Tuesday, January 13
Shadow
Kai Duniya ina zaki damu? Kalli Bidiyon yanda aka yi hira da wata ma’aikaciyar Mutuware inda tace masu sayar da abinci da shahararrun mutane na zuwa ta wanke kudin Gawa ta basu ruwan

Kai Duniya ina zaki damu? Kalli Bidiyon yanda aka yi hira da wata ma’aikaciyar Mutuware inda tace masu sayar da abinci da shahararrun mutane na zuwa ta wanke kudin Gawa ta basu ruwan

Duk Labarai
Wata ma'aikaciyar mutuware ta bayyana yace take sayar da ruwan wankin Gawa. Tace yawanci masu kudi da masu sayar da abinci da sauransu ne ke zuwa su sayi ruwan wankin gawar dan neman Duniya. Tace neman kudi ne yasa ta take wannan bakar sana'a. https://twitter.com/General_Somto/status/2004584482272403942?t=wkLyTkthCWwEoinzjw3zqg&s=19
Yawan kudin da hukumar Kwastam ta tarawa Shugaba Tinubu a shekaru 2, sun fi yawan wanda Kwastam din suka tarawa shugaba Buhari a cikin shekaru 8

Yawan kudin da hukumar Kwastam ta tarawa Shugaba Tinubu a shekaru 2, sun fi yawan wanda Kwastam din suka tarawa shugaba Buhari a cikin shekaru 8

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana yawan kudaden da Hukumar kwastam suka tarawa shugaba Muhammadu Buhari da kuma wanda suka tarawa shugaba Tinubu. Rahoton ya nuna cewa yawan kudaden shigar da Kwastam suka tarawa shugaba Buhari sun kai sama da Naira Tiriliyan 1,400 a cikin shekaru 8 A yayin da shi kuma Tinubu a cikin shekaru 2 kaca Kwastam din sun tara masa kudin shiga sama da Naira Tiriliyan 1,700. Q2 2016: N46.09bn Q2 2017: N139.59bn Q2 2018: N157.62bn Q2 2019: N199.36bn Q2 2020: N195.82bn Q2 2021: N275.81bn Q2 2022: N385.79bn Q2 2023: N326.74bn Q2 2024: N727.12bn Q2 2025: N961.14bn
Kalli Bidiyon: Ministan Kasafin kudi, Atiku Bagudu ya kaiwa Abubakar Malami ziyara inda yace Malami shine silar daukakarsa da Ma gwamnan jihar Kebbi me ci na yanzu

Kalli Bidiyon: Ministan Kasafin kudi, Atiku Bagudu ya kaiwa Abubakar Malami ziyara inda yace Malami shine silar daukakarsa da Ma gwamnan jihar Kebbi me ci na yanzu

Duk Labarai
Ministan Kasafin Kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya bayyanawa Tsohon Ministan shari'a Abubakar Malami cewa shine silar daukakarsa. Ya bayyana masa hakane a yayin da ya kai masa ziyara a gidansa. Sannan yace Malamin kuma dai shine silar daukakar gwamnan jihar Na yanzu. https://twitter.com/KafinHausaa/status/2004601620722766213?t=Udu69Y1AQY4N8cEEAgeNFQ&s=19
Ba kasarka ta UAE ba, Musulunci ya riga zuwa Afrika kamin ya je Madina>>Gimba Kakanda ya mayarwa da Balarabe da yace a wajansu Bakaken Fata suka koyi Addini Martani

Ba kasarka ta UAE ba, Musulunci ya riga zuwa Afrika kamin ya je Madina>>Gimba Kakanda ya mayarwa da Balarabe da yace a wajansu Bakaken Fata suka koyi Addini Martani

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani Balarabe da ya yiwa wani dan Najeriya gorin cewa a wajansu aka koyi addini, ya sha raddi daga wajan Gimba Kakanda. Wani dan Najeriya ne ya nuna rashin jin dadi game da yanda kasar UAE ta taya Kiristoci murnar Kirsimeti. Balaraben dan kasar ta UAE wanda ke amfanin da sunan Imam of Peace ya cewa dan Najeriyar ya kyalesu dan a wajansu aka koyi addinin Musulunci. Saidai Gimba Kakanda yace masa Musulunci ya riga zuwa Afrika kamin yaje Madina ballantana ma kasarsa ta UAE. Y...
Wata Sabuwa: Wannan Bahaushen ya fito yana kira ga Hausawa su tashi su kwace sarauta da Mulki daga hannun Fulani

Wata Sabuwa: Wannan Bahaushen ya fito yana kira ga Hausawa su tashi su kwace sarauta da Mulki daga hannun Fulani

Duk Labarai
Wannan wani Bahaushene da ya bayyana yana kira ga Hausawa da su tashi su kwace mulki da Sarauta daga hannun Fulani. Ya bayyana cewa, Fulani sun yiwa Hausawa kaka Gida da fin karfi inda suka musu kwacen sarauta da mulki. Yayi Kiran Hausawa su tashi su kwaci 'yancinsu daga hannun Fulani. https://twitter.com/BiaPulse/status/2004580409586364860?t=8Fvh8LhuKTsdRL6FmsWrVg&s=19
Tun tuni ya kamata in kawo Khàrì Najeriya amma na bari sai ranar Kirsimeti ne dan ya zama kyautar Kirsimeti>>Inji Trump

Tun tuni ya kamata in kawo Khàrì Najeriya amma na bari sai ranar Kirsimeti ne dan ya zama kyautar Kirsimeti>>Inji Trump

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, tun tuni ya kamata ya kai Najeriya hari, watau Rana Laraba. Amma yace ya jinkirta sai ranar Kirsimeti ne dan harin ya zama waa kyauta ta musamman. Ya bayyana hakane ranar Laraba, Kwana daya bayan kai harin Sokoto da Kwara wanda rahotanni suka ce ba kan 'yan Tà'àddà ya fada ba.
Khàrìn Da Amirka ta kawo Najeriya ba wani abu ne na musamman ba, Sojojin Najeriya ma zasu iya kai irinsa>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Khàrìn Da Amirka ta kawo Najeriya ba wani abu ne na musamman ba, Sojojin Najeriya ma zasu iya kai irinsa>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, harin da kasar Amurka ta kawo Najeriya bata yi kokari ba. Yace Sojojin Najeriya na da kwarewa da makaman da zasu iya kai irin wannan hari. Yace Yana kiran Gwamnati ta yanke hulda da Amurka sannan kuma idan taimakon yaki da ta'addanci take nema ta nema wajan kasashen Pakistan, Turkiyya ko China. Yace dalili kuwa shine shugaban kasar Amirka, Donald Trump a wulakance yake kallon Najeriya