Monday, December 15
Shadow
Kalli Bidiyon cikin jirgin saman da Tawagar Rarara ta tafi Maiduguri a ciki wajan daurin aurensa

Kalli Bidiyon cikin jirgin saman da Tawagar Rarara ta tafi Maiduguri a ciki wajan daurin aurensa

Duk Labarai
A yau an daura auren Shahararren mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara a garin Maiduguri tare da amaryarsa, A'isha Humaira. Wannan Bidiyon yanda tawagarsa data hada da 'yan siyasa ne yayin da suke cikin jirgin sama akan hanyarsu ta zuwa Maiduguri wajan daurin aure. https://www.tiktok.com/@zinariya.tv0/video/7497210704563391750?_t=ZM-8vpW6iyJSA2&_r=1 Muna fatan Allah ya bada zaman Lafiya.
Wata Sabuwa: An gano cewa, Kwankwaso da Peter Obi Tinubu sukawa aiki a zaben 2023 kuma akwai yiyuwar a 2027 ma zasu sake masa

Wata Sabuwa: An gano cewa, Kwankwaso da Peter Obi Tinubu sukawa aiki a zaben 2023 kuma akwai yiyuwar a 2027 ma zasu sake masa

Duk Labarai
Dan fafutuka kuma Lauya, Deji Adeyanju ya yi zargin cewa, Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da dan takarar shugaban kasa na Labour party, Peter Obi, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sukawa aiki a shekarar 2023. Ya bayyana cewa kuma akwai yiyuwar a shekarar 2023 ma zasu sake yi masa. Deji ya bayyana hakane a shafinsa na X inda yake sharhi game da hadakar 'yan Adawa da ake shirin kullawa. Yace idan ana son wannan hadaka ta yi aiki, sai Atiku da Peter Obi sun koma gefe sun bar wanda bai goyon bayan kowa ya jagoranci wannan tafiya. Deji yace amma da wuya Peter Obi ya yadda a yi wata hadaka dashi
Dauda Kahutu Rarara ya Zaɓi Ummi Ibro A matsayin Sabuwar P.A. dinsa Sakamakon Aurensu da Aisha Humaira da ake shirin daurawa yau a jihar Borno

Dauda Kahutu Rarara ya Zaɓi Ummi Ibro A matsayin Sabuwar P.A. dinsa Sakamakon Aurensu da Aisha Humaira da ake shirin daurawa yau a jihar Borno

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wasu Rahotanni dake yawo a kafafen sadarwa sun bayyana cewa, Dauda Kahutu, Rarara ya zabi sabuwar P.A bayan Auren A'isha Humaira. Ga rahoton da muka ci karo dashi. Da Dumi Duminsu Dauda Adamu Kahutu Rarara ya Zaɓi Ummi Ibro A matsayin Sabuwar P.A. dinsa Sakamakon Aurensu da Aisha Humaira da ake shirin daurawa yau a jihar Borno, A wata majiyar Tun kwana biyu kafin yau Rarara Ya nemi Ummi da tazo su tattauna ta yadda zata maye masa Gurbin Aisha Humaira.
Gaba daya na makance na daina gani bayan dana biyewa Snoop Dog muka sha wiwi>>Inji Mawaki Ed Sheeran

Gaba daya na makance na daina gani bayan dana biyewa Snoop Dog muka sha wiwi>>Inji Mawaki Ed Sheeran

Duk Labarai
Mawakin kasar Ingila, Ed Sheeran ya bayyana cewa, sai da ya makance gaba daya ya daina gani bayan da ya biyewa mawakin gambara na kasar Amurka, Snoop Dog suka sha wiwi tare. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta. Ed Sheeran dai ya taba bayyana cewa ya sha wiwi tare da mawakin Najeriya, Burna Boy wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin wanda suka fi shan wiwi da ya taba gani.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fara yakin neman zaben 2028 inda yake neman zama shugaban kasa a karo na 3 duk da kundin tsarin mulkin kasar Amurka ya hana hakan

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fara yakin neman zaben 2028 inda yake neman zama shugaban kasa a karo na 3 duk da kundin tsarin mulkin kasar Amurka ya hana hakan

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fara yakin neman zaben shekarar 2028. A shekarar 2028 ne kasar Amurka zata saken yin zaben shugaban kasa. Sannan kudin tsarin mulkin kasar ya haramta a zabi shugaban kasa sau uku amma duk da haka Trump yace ya gano wata hanyar da zai yi nasara. Dan shugaban kasar, Eric Trump ne da kansa ya fara tallar baban nasa inda ya saka hular dake tallata babban nasa a zaben shekarar 2028. Wata majiya dai tace Trump na kokarin saka mataimakinsa, JD Vance ne ya fito takarar shugaban kasa inda shi kuma Trump din zai masa mataimakin shugaban kasa. Bayan an ci zabe, Trump zai bukaci JD Vance ya sauka inda shi kuma sai ya zama shugaban kasar.
IMF ta baiwa Gwamnatin Tinubu shawarar ta kara kaimi wajan karbar Haraji

IMF ta baiwa Gwamnatin Tinubu shawarar ta kara kaimi wajan karbar Haraji

Duk Labarai
Kungiyar bada Lamuni ta Duniya, IMF ta baiwa Gwamnatin tarayya shawarar cewa su kara kaimi wajan karbar haraji. Wakiliyar kungiyar, Kristalina Georgieva ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a birnin Washington DC. Ta bayyana cewa, ya kamata gwamnatin ta yi amfani da fasahar zamani wajan karbar harajin. Ta bayyana cewa, bayar da shawara irin wannan ya zama dole musamman lura da cewa farashin man fetur da Najeriya ta dogara dashi wajan samun kudin shiga ya fadi a kasuwannin Duniya.
Karya ake mana bamu biya Biliyan 6 ba na diyyar mafarautan Kano da aka kònà>>Inji Gwamnatin jihar Edo

Karya ake mana bamu biya Biliyan 6 ba na diyyar mafarautan Kano da aka kònà>>Inji Gwamnatin jihar Edo

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Edo ta musanta ikirarin kungiyar IPOB dake cewa ta biya Biliyan 6 a matsayin diyyar mafarauta 16 da aka kashe aka Kona a jihar. Kakakin Gwamnatin jihar, Fred Itua yace maganar kungiyar IPOB ba ba gaskiya bace, basu bayar da naira Biliyan 6 a matsayin kudin diyyar kisan wadannan mafarauta da aka kona ba. Yace maganar ta IPOB kawai sun yi tane dan kawo hargitsi da gwara kawunan mutane. Dan haka ya bukaci mutane su yi watsi da wannan magana.
Ji alkawarin da aka yiwa ‘Yan majalisar NNPP da suka koma APC

Ji alkawarin da aka yiwa ‘Yan majalisar NNPP da suka koma APC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan majalisar jam'iyyar NNPP da suka koma jam'iyyar APC an musu alkawari me tsoka. Daga cikin Alkawuran da aka musu akwai maganar cewa, kowanne dan majalisa zai koma kan kujerarsa ba tare da an tsayar da kowa ba yayi takara dashi. Wata majiya daga jam'iyyar NNPP dince ta bayyana hakan. A jiyane dai Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi wasu 'yan jam'iyyar ta NNPP da suka koma cikinta.