Mummunan rikici ya barke a jam’iyyar PDP
Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BoT) ta yi watsi da matakin da shugaban jam’iyyar Iliya Damagum, ya dauka na soke taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, 30 ga Yuni, 2025.
Haka nan kwamitin ya ce matakin da Damagum ya ɗauka na mayar da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar ba shi da tushe a kundin tsarin mulki na PDP.
A wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattun, Sanata Adolphus Wabara ya fitar, ya bayyana cewa "kundin tsarin mulkin PDP na shekarar 2017 ya bayyana ƙarara cewa babu wani mutum ko ɓangare da ke da ikon soke ko ɗage taron shugabannin jam'iyya da aka yanke shawarar gudanarwa a taro na 99 da aka yi a ranar 27 ga Mayu, 2025".
Saboda haka, matakin soke taron da Damagum ya ɗauka ya saɓa wa kundin tsarin jam’...








