Monday, December 15
Shadow
Idan muka dage, Cikin shekaru 5 zamu iya maida Afrika Aljannar Duniya>>Inji Dangote

Idan muka dage, Cikin shekaru 5 zamu iya maida Afrika Aljannar Duniya>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, idan aka dage a Afrika, cikin shekaru 5 za'a iya mayar da nahiyar Aljannar Duniya. Ya bayyana hakane a wajan wata hira da aka yi dashi. Dangote ya bayyana cewa, babbar matsalarmu a Afrika shine satar kudi da ake ana kaiwa kasashen ketare. Yace babu inda ba'a rashawa da cin hanci, yace amma matsalar ta Africa shine, maimakon idan an sata a zuba jari da kudin a Afrika, sai a mayar dasu zuwa kasashen waje. Dangote yace ba wai yana karfafa satar kudin Gwamnati bane amma abinda yake cewa, shine a daina kai kudaden kasashen waje.
Sharudan da aka gindaya min kamin a mayar da ni Gwamna basu da dadi amma na amince>>Inji Fubara

Sharudan da aka gindaya min kamin a mayar da ni Gwamna basu da dadi amma na amince>>Inji Fubara

Duk Labarai
Dakataccen Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ya bayyana cewa, Sharudan da aka gindaya masa ya cika kamin a mayar dashi kan kujerar gwamna basu da dadi. Yace amma ya amince dasu. Fubara ya bayyana hakane a yayin ganawa da kungiyar masoyansa inda yace musu su amince da sharadin suma domin indai ba rayuwarsa aka ce ya bayar ba zai amince da duk wani sharadi dan dai a zauna lafiya. Fubara ya bayyana cewa, suna godiya da irin rawar da Wike ya taka wajan ci gaban jihar da kawo karshen rikicin jihar. Wasu daga cikin sharudan da aka gindayawa Fubara sune dole ya amince ba zai sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027 ba sannan zai biya 'yan majalisar jihar hakkokinsu da ya dakatar, sannan Wike ne zai tsayar da 'yan takarar kananan hukumomi a jihar.
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Paul Pogba ke kuka bayan Komawa kungiyar AS Monaco

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Paul Pogba ke kuka bayan Komawa kungiyar AS Monaco

Duk Labarai
Paul Pogba ya saka hannun yarjejeniya da kungiyar AS Monaco. Zai bugawa kungiyar wasa na tsawon shekaru 2 zuwa shekarar 2027. Hakan na zuwane bayan da ya kammala dakatarwar shekaru 2 da aka masa bayan samunshi da ta'ammuli da miyagun kwayoyi. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1939052855815741547?t=K6H25L7HO2F_6YNje1ZAIA&s=19 Da farko an yanke masa dakatarwar shekaru 4 amma daga baya aka mayar dashi shekaru 2 bayan ya daukaka kara. Saidai Pogba a yayin da yake sakawa AS Monaco hannu ya fashe da kuka inda aka rika bashi baki.
Bidiyo: Mansurah Isah ta bayyana yanda ta tsira daga hannun ‘yan damfara

Bidiyo: Mansurah Isah ta bayyana yanda ta tsira daga hannun ‘yan damfara

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana yanda ta tsira daga hannun 'yan Damfara. Mansurah tace wani yaro ya je gidanta inda ya rubuta sunanta a jikinsa da sunan cewa, wai yana sonta, yana son ta taimaka masa. Saidai tace ta kai maganar wajan 'yansanda inda aka mayar da yaron Bauchi saboda yace daga kauyen Bauchi ya fito, tace ta yi yunkurin tallafawa yaron inda tace a tambayo kudin makarantar Bokonsa da Arabi. Tace amma sai akance wai makarantar Arabi ana biyan Naira dubu 70 duk wata ita kuma Boko ana biyan Dubu 150 duk wata. Mansurah tace data ga abin nasu damfara ne sai kawai ta ce a bar maganar ta daina kulasu. Tace kwatsam sai gashi kuma ta ga yaron wai ya rubuta sunan Lilin Baba a jikinsa. Mansurah tace Allah ya ceceta. Kalli Bidiyon ta: https://...
David Mark zai shagabanci jam’iyyar ADC ta hadakar ‘yan adawa

David Mark zai shagabanci jam’iyyar ADC ta hadakar ‘yan adawa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon kakakin Majalisar Dattijai, Sanata David Mark ne ake sa ran zai jagoranci Jam'iyyar hadaka ta 'yan Adawa watau ADC. Ana tsammanin nan gaba kadanne hadakar 'yan adawar zasu bayyana ADC a matsayin jam'iyyar da zasu yi amfani da ita wajan kalubalantar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 kuma David Mark ne zai zama shugaban jam'iyyar na rikon kwarya. Rahoton yace hadakar 'yan adawar ta hada da Atiku Abubakar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Rotimi Amaechi, da Peter Obi. Jaridar Punchng tace David Mark ya amince ya zama shugaba jam'iyyar ta ADC. Rahoton yace hadakar 'yan adawar na neman wanda zai zama sakataren jam'iyyar tasu bayan da Rauf Aregbesola, da Senator Ben Obi suka ki amincewa da tayin zama sakataren jam'iyyar. Ana ts...
Har Yanzu Akume Ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cewar Fadar Shugaban Ƙasa

Har Yanzu Akume Ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cewar Fadar Shugaban Ƙasa

Duk Labarai
Har Yanzu Akume Ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, Cewar Fadar Shugaban Ƙasa. Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu wani canji da aka yi game da matsayin Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF). A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin bayani da dabarun yada labarai, ya fitar a yau Asabar, an bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda a halin yanzu yake Saint Lucia bai yi wani sabon nadin mukami ba. Sanarwar ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da labarai cewa an sauke Sanata Akume daga mukaminsa, tana mai cewa wannan labari ƙarya ne da aka kirkira don cimma wata manufa. Fadar Shugaban Ƙasar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da irin wadannan jita-jita da basu da t...
Gwamnatin Tarayya zata samar da sabbin ofisoshin ‘yansanda masu kayan aiki sosai

Gwamnatin Tarayya zata samar da sabbin ofisoshin ‘yansanda masu kayan aiki sosai

Duk Labarai
Newly deployed Nigerian Formed Police Unit (FPU) personnel under the African Union Mission in Somalia (AMISOM) arrive at Aden Abdulleh International Airport, Mogadishu, Somalia on January 6, 2016. AMISOM Photo / Ilyas Ahmed Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin samar da ofisoshin 'yansanda masu isassun kayan aiki a fadin Najeriya. Gwamnatin ta sanar da cewa za'a yi hadaka ne tsakanin ma'aikatun Gwamnati da hukumar kula da 'yansanda. Rahoton yace za'a samar da ofisoshin da za'a zubawa kayan aiki na zamani.
Kungiyar dattawan Arewa sun nemi shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaron Arewa

Kungiyar dattawan Arewa sun nemi shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaron Arewa

Duk Labarai
Kungiyar dattawan Arewa ta NEF sun nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ayyana dokar ta baci akan matsalar tsaron Arewa. Kungiyar dattawan sun kuma yi Allah wadai da kisan sojoji 20 a kananan hukumomin Bangi, Mariga dake Jihar Naija. A sanarwar da kakakin kungiyar, Prof Abubakar Jiddere ya fitar, yace kisan sojojin alamace ta rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Yace irin wannan hari alamace ta kaddamar da yaki akan Najeriya da 'yan ta'addar suka yi.