Monday, December 15
Shadow
‘Yan sanda basu kama mutane saboda zagin ‘yan siyasa, har ni ku zaga babu wanda zai kamaku>>Inji Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun

‘Yan sanda basu kama mutane saboda zagin ‘yan siyasa, har ni ku zaga babu wanda zai kamaku>>Inji Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa, 'yansanda basa kama mutum dan kawai ya zagi ko sukar dan siyasa. Yace koshi ana zaginshi a kafafen sada zumunta amma hakan baya sawa a kama mutane. Ya bayyana hakane ranar Talata a wajan wani taron da aka gudanar a Abuja inda yace amma inda za'a iya kama mutum shine idan ya wallafa labaran karya. Yace ko da ba akan dan siyasa ba idan mutum ya wallafa labaran karya za'a iya hukuntashi.
Gaf nake da barin jam’iyyar APC saboda alamu na nuna ba lallai Tinubu ya kai labari ba duk da gwamnonin dake tururuwar komawa jam’iyyar APC>>Sanata Ali Ndume

Gaf nake da barin jam’iyyar APC saboda alamu na nuna ba lallai Tinubu ya kai labari ba duk da gwamnonin dake tururuwar komawa jam’iyyar APC>>Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya bayyana cewa, gaf yake da barin jam'iyyar APC saboda ba lallai jam'iyyar ta kai labari ba a zaben 2027. Ndume a wata hira da aka yi dashi a Arise TV yace a baya yayi imanin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai iya gayara matsalolin Najeriya amma daga baya abubuwa suka canja. Ya bayyana cewa, maganar gaskiya shi tuni ma ya fara halartat tarukan hadakar 'yan Adawa dan kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027. Yace amma har yanzu bai yankewa shugaban kasar tsammanin yin gyara ba amma idan aka ci gaba a haka, shi zai fice daga jam'iyyar.
Mutane Miliyan 1.3 ne suke mutuwa duk shekara saboda shakar hayakin taba duk da su ba mashaya tabar bane

Mutane Miliyan 1.3 ne suke mutuwa duk shekara saboda shakar hayakin taba duk da su ba mashaya tabar bane

Duk Labarai
Rahotan hukumar lafiya ta Duniya, WHO yace mutane Miliyan 1.3 ne ke mutuwa duk shekara daga shakar hayakin taba sigari duk da su ba mashaya tabar bane. WHO ta fitar da rahoton ne bayan taronta a Birnin Dublin. Rahoton yace akwai bukatar a samar da tsari da zai dakatar da irin wannan asara da ake yi. Hukumar ta fito da wani tsari me suna MPOWER wanda tace idan aka bishi za'a samu saukin mutuwar mutane dalilin shan taba Sigari. Tsarin na dauke da kula da masu shan taba sigari da kuma tsaftace iska da kuma taimakawa masu shan tabar su daina sha.
Duba Yankunan Najeriya biyu da basu taba samar da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba

Duba Yankunan Najeriya biyu da basu taba samar da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba

Duk Labarai
Yankunan Arewa ta tsakiya da yankin Kudu maso gabas ne basu taba samar da shugaban kasa ba a Najeriya. Amma yankunan: North West — Sun samar da shugaban kasa da mataimakin shugaban kasaSouth West — Sun samar da shugaban kasa da mataimakin shugaban kasaSouth South — Sun samar da shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa North East — Sun samar da mataimakin shugaban kasa.
‘Yan Siyasa na ta canja Jam’iyya amma mabiyansu basa canjawa>>Inji Sanata Ali Ndume

‘Yan Siyasa na ta canja Jam’iyya amma mabiyansu basa canjawa>>Inji Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa 'yan siyasa na ta canja sheka amma mabiyansu basa canjawa. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Sanata Ali Ndume yace hadakar 'yan adawa da ake samu abune me kyau wanda ya kamata ace dama can akwaishi. Yace shekararsa 65 kuma ya shafe sama da shekaru 20 a cikin siyasa dan haka babu abinda ke gabansa yansu sai fadar gaskiya komai dacinsa. Sanata Ali Ndume ya yi wasu kalamai dake nuna alamun cewa, yana shirin canja jam'iyya.
Kalli Bidiyon yanda aka kama masu kwacen waya da suka shiga gidan wata Sabuwar Amarya a Kano, abinda sukawa amaryar ya bada mamaki

Kalli Bidiyon yanda aka kama masu kwacen waya da suka shiga gidan wata Sabuwar Amarya a Kano, abinda sukawa amaryar ya bada mamaki

Duk Labarai
Wasu masu kwacen waya sun shiga gidan wata sabuwar Amarya a unguwar Gaida dake Kano. Sun caccaka mata wuka sannan suka kwace mata waya, ta rika ihun barawo har mutane suka taru. Barayin 3 ne inda jama'a da suka taru suka yi nasarar kama guda 2 daga ciki. https://twitter.com/Alameen___Abba/status/1937492720034988336?t=yzO5jHDArxWZ5dgTJQyvNA&s=19 Amaryar dai an garzaya da ita Asibiti inda tana can tana samun sauki.
Wata Kungiya ta yi kiran shugaba Tinubu ya dauki Yakubu Dogara a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027

Wata Kungiya ta yi kiran shugaba Tinubu ya dauki Yakubu Dogara a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027

Duk Labarai
Wata Kungiya daga yankin Arewa maso gabas ta yi kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya ajiye Kashim Shettima ya dauki Yakubu Dogara a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027. Kungiyar me suna the Coalition of APC Support Groups in the North-East ta bayyana hakane a zaman data gudanar a ranar Litinin a jihar Gombe. Kungiyar tace Yakubu Dogara ne wanda yafi dacewa ya zama mataimakin shugaban kasa a shekarar 2027. Tace zata nada wakilai da zasu jagoranci mutane zuwa ganin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a Abuja dan isar masa da sakonsu.
Sai Tinubu ya yi sa’a ma zai zo na uku a zaɓen 2027— In ji El-Rufai

Sai Tinubu ya yi sa’a ma zai zo na uku a zaɓen 2027— In ji El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ba ya damu da yawan sauya sheƙa da ake yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki. A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a shirin Arise TV a daren Litinin, El-Rufai ya ce shugaban ƙasa mai ci yana ɗaukar matsayin cewa tuni an gama da dawowar sa karo na biyu, ganin yadda wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa ke sauya sheƙa zuwa APC. Sai dai ya bayyana cewa: "Tinubu ba zai ci zaɓe ba. A gaskiya, zai yi sa’a idan ma ya zo na uku." Tsohon gwamnan ya zargi gwamnatin Tinubu da halin ko in kula dangane da matsanancin halin tsaro da ƙasar ke ciki, yana mai bayyana cewa an cire naira biliyan 100 daga Asusun Tarayya cikin watanni 15 da suka gabata ba tare da amincewar jihohi ko majalisar dokoki ba. Ya ce: "Tun cikin watanni 15 da suka wuce, ana...
Gaskiya ka iya Karya, ta ya zaka ce mana kun kammala jami’a da dan shekaru 13?>>Atiku Abubakar ya caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Gaskiya ka iya Karya, ta ya zaka ce mana kun kammala jami’a da dan shekaru 13?>>Atiku Abubakar ya caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, akwai daure kai da rainin hankali ace wai Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala jami'a tare da dan shekaru 13. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a yayin da yake kaddamar da shirinsa na Renew Hope Agenda a Abuja ya bayyana wani me suna Alex Zingman  da cewa, abokin karatunsa ne. Saidai Atiku yace shi wannan me suna Alex Zingman da Tinubu yace sun kammala jami'ar Chicago State University (CSU) tare a shekarar 1979, an haifeshine a shekarar 1966, watau yana da shekaru 13 kenan suka kammala karatu tare da shugaba Tinubu. Dan haka Atiku a sanarwar da ya fitar ta hannun me magana da yawunsa, Paul Ibe yace wata kila kundin tarihin Duniya ya manta ne bai saka wannan abokin karatu n...