Tuesday, December 16
Shadow
Ji yanda aka kama wasu da suka sàcè yaro me shekaru 6 suka yi gùndùwa-gùndùwa dashi dan yin tsafin samun kudi a jihar Gombe

Ji yanda aka kama wasu da suka sàcè yaro me shekaru 6 suka yi gùndùwa-gùndùwa dashi dan yin tsafin samun kudi a jihar Gombe

Duk Labarai
A jihar gombe, jami'an 'yanssnda sun kama wasu mutane 8 da ake zargi da hannu a cikin yin garkuwa da kashe wani yaro dan shekaru 6. Wadanda ake zargin sun sae yaronne me suna Muhammad Ibrahim Bulama daga gidan kakansa. Sannan suka masa yankan rago suka raba gawarsa gida biyu suka kaiwa wani matsafi da yace zai musu asirin kudi. Wadanda ake zargin sune Magaji Adamu (Wazam), 45, Babayo Musa, 18 years, Jibrin Muhammad (Alias Ya’Haji), 40, Usman Abubakar Khalla, 37, Sadam Umaru, 28, Idris Dayyabu, 45, Abdulrauf Hussaini, 33,Isiyaku Muhammad, 39. Dukansu sun amsa zarge-zargen da ake musu. Kakakim 'yansandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace zasu ci gaba da bincike da tabbatar cewa an yiwa wadannan mutane hukuncin da ya dace dasu.
Kalli Bidiyo: Tauraron fina-finan Hausa, Horo Dan Mama na shan Tofin Allah Tsine saboda cewa Sheikh Bala Lau ya fito da hujja ya kare kansa kan zargin da ake mass

Kalli Bidiyo: Tauraron fina-finan Hausa, Horo Dan Mama na shan Tofin Allah Tsine saboda cewa Sheikh Bala Lau ya fito da hujja ya kare kansa kan zargin da ake mass

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Abdullahi Dan Mama wanda aka fi sani da Horo Dan mama na ci gaba da shan tofin Allah tsine bayan da yayi kira ga shugaban Izala, Sheikh Bala Lau ya fito ya kare kansa kan zargin da ake masa. Horo Dan mama ya wallafa Bidiyon ta sigar barkwanci yana kira ga Sheikh Bala Lau ya fito da takardu a yi bincike kan lamarin zargin da ake masa. https://www.tiktok.com/@horodanmama3/video/7496234447457570103?_t=ZM-8vq7Bfl2rDC&_r=1 Saidai da yawa sun mai Allah wadai da wannan abu da yayi.
Mahaukaciyar wutar Daji ta tashi a kasar Yahudawan Israyla inda tasa mutane guduwa daga gidajensu

Mahaukaciyar wutar Daji ta tashi a kasar Yahudawan Israyla inda tasa mutane guduwa daga gidajensu

Duk Labarai
Wutar daji da ba'a san daga ina ta fara ba ta tashi a yankunan kasar Israela daban-daban. Hakan yawa dole aka kwashe mutane da yawa daga gidajensu. Ana tsammanin tsananin zafi da iska me kadawa sun taimaka matuka wajan yaduwar wannan wuta. Wutar dai ta farane a ranar 24 ga watan Afrilu kuma tuni an shawo kanta kamar yanda mahukuntan kasar suka sanar.
SO GAMON JINI: Murtala Idris Kenan Wanda Tsananin Farin Ciki Da Murnar Auren Mawaƙi Rarara Da A’isha Humaira Ya Sadaukar Da Bijiminsa, Tare Da Alƙawarin Kai Masa Shi Har Garin Abuja

SO GAMON JINI: Murtala Idris Kenan Wanda Tsananin Farin Ciki Da Murnar Auren Mawaƙi Rarara Da A’isha Humaira Ya Sadaukar Da Bijiminsa, Tare Da Alƙawarin Kai Masa Shi Har Garin Abuja

Duk Labarai
Murtala Idris Kenan Wanda Tsananin Farin Ciki Da Murnar Auren Mawaƙi Rarara Da A'isha Humaira Ya Sadaukar Da Bijiminsa, Tare Da Alƙawarin Kai Masa Shi Har Garin Abuja Murtala ya fito daga Sara ƙaramar hukumar Gwaram dake jihar Jigawa. Ko ya kuke kallon wannan sadaukarwa? Daga Abubakar Shehu Dokoki
Kalli Bidiyo: Ku daina zarginmu idan mukace sai me Kudi muke so, Babu wadda zata so ta fito daga gidan Talauci ta fada gidan Talaka>>Inji Wanan Matashiyar

Kalli Bidiyo: Ku daina zarginmu idan mukace sai me Kudi muke so, Babu wadda zata so ta fito daga gidan Talauci ta fada gidan Talaka>>Inji Wanan Matashiyar

Duk Labarai
Wata Matashiya ta dauki hankula a kafafen sadarwa bayan da ta ce a daina zargin mata masu cewa sai me kudi suke so. Tace babu wadda zata so fitowa daga gidan Talakawa kuma ta auri Talaka. Hakanan tace maza sukan ce sai kyakkyawa suke so dan haka suma mata a daina zarginsu idan sun ce sai mai kudi Kalli Bidiyon ta: kalli anan https://twitter.com/northern_blog/status/1914751317664215386?t=QxvGn1X_nlwcYO63kSMyww&s=19
Kalli Bidiyo: Wannan mutumin yayi ikirarin yin aiki a karkashin Kamfanin Sheikh Bala Lau inda yace an rike masa hakkinsa ba’a biyashi ba

Kalli Bidiyo: Wannan mutumin yayi ikirarin yin aiki a karkashin Kamfanin Sheikh Bala Lau inda yace an rike masa hakkinsa ba’a biyashi ba

Duk Labarai
Wani mutum ya dauki hankula sosai a kafafen sadarwa bayan da yayi zargin cewa yana aiki ne a wani kamfani dake karkashin shugaban Izala, Sheikh Bala Lau amma ba'a biyashi hakkinsa ba. Yace wasu daga cikin abokan aikinsa sun gudu saboda babu Albashi a aikin. Mutum ya bayyana cewa an kaisu aikin tsaron Titin Jirgin kasa ne. Kalli Bidiyon a kasa: https://www.tiktok.com/@najib.zubairu/video/7495804901910465797?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7495804901910465797&source=h5_m&timestamp=1745618943&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&ut...
Gaba daya Albashin mu ya kare a biyab kudin wuta da sakata katin waya>>Inji Kungiyar Kwadago

Gaba daya Albashin mu ya kare a biyab kudin wuta da sakata katin waya>>Inji Kungiyar Kwadago

Duk Labarai
Kungiyar kwadago NLC ta koka da cewa albashin dubu 70 da ake biyan ma'aikata a biyan kudin wutar Lantarki da sayen katin waya yake karewa. Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya bayyana cewa hakanan masu gidajen haya da ababen hawa na haya duk sun kara kudi. Yace zasu hada kai da tawakararsu kungiyar TUC dan kwatarwa da talakawa 'yanci.
Ji yanda dan Najeriya ya cirewa dan sandan kasar Malaysia kunne ta hanyar cizo bayan da aka kamashi da karfin tsiya

Ji yanda dan Najeriya ya cirewa dan sandan kasar Malaysia kunne ta hanyar cizo bayan da aka kamashi da karfin tsiya

Duk Labarai
Wani dan Najeriya ya cirewa dan sandan kasar Malaysia kunne ta hanyar cizo bayan da aka kamashi a wani Asibiti. An kama dan Najeriyar ne a Metro Prima, Kepong, Kuala Lumpur, Malaysia. Shugaban 'yansandan birnin Kuala Lumpur Datuk Rusdi Mohd Isa ya tabbatar da kamen inda yace sun kama dan Najeriyar ne bayan da aka kirasu aka shaida musu cewa wani dan kasar waje ya tayar da hankali a wani Asibiti. Ya kara da cewa, lamarin ya farune ranar Juma'a da misalin karfe 10:03 na safe April 25, 2025. Yace bayan an kama mutumin me shekaru 38, an hadashi da dansanda ya kaishi Ofis inda aka ajiyeshi a bayan mota da ankwa a hannunsa. Saidai a hakanne ya kama kunnen dansandan ta baya ya cizge. Yace an kai dansandan Asibiti yayin da shi kuma wanda ake zargi ana ci gaba da bincike akansa.
Kalli Hotuna: Shugaba Tinubu ya aika wakili zuwa wajan daurin auren Rarara

Kalli Hotuna: Shugaba Tinubu ya aika wakili zuwa wajan daurin auren Rarara

Duk Labarai
Mallam Abdulaziz Abdulaziz Ya Wakilci Shugaban Ƙasa Tinubu Wajen Halartar Ɗaurin Auren Rarara Da A’isha Humaira. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya wakilta mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa, Mallam Abdulaziz Abdulaziz wajen halartar ɗaurin auren shahararren mawaƙin jam’iyyar APC, Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) da amaryarsa, A’isha Humaira. Auren wanda aka ɗaura yau a garin Maidugurin Jihar Borno, ya samu halartar mataimakin shugaban majalissar dattawa ta ƙ...
Bill din wuta da akw kawo mana yayi yawa ba zamu iya biya ba shiyasa zamu koma amfani da Sola>>Inji Fadar shugaba Tinubu

Bill din wuta da akw kawo mana yayi yawa ba zamu iya biya ba shiyasa zamu koma amfani da Sola>>Inji Fadar shugaba Tinubu

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, kudin wutar lantarkin da suke biya a duk shekara ya kai Naira Biliyan 47. Fadar tace dan haka ba zata iya ci gaba da biyan wadannan kudi bane shiyasa shugaba Tinubu ya amince a saka solar. Shugaban Hukumar makamashi ta kasa, Mustapha Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma'a. Yace kuma wannan na kan hanyar kokarin Gwamnati na samar da makamashi wanda baya gurbata Muhalli.