Yadda zaka sa mace tunaninka
Idan kana son mace ta rika tunaninka, to ka rika yin wadannan abubuwan:
Ka rika sata dariya: Ya zamana daga lokaci zuwa lokaci kana iya sa budurwarka raha da zata sa ta kyakyace da dariya, hakan zai sa ta rika tunaninka da son kasancewa tare da kai.
Ka zama me kwalliya da tsafta: Ka zama me kwalliya da zama fesfes babu datti a tattare da kai, kana kamshi, hakan zai sa budurwarka ta rika tunaninka.
Ka iya kalaman soyayya: Ya zamana Ka iya kalaman soyayya masu kwantar da hankali da Sata nishadi, Ka iya tadi da yabon budurwarka sosai, hakan zai sa task kasancewa da kai.
Ka zama me kyauta: Ka zamana kana yiwa budurwarka kyauta sosai, hakan ma zai sa ta rika tunaninka da damuwa da kai.
Ka rika bata labarin irin rayuwar jin dadin da ka shirya muku nan gaba: Ka rika bata labarin ir...