Saturday, March 7
Shadow
Kalli Bidiyon: Tun shekarar farko ta Mulki Abba suka fara samun matsala da Kwankwaso>>Inji Sanat Rufai Hanga

Kalli Bidiyon: Tun shekarar farko ta Mulki Abba suka fara samun matsala da Kwankwaso>>Inji Sanat Rufai Hanga

Duk Labarai
Sanata Rufai Hanga ya bayyana cewa rashin jituwar dake tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta fara ne tun shekarar farko da fara Mulkin Abba. Yace a wancan lokacin Sanata Kwankwaso ya so ganin Abba amma Abban yaki zuwa shi kuma idan ya ce zai je wajan Abban sai Abban yaki yadda ya ganshi. Yace Sanata Kwankwaso ya gaya masa cewa, Lamarin ya dameshi saboda yanda yake ganin dansa Mustapha haka yake kallon Abba inda yace yana tunanin wani abu akawa Abba dan wannan ba Abban da ya sani bane. Sanata Rufai yace Kwankwaso ya nemi a saka Gwamna Abba a addu'a inda daga baya suka samu ganawa. https://twitter.com/i/status/2018096318753775892
Allah Sarki Kalli Bidiyon: Asalin dan mutuminnan da akewa laqabi da Sarkin Qarya ya fito yace dan Allah a daina ce masa Yarima

Allah Sarki Kalli Bidiyon: Asalin dan mutuminnan da akewa laqabi da Sarkin Qarya ya fito yace dan Allah a daina ce masa Yarima

Duk Labarai
Asalin dan mutuminnan da akewa Laqabi da Sarkin Qarya, ya fito yace wani da ya bayyana tun farko yace shine dan mahaifin nasu har ana tara masa kudi ba gaskiya bane. Yace su basu ma sanshi ba suma a kafafen yada labarai suke ganinsa. Ya kara da cewa, yana rokon mutane su daina ce masa Yarima. https://www.tiktok.com/@official.abdul297/video/7601483441531522325?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7601483441531522325&source=h5_m&timestamp=1769935696&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_i...
Kalli Bidiyon hira da matarnan da ake zargin ta kori mahaifiyarta daga gidanta saboda mahaifiyar ta kasa biyan kudin haya

Kalli Bidiyon hira da matarnan da ake zargin ta kori mahaifiyarta daga gidanta saboda mahaifiyar ta kasa biyan kudin haya

Duk Labarai
Matar nan 'yar garin Daura da ake zargin ta kori mahaifiyarta daga gidanta sabida mahaifiyar ta kasa biyan kudin haya ta fito ta kare kanta. Tace itama kamar yanda aka gani, haka taga lamarin a kafafen sada zumunta. Tace mijin mahaifiyarta ne ke son sai ta sayar masa da gidan wanda gado ne da mahaifinta ya bar mata amma taki amincewa, tace tana tunanin yana da hannu game da abinda ke faruwa. https://twitter.com/i/status/2017523186250690887 Wasu da a baya suka yi sharhi me kaushi akan matar sun fito sun bata hakuri. https://www.tiktok.com/@prettyme_barrister/video/7601657152842763528?_r=1&_t=ZS-93YNAAnTn5V
Farashin Man Fetur ka iya kai Naira Dubu 1 kowacw lita

Farashin Man Fetur ka iya kai Naira Dubu 1 kowacw lita

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Farashin man fetur ka iya kai Naira 1000 kowace lita. Hakan na zuwane bayan da farashin danyen man fetur ya tashi a kasuwar Duniya. 'yan kasuwar man sun shaidawa majiyar Hutudole cewa, farashin ka iya tashi nan da kwanaki masu zuwa. A ranar Alhamis ne dai farashin na danyen man fetur ya tashi zuwa dala $70 akan kowace ganga a kasuwar Duniya. Dangote na sayar da man fetur dinsa akan farashin 739 zuwa 839 akan kowace lita a yanzu.