
Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani
Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Uba Sani.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya daidaita harkar tsaro a yankin Arewa maso Yamma tare da farfado da harkokin noma da 'yan ta'adda suka durkusar da su a baya.
Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar, Sani ya ce yankin da a da ke zama cibiyar ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga, yanzu yana samun sauyi mai ma’ana.
“Tun kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, yankin Arewa maso Yamma ne cibiyar ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifukan tashin hankali,” in ji shi.
“Ba za ka iya yin tafiya daga wuri zuwa wani wuri ba. Manoma ba za su iya zuwa gonakinsu ba. Rayuwa ta kasance...