Fitsararriyar Mawakiyar Amurka, Nicki Minaj ta tabbatar da cewa lallai ana Mhuzghunawa Kiristoci a Najeriya kuma zata je majalisar Dinkin Duniya dan ta nuna irin cin kashin da akewa Kiristoci a Najeriyar ita da wakilin Amurka a majalisar
Rahotanni sun bayyana cewa, Fitsararriyar mawakiyar kasar Amurka, Nicki Minaj ta amince zata je majalisar Dinkin Duniya dan bayyana Irin Khisan Khiyashi da akewa kiristoci a Najeriya.
Nicki Minaj zata yi hakan ne bisa goyon bayan wakilin Amurka a majalisar, Mike Waltz.
Tun a baya dai Nicki Minaj ta bayyana goyon bayan ta ga shugaban Amurka, Donald Trump da yace zai kaso hari Najeriya dan maganin masu Mhuzghunawa Kiristoci.
Hakan ya jawo mata yabo da kuma suka daga Amurkawa da yawa.








