995?t=6E_jyQ2Plu96hHwEVx-jLA&s=19
Bayan na Farko, Matatar Man fetur din Dangote ta sake aika Jiragen Ruwa uku dauke da Gas zuwa kasar Amurka

Bayan na Farko, Matatar Man fetur din Dangote ta sake aika Jiragen Ruwa uku dauke da Gas zuwa kasar Amurka

Duk Labarai
Rahotanni sun ce matatar man fetur din Dangote ta sake aikewa da Manyan Jiragen ruwa dauke da Gas zuwa kasar Amurka. Hakan na zuwane bayan na farko da matatar ta kai kasar. Rahotannin sun ce kasar Amurka ta bayyana cewa, Gas din da matatar man fetur din Dangote ke fitarwa na da ingancin da kasar ke bukata. A baya dai mutane da yawa sun yi mamakin jin yanda matatar man fetur din Dangoten ta yi nasarar fara fitar da man fetur zuwa kasar Amurka.
Daga Shekarar 2026, Duk Naira dubu dari da Dan Najeriya ya samu, Gwamnatin Tarayya zata dauki Naira dubu goma sha biyar daga ciki a matsayin kudin haraji

Daga Shekarar 2026, Duk Naira dubu dari da Dan Najeriya ya samu, Gwamnatin Tarayya zata dauki Naira dubu goma sha biyar daga ciki a matsayin kudin haraji

Duk Labarai
Ko kun san cewa sabuwar dokar Haraji ta tanadi cewa daga shekarar 2026, Duk wanda ya samu 100 a matsayin kudin shiga, Gwamnati zata dauki Naira 15,000 a matsayin kudin Haraji? Dokar dai ta bayyana yawan kudin da za'a rika cirewa daga yawan kudin da mutum ya samu: First ₦800k: 0% Next ₦2.2M: 15% Next ₦9M: 18% Next ₦13M: 21% Next ₦25M: 23% Above ₦50M: 25%
Kalli Bidiyo: Cikin sahabban Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) babu wanda ya rika cewa shi Ahalussunnah ne ya rika kafirta sauran sahabbai>>Inji Digital Imam

Kalli Bidiyo: Cikin sahabban Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) babu wanda ya rika cewa shi Ahalussunnah ne ya rika kafirta sauran sahabbai>>Inji Digital Imam

Duk Labarai
Malamin addinin Islama, Digital Imam ya bayyana cewa, a cikin Sahabban Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam babu wadanda suka rika ikirarin Ahlussunah suka rika kafurta sauran Sahabbai. Malam yace ikirarin Ahlussunah daga baya ya fito. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7551058248858619143?_t=ZS-8zqp1hX5n05&_r=1
Kalli Bidiyo: Ta aikawa Malam ya baiwa Mijinta Hakuri bayan da ya hanata kudin anko da kudin gudummawar zuwa bikin kawarta amma ta sayar da buhun shinkafa ta tafi

Kalli Bidiyo: Ta aikawa Malam ya baiwa Mijinta Hakuri bayan da ya hanata kudin anko da kudin gudummawar zuwa bikin kawarta amma ta sayar da buhun shinkafa ta tafi

Duk Labarai
Wata mata da mijinta ya ki bata kudin gudummawa dana Anko zuwa wajan bikin kawarta ta sayar da buhun shinkafa ta yi hidimar bikin. Saidak bayan data dawo daga wajan bikin, ya dauke mata duka kayanta inda yace sai ta shekara 2 tana saka wadannan kayan kamin ya fito mata da kayanta. Tace ta gayawa mahaifinta kuma yace mijin yayi daidai. Shine ta aikawa malam ya baiwa mijin hakuri. https://www.tiktok.com/@mariamelhadjigomb/video/7550917552537423126?_t=ZS-8zqnVya4ktN&_r=1