Saturday, December 13
Shadow
Gwamnan Katsina ya ba da hutun aiki saboda ziyarar Tinubu

Gwamnan Katsina ya ba da hutun aiki saboda ziyarar Tinubu

Duk Labarai
Gwamnan jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ya ayyana yau Juma'a a matsayin ranar hutu ga ma'aikata domin "tarɓar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu" da ke ziyara a jihar tasu. Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin jawabin da ya gabatar a taron Ranar Ma'aikata. "Ina mai farin cikin shaida muku cewa Shugaba Tinubu zai kawo ziyara Katsina gobe [Juma'a] domin buɗe ayyuka da dama da muka kammala cikin shekara biyu da suka wuce," in ji gwamnan. "Saboda haka, na ayyana goben a matsayin ranar hutu saboda ma'aikata su samu damar haɗuwa da mu wajen tarɓar shugaban ƙasa." A jiya Alhamis ne fadar shugaban Najeriya ta sanar cewa Tinubu na jam'iyyar APC zai kai ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar da ke arewa maso yamma kuma ta tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Yau juma’a an shiga ruɗani a birnin Kano kan sanin ainihin Galadiman Kano na gaskiya bayan da Sarki Sanusi II da Sarki Aminu Ado kowa ya naɗa nasa Galadiman

Yau juma’a an shiga ruɗani a birnin Kano kan sanin ainihin Galadiman Kano na gaskiya bayan da Sarki Sanusi II da Sarki Aminu Ado kowa ya naɗa nasa Galadiman

Duk Labarai
Yau juma'a an shiga ruɗani a birnin Kano kan sanin ainihin Galadiman Kano na gaskiya bayan da masu ikirarin sarautar Kano biyu kowa ya naɗa nasa Galadiman. Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ya jagoranci majalisarsa da hakimai da magoya bayansa naɗa ɗan uwansa Sunusi Ado Bayero, a matsayin sabon Galadiman Kano. Shima Sarkin Kano Muhammad Sunusi ll ja jagoranci tasa majalisar da hakiman da ke masa biyayya da masoya in da ya naɗa ɗan uwan mahaifinsa wato Munir Sunusi, a matsayin sabon Galadiman Kano. Sarautar Galadiman Kano ta rabu biyu ne tun bayan rasuwar marigayi Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi. Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya halarci fadar masarautar Kano da ke Kofar Kudu in da aka Sarki Sunusi ya yi nasa naɗin, yayin da magoya bayan jam'iyyar APC da ke adawa da Gwamnat...
Wata Sabuwa: Sanata Natasha Akpoti ta bani Naira Miliyan 200 dan in kalawa Sanata Godswill Akpabio sharri>>Inji Dr. Duru

Wata Sabuwa: Sanata Natasha Akpoti ta bani Naira Miliyan 200 dan in kalawa Sanata Godswill Akpabio sharri>>Inji Dr. Duru

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Wata farfesa a kasar Amurka me suna Dr. Sandra Duru ta zargi Sanata Natasha Akpoti da nemanta da ta kullawa Sanata Godswill Akpabio sharri tace yana safarar sassan jikin dan Adam. Dr. Sandra Duru ta bayyana hakane a cikin hirar waya data nada da suka yi ita da Sanata Natasha Akpoti. Saidai Sanata Natasha Akpoti tace ita bata ma santa ba, dalili kenan da yasa Dr. Sandra Duru ta mikawa jami'an tsaro hirar da suka yi dan su yi bincike akai. Rahoton yace Sanata Natasha Akpoti ta yi hakanne a yayin da ta ga cewa sharrin da ta ke shirin kullawa kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio na cewa ya nemeta da lalata bai yi nasara ba. Matar wadda kuma 'yar jarida ce tace Sanata Natasha Akpoti bata da wata hujja akan zargin da takewa kakakin majalisar.
Da Duminsa: Kalli yanda Matan Jihar Rivers suka tashi suka kama gabansu yayin da ake tsaka da taro matar shugaban kasa, Remi Tinubu na jawabi, sun ce basa son jin jawabinta, Ance bai kamata su kunyata matar shugaban kasar irin haka ba

Rahotanni daga jihar Rivers sun ce matan jihar sun kunyata, matar shugaban kasa, Remi Tinubu yayin da ake gudanar da wani taro inda ana tsaka da taron suka tashi suka kama gabansu yayin da ta tashi take jawabi. Sun ce basa son jin jawabinta, jawabin matar dakataccen gwamnansu, Simi Fubara suke son ji. https://twitter.com/Jmartinsijere/status/1918268255355150504?t=fyRKau1lIoSZR6mBNTqBOQ&s=19 https://twitter.com/PH_Socials/status/1918254642372460688?t=temFX-6zzhfCPtMH45NXWA&s=19 Da yawa sun jinjinawa matan saboda wannan kokari
Munin Tattalin arzikin Najeriya a yanzu yafi na lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yanci a shekarar 1960>>Inji Shugaba  Bankin Afrika

Munin Tattalin arzikin Najeriya a yanzu yafi na lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yanci a shekarar 1960>>Inji Shugaba Bankin Afrika

Duk Labarai
Shugaban bankin Afrika, AFDB, Dr Akinwumi Adesina ya bayyana cewa, lalacewar tattalin arzikin Najeriya a yanzu ya fi muni fiye da lokacin da aka baiwa Najeriya 'yancin kai a shekarar 1960. Ya bayyana hakanne a wajan wani taro da ya faru a Legas ranar Alhamis. Yace Abinda ake cewa GDP per capital wanda shine ake auna ma'aunin tattalin arzikin kasa dashi a yanzu yana kan Dala $824 ne. Yace a yayin da a lokacin da aka baiwa Najeriya 'yancin kai a shekarar 1960 GDP per Capital yana kan Dala $1,847 ne. Yace hakan ba karamar matsala bace inda yace ya kamata Gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye dan shawo kan wannan matsalar.
Hukumomin kasar Amurka sun nemi a kara musu kwanaki 10 kamin su fitar da bayanan zargin safarar miyagun Kwàyòyì da akewa shugaban Tinubu

Hukumomin kasar Amurka sun nemi a kara musu kwanaki 10 kamin su fitar da bayanan zargin safarar miyagun Kwàyòyì da akewa shugaban Tinubu

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, Hukumar tsaro ta FBI da masu kula da harkar kwayoyi sun nemi a kara musu kwanaki 90 kamin su fitar da bayanai kan shari'ar zargin da akewa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ta Safarar Kwayoyi. Ana zargin a shekarar 1990 ne dai Shugaba Tinubu da wasu mutane 3 Lee Andrew Edwards, Mueez Abegboyega Akande, da Abiodun Agbele suka yi safarar kwayoyi a birnin Chicago na kasar. Wani lauya a kasar Amurka, Aaron Greenspan ne ya nemi wadannan bayanai. Kuma kotu ta nemi hukumomin FBI da DEA su fitar da bayanan inda aka saka ranar 2 ga watan Mayu dan fitar dasu. Saidai yayin da ake dakon jiran wadannan bayanai, wadannan hukumomin sun bayyana cewa basu kammalu ba sai nan da kwanaki 90. Saidai Lauyan Aaron Greenspan ya bayyana cewa, kwanaki 90 ...
ALLURAR CIKIN RUWA: Duk Wadda Take Sona Da Aure Kofa A Bude Take, Kawai Ta Samu ‘Yan ‘Halal Match’ Ta Ba Su Lambarta Su Ba Ni, Domin Ina Bukatar Auŕe, Inji Babba

ALLURAR CIKIN RUWA: Duk Wadda Take Sona Da Aure Kofa A Bude Take, Kawai Ta Samu ‘Yan ‘Halal Match’ Ta Ba Su Lambarta Su Ba Ni, Domin Ina Bukatar Auŕe, Inji Babba

Duk Labarai
ALLURAR CIKIN RUWA: Duk Wadda Take Sona Da Aure Kofa A Bude Take, Kawai Ta Samu 'Yan 'Halal Match' Ta Ba Su Lambarta Su Ba Ni, Domin Ina Bukatar Auŕe, Inji Babba Ina 'yan mata? Kada ku bari wannan damar ta wuce ku! Alhaji Babba dai yana ikrarin shi matashin mai kudi ne. Kuma gashi mutum mai yawan fara'a.
KATSINA BA KORAFI: Gabanin Zuwan Tinubu Jihar Katsina An Hango An Rubuta Katsina Ba Ƙorafi A Allon Da Aka Sanya A Bakin Hanya Duk A Shirye-Shiryen Tarbar Shugaba Tinubu Zuwa Jihar

KATSINA BA KORAFI: Gabanin Zuwan Tinubu Jihar Katsina An Hango An Rubuta Katsina Ba Ƙorafi A Allon Da Aka Sanya A Bakin Hanya Duk A Shirye-Shiryen Tarbar Shugaba Tinubu Zuwa Jihar

Duk Labarai
KATSINA BA KORAFI: Gabanin Zuwan Tinubu Jihar Katsina An Hango An Rubuta Katsina Ba Ƙorafi A Allon Da Aka Sanya A Bakin Hanya Duk A Shirye-Shiryen Tarbar Shugaba Tinubu Zuwa Jihar Hakan na nufin Katsinawa sun gamsu da salon mulkin Tinubu kenan? Menene ra'ayinku?
Atiku Da Tinubu bai kamata su fito takarar shugaba cin Najeriya a shekarar 2027 ba>>Inji Baba Ahmad

Atiku Da Tinubu bai kamata su fito takarar shugaba cin Najeriya a shekarar 2027 ba>>Inji Baba Ahmad

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa, Dr. Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa, da Atiku Abubakar da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai kamata su tsaya takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2027 ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na ChannelsTV. Yace maganar tsayawa takarar Atiku a 2027 bai kamata ba, tunda ya gwada bai yi nasara ba, kamata yayi ya koma gefe ya zama mai bayar da shawara. Yace Tinubu ma haka ya dace dashi musamman ma lura da yanda tattalin arzikin Najeriya ya samu kansa. Yace har Peter Obi duk kamata yayi su hakura in kuma basu hakura ba, 'yan Najeriya su musu ritaya.
An shawarci Atiku cewa kar ya hada kai da El Rufai, domin zai sake yin kuskuren da yayai abaya ne, lokacin daya kai El Rufai wurin Obasanjo amma ya juya masa baya

An shawarci Atiku cewa kar ya hada kai da El Rufai, domin zai sake yin kuskuren da yayai abaya ne, lokacin daya kai El Rufai wurin Obasanjo amma ya juya masa baya

Duk Labarai
An shawarci Atiku cewa kar ya hada kai da El Rufai, domin zai sake yin kuskuren da yayai abaya ne, lokacin daya kai El Rufai wurin Obasanjo amma ya juya masa baya. Atiku ne dai ya gabatar da El-Rufai a wajan Obasanjo wanda daga baya aka bashi mukamin Ministan Abuja amma daga baya adawar siyasa tasa ya rika adawa da Atikun. Saidai yanzu sun sake hadewa.