Tuesday, December 16
Shadow
Kalli Bidiyo: Ana zargin shuwagabannin kasashen Faransa, Jamus, da Ingila da shan Hòdàr Iblìs

Kalli Bidiyo: Ana zargin shuwagabannin kasashen Faransa, Jamus, da Ingila da shan Hòdàr Iblìs

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa an ga Shuwagabannin kasashen Faransa, Emmanuel Macron dana Ingila, Sir Keir Starmer da ta jamus, Friedrich Merz suna ta'ammuli da Hòdar Iblìs. https://twitter.com/GlobalDiss/status/1921520024776241239?t=Nlsn9-dGxHwIZqHCW85arg&s=19 Rahoton yace shuwagabannin sun kammala ganawa ne da Shugaban Ukraine, Zelenskyy inda suka shiga jirgin kasa dan komawa kasashen su. https://twitter.com/KevorkAlmassian/status/1921546995900002603?t=YT_ERb4lRgUCAV_W7Y9NJw&s=19 Saidai akan hanyarsu an yi zargin sun shaka hodar Iblis inda har suka manta basu dauke abubuwan da suka yi amfani da su ba akan teburinsu, har wata 'yar Jarida ta shiga wajan da suke ta daukesu hoto. Yar jaridar ta watsa Bidiyon data dauka a kafafen sada zumunta wanda kuma suka dauki ...
Mun tarwatsa sansanin Màhàrà a Borno>>Inji Sojojin Najeriya

Mun tarwatsa sansanin Màhàrà a Borno>>Inji Sojojin Najeriya

Duk Labarai
Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation HADIN KAI (OPHK) sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama a wani samame da suka ƙaddamar a dajin Sambisa da ke jihar Borno. Wannan aikin, a cewar sanarwar da shalkwatar sojojin ta fitar ta ce ya gudana ne a ranar 11 ga watan Mayu, 2025, a yankin Ladin Buttu, "wurin da aka san shi da zama mafakar ’yan ta’adda" kuma rundunar sojin ta bayyana nasarar a matsayin muhimmin ci gaba a yaƙin da ake yi da ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso gabashin ƙasar. Hakan na zuwa ne bayan sabbin hare-haren da mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar kan wurare daban-daban a jihar Borno, inda matsalar rikicin Boko Haram ta fi ƙamari. A sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, mataimakin daraktan hulda da jama’a na Sojojin, Kyaftin Reuben Kovangiya...
Za mu koma aikin haƙo ɗanyen mai a arewacin Najeriya – NNPCL

Za mu koma aikin haƙo ɗanyen mai a arewacin Najeriya – NNPCL

Duk Labarai
Shekara biyu bayan ƙaddamar da aikin haƙo ɗanyen man fetur a iyakar jihohin Bauchi da Gombe - wanda tun daga wancan lokaci ba a ci gaba da aikin ba - a yanzu sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya Bayo Ojulari ya fada wa BBC cewa za a koma kan aikin. Aikin da aka ƙaddamar a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata, ya sanya al’ummar arewacin ƙasar sun fara kyakkyawar fatan cewa yankin zai bi sahun wasu yankunan ƙasar da ke samar da man fetur wanda tattalin arzikin ƙasar ya dogara a kai. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, wadda ke da alaƙa tashin farashin man fetur a sanadiyar cire tallafin da gwamnati ke bayarwa a bangaren. Tun a jawabin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na farko bayan shan rantsuwar kama mulki ne ...
Rashin Tabbas bayan kammala karatu da tsadar Rayuwa tasa yanzu iyaye sun fara tura ‘ya’yansu koyan aikin hannu

Rashin Tabbas bayan kammala karatu da tsadar Rayuwa tasa yanzu iyaye sun fara tura ‘ya’yansu koyan aikin hannu

Duk Labarai
Rahotanni sun ce iyaye a yanzu sun fara hakura da maganar sai 'ya'yansu sun samu aikin Gwamnati da daukar albashi me tsoka. Inda aka fara tura yara koyon sana'a yayin da suke zuwa makaranta a lokaci guda. Rahoton wanda jaridar Vanguard ta hada, yace yanzu yara tun daga shekara 10 ana fara turasu zuwa koyon aiki dan su dogara da kansu da kaucewa matsalar su kammala karatu ya zamana sun zauna babu aikin yi. Wasu kuma na tafiya da 'ya'yan nasu ne wajan aikin da suke dan su rika koya musu da wuri. Lamarin matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ya zama ruwan dare inda dubbai sun kammala karatu amma basu samu aikin zama a ofis ba.
Duka da zagin me laifi baya cikin aikin ku>>Hukumar ‘Yansandan Najeriya ta gayawa ‘yansandan

Duka da zagin me laifi baya cikin aikin ku>>Hukumar ‘Yansandan Najeriya ta gayawa ‘yansandan

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan babban birnin tarayya, Abuja ta gargadi 'yansandan cewa duka da zagin wanda ake zargi baya cikin aikinsu. An bayyana musu hakane a yayin wani taron karawa juna Sani da aka yi. https://www.youtube.com/watch?v=Misftjbq4_A Akan samu rahotannin jikkata masu laifi ko wanda ake zargi da 'yansanda suka kama daga lokaci zuwa Lokaci.
Ziyarar Kakakin ‘yansandan Najeriya kasar Ingila ta jawo cece-kuce inda mutane ke tambayar ina ya samu kudin zuwa Ingila?

Ziyarar Kakakin ‘yansandan Najeriya kasar Ingila ta jawo cece-kuce inda mutane ke tambayar ina ya samu kudin zuwa Ingila?

Duk Labarai
Kakakin 'yansandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya je kasar Ingila ziyara. Ya wallafa hotunan ziyarar tasa inda yake daukar hotuna a gurare masu daukar hankali. https://twitter.com/BenHundeyin/status/1921144147219517667?t=YNzgqkNgR-RWLdv2uGz5gg&s=19 Saidai mutane da yawa na tambayar nawane Albashinsa da har ya iya zuwa kasar Ingila ziyara?
Ganduje zai dawo jam’iyyar mu ta PDP>>Inji Sule Lamido

Ganduje zai dawo jam’iyyar mu ta PDP>>Inji Sule Lamido

Duk Labarai
Jigo a jam'iyyar PDP tsohon gwamnan jihar Jigawa Alh.Sule Lamiɗo, ya yi hasashen cewa za a samu ɓarkewar rikici mai girma a jam'iyyar APC, inda ya ce nan da ɗa wani lokaci kaɗan jiga-jigai a Jam'iyyar APC, ciki har da shugaban jam'iyya na ƙasa, Dr.Abdullahi Umar Ganduje za su iya komowa cikin jam'iyyar PDP. Lamiɗo ya bayyana haka ne ya yin gangamin taron da aka gudanar a filin taro na Aminu kano Triangle a babban birinin jiha Dutse a lokacin zaɓan shuwagabannin jam'iyyar a matakin jiha. Ya ce "Na tabbatar da cewa waɗanda suka bar jam'iyyar PDP za su dawo, domin APC a cike take da rigima kuma nan ba da daɗewa ba gayyar za ta watse" ~Sule Lamiɗo Ya ƙara da cewa "Ku rubuta ku a jiy, nan da watanni shida da yawa daga cikin waɗanda suka koma j'iyyar APC za su dawo PDP, kuma idan suka y...
Karanta Jadawalin wanda suka halarci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP

Karanta Jadawalin wanda suka halarci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP

Duk Labarai
Ministan Tinubu na Abuja Nyesom Wike ya halarci taron jiga-jigan jam'iyyar PDP na Nijeriya da a ka gudanar a daren Lahadin a Abuja Taron wanda Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya kira da nufin Dinke Barakar da Jami’iyar PDP ke fama da ita ta samu halartar tsoffi da gwamnonin jam'iyyar PDP Da Shuwagabanin kamarMembers na National Working Committee (NWC) a jagoran Shugaban Riko Ambassador Iliya Damagum. GovernorH.E. Senator Bala Abdulkadir Mohammed (Bauchi State) - Chairman H.E Dr. Agbu Kefas ( Taraba State) - Member H.E. Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa State) - Member H.E. Dr. Dauda Lawal (Zamfara State) - Member H.E. Senator Ademola Adeleke, (Osun State) - Member H.E. Pastor Umo Eno Ph.D (Akwa Ibom State) - Member H.E. Dr. Peter Mbah (Enugu State) - Member H.E. B...