Tuesday, December 23
Shadow
Mun godewa Allah da kafuwar Jam’iyyar ADC, saboda ta fito mana da bakaken munafukan cikin jam’iyyar mu ta APC wanda suka Munafurci Tinubu a zaben 2023 Karara mun gansu>>Inji Ministan Sufurin Jiragen sama, Festus Keyamo

Mun godewa Allah da kafuwar Jam’iyyar ADC, saboda ta fito mana da bakaken munafukan cikin jam’iyyar mu ta APC wanda suka Munafurci Tinubu a zaben 2023 Karara mun gansu>>Inji Ministan Sufurin Jiragen sama, Festus Keyamo

Duk Labarai
Ministan Sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya yi martani ga komawar hadakar 'yan jam'iyyar Adawa musamman daga APC zuwa ADC. Keyamo yace 'yan APC din da suka koma ADC a jiya sune munafukan cikin APC da suka munafurci shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023 basu so ya ci zabe ba. Manya-manyan wadanda suka koma ADC wadanda 'yan APC ne sun hada da Rotimi Amaechi da Abubakar Malami da kuma Malam Nasiru Ahmad El-Rufai wanda shi dama ya dade da ficewa daga jam'iyyar ta APC zuwa SDP Keyamo yace komawarsu ADC bai ragi APC da komai ba sai ma kara karfi da jam'iyyar ta yi. Festus Keyamo ya kara da cewa sauran wadanda suka koma ADC wadanda suka nemi takarkaru ne amma basu samu nasarar ci ba.
‘Abin da ya sa muka zaɓi ADC a matsayin jam’iyyar haɗaka’ Su Atiku suka yi Bayani Dalla-dalla

‘Abin da ya sa muka zaɓi ADC a matsayin jam’iyyar haɗaka’ Su Atiku suka yi Bayani Dalla-dalla

Duk Labarai
A ranar Laraba ne manyan ƴan adawar siyasa na Najeriya suka tabbatar da amincewa da jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin wadda za su yi aiki da ita domin tunkarar zaɓen 2027. Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, wanda jigo ne a haɗakar ya ce: "mun kwashe wata tara zuwa shekara ɗaya muna tattaunawa domin ganin yadda za mu haɗa kanmu mu shiga jam'iyya ɗaya da ba za a iya soke rajistarta ba, mu gyara jam'iyyar da shugabancinta da aƙidarta da fito da tsarin da zai ceci ƙasarmu daga wannan hali da aka shiga." Hakan na zuwa ne bayan yunƙuri daban-daban da ƴan adawar suka yi na ganin sun samar da ƙwaƙƙwarar adawa da za su iya tunkarar shugaban ƙasar mai ci Bola Ahmed Tinubu, wanda suke zargi da gazawa a mulkinsa. Ana iya cewa wannan mataki ya kawo ƙarshen raɗe-...
Masu fita daga PDP zama su dawo ne saboda jam’iyyar mu ce kadai zata iya kada Tinubu>>Inji Shugaban PDP

Masu fita daga PDP zama su dawo ne saboda jam’iyyar mu ce kadai zata iya kada Tinubu>>Inji Shugaban PDP

Duk Labarai
Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta gargaɗi ƴanƴanta da ke shirin shiga sabuwar haɗakar ADC. Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin amintattun jam'iyyar, shugaban jam'iyyar na ƙasa Amb. Iliya Damagum ya ce jam'iyyar za ta ɗauki tsattsauran mataki kan mambobinta da ke ƙoƙarin shiga haɗakar. Damagum ya ce ƙoƙarin da haɗakar ke shirin yi ba zai yi tasiri ba, yana mai cewa da dama daga cikin mambobin haɗakar za su koma jam'iyyunsu. “Yana da kyau su sani cewa babu inda ya kamata a haɗu domin tunkarar gwamnatin APC da ya wuce jam'iyyar PDP, amma in suna ganin ba haka ba, to su je su gwada su gani, amma dai na san dole za su dawo'', in ji shi. Shugaban riƙon ya kuma gargaɗi ƴan PDP da ya ce suna ƙoƙarin ''sayar da jam'iyyar''. Kawo yanzu dai akwai jiga-...
Dalilin da ya sa ake yi wa Buhari kallon shugaba mai jan ƙafa – Garba Shehu

Dalilin da ya sa ake yi wa Buhari kallon shugaba mai jan ƙafa – Garba Shehu

Duk Labarai
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban Najeriya, Garba Shehu ya kare salon mulkin shugaba Muhammad Buhari. Malam Garba Shehu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise TV, inda ya amince da cewa duk da wani lokacin ana bayyana shugabancin Buhari da mai jan ƙafa amma ya ce hakan na faruwa ne sakamakon ƙoƙarinsa na bin ƙa'ida wajen aiwatar da al'amura a ƙoƙarinsa na sauyin da yake yi daga mulkin soji zuwa na farar hula. Sai dai kuma tsohon mataimakin na Buhari, ya ce ƴan Najeriya ba su da haƙuri kasancewar suna son sha yanzu magani yanzu ko da kuwa za a saɓa ƙa'idojin dimokraɗiyya. "Yana da jan ƙafa? E, shi ma da kansa ya kan yi barkwanci dangane da hakan. Kuma ya yawan faɗin hakan lokacin da ya hau mulki a matsayinsa na soja, yana yin abun da ya g...
NAHCON ta kammala jigilar alhazan Najeriya daga Saudiyya

NAHCON ta kammala jigilar alhazan Najeriya daga Saudiyya

Duk Labarai
Hukumar Alhazan Najeriya ta kamala jigilar alhazan ƙasar da suka sauke farali a aikin hajjin bana. Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kammala aikin kwaso alhazan daga ƙasa mai tsarki a yau Laraba 2 ga watan Yulin 2025. Kimanin alhazan Najeriya 41,291 ne suka sauke farali a wanan shekara, kamar yadda hukumar ta bayyana. Jirgin ƙarshe da ya ɗauko alhazan jihar Kaduna ya taso da safiyar yau.
Ya Bude Shagon Siyar Da Yajin Daddawa Bayan Ya Kammala Digiri A Jami’ar Bayero

Ya Bude Shagon Siyar Da Yajin Daddawa Bayan Ya Kammala Digiri A Jami’ar Bayero

Duk Labarai
Ya Bude Shagon Siyar Da Yajin Daddawa Bayan Ya Kammala Digiri A Jami'ar Bayero. Bayan kammala karatunsa na digiri daga jami'ar Bayero ta Kano bai tsaya jiran aiki ba ya buɗe shagon siyar da yajin daddawa a zamanance. Yanzu haka ya dauki ma'aikata a kasansa. Inda shagon nasa yake akan titin gidan zoo dake Kano. Ya kamata matasa su yi koyi da shi. Daga Dr.Yak'S
Sanata Kwankwaso Ya Kaiwa Sani Danja Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa

Sanata Kwankwaso Ya Kaiwa Sani Danja Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Sanata Kwankwaso Ya Kaiwa Sani Danja Ziyarar Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa.