Saturday, December 13
Shadow
Babu wanda ya isa ya sauke Sanata Godswill Akpabio daga mukaminsa saboda wannan dan zargin da Natasha tai masa>>Inji Basaraken jihar Bayelsa

Babu wanda ya isa ya sauke Sanata Godswill Akpabio daga mukaminsa saboda wannan dan zargin da Natasha tai masa>>Inji Basaraken jihar Bayelsa

Duk Labarai
Basaraken jihar Bayelsa kuma shugaban sarakunan jihar, Bubaraye Dakolo Agada IV, ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya sauke Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio. Ya bayyana cewa saboda wannan dan zargin da sanata Natasha Akpoti ta yi masa, bai isa ya sa a saukeshi ba. Yace su suna tare da Sanata Godswill Akpabio saboda dansu ne. Yace ya kamata awa Sanata Akpabio adalci kuma a kafa kwamitin bincikw da zai binciki lamarin. Yace Sanata Godswill Akpabio ya kawowa Najeriya ci gaba sosai.
‘Hotuna Da Duminsu: Yansanda sun harbawa masu zanga-zangar goyon bayan sanata Natasha Akpoti barkonon tsohuwa a Abuja

‘Hotuna Da Duminsu: Yansanda sun harbawa masu zanga-zangar goyon bayan sanata Natasha Akpoti barkonon tsohuwa a Abuja

Duk Labarai
Wasu mata sun fita yin zanga-zanga dan nuna goyon baya ga Sanata Natasha Akpoti data zargi kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio da neman yin lalata da ita. Masu zanga-zangar sun je kofar shiga majalisar tarayya ne suna suke yi zanga-zangar acan. Saidai tuni 'yansanda suka watsa musu barkonon tsohuwa inda suka watsa su. Hutudole ya fahimci cewa, masu zanga-zangar sun je kofar majalisar ne da misalin karfe 8 na safiyar yau, Laraba.
Tafiye-Tafiyen da Tinubu yayi sun kawowa Najeriya zuba jari na dala Biliyan $50

Tafiye-Tafiyen da Tinubu yayi sun kawowa Najeriya zuba jari na dala Biliyan $50

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya tace tafiye-Tafiyen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke yi sun kawowa Najeriya zuba jarin dala Biliyan $50. Ministar masana'antu, Jumoke Oduwole ce ta bayyana hakan a wata ganawa da aka yi da ita ranar Talata a Abuja. Tace shugaban ya halarci taruka irin su na manyan kasashe mafiya karfin tattalin arzikin a Duniya watau G20 wanda kuma kamfanoni da yawa suka hadu a wajan. Tace wakilan wadannan kamfanoni da masu zuba jari sun kawo ziyara Najeriya kuma sun ga damar zuba jari kuma sun bayar da tabbacin zasu zo su zuba wannan jari a Najeriya.
Kai da kace idan ka zama shugaban kasa zaka halasta shan Wìwì shine kake da bakin cewa musulmai Jahilai? Kaine babban dakiki>>Reno Omokri ya mayarwa Sowore martani

Kai da kace idan ka zama shugaban kasa zaka halasta shan Wìwì shine kake da bakin cewa musulmai Jahilai? Kaine babban dakiki>>Reno Omokri ya mayarwa Sowore martani

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya mayarwa da dan takarar shugaban kasa, kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore martani kan zagin da yawa gwamnonin Arewa saboda sun bayar da hutun makaranta saboda zuwan watan Ramadan. Sowore yace Gwamnonin jihohin Kebbi, Katsina, Bauchi da kano dakikai ne kuma sakarkarune saboda sun bayar da hutun makaranta dalilin zuwan watan Azumin Ramadana. Inda ya bayar da hujjar cewa ko Saudi Arabia bata kulle makarantu saboda zu...
EFCC ta kama tsohon Gwamnan Akwa-Ibom bisa zargin satar Naira Biliyan 700

EFCC ta kama tsohon Gwamnan Akwa-Ibom bisa zargin satar Naira Biliyan 700

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kama tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Udom Emmanuel bisa zargin satar Naira Biliyan 700 a yayin mulkinsa. Tsohon Gwamnan ya shiga komar EFCC ne a yayin da yace ofishin hukumar dan amsa gayyatar da suka masa kan zargin Rashawa da cin hanci. Wata kungiyar dake yaki da Rashawa da cin hanci me suna (NACAT) ce ta shigar da korafi akan tsohon gwamnan. Kungiyar ta yi korafin cewa, tsohon gwamnan ya karbi Naira Tiriliyan 3 a zamanin da yayi mulki tsakanin shekarun 2015 da 2023 daga gwamnatin tarayya. Saidai ya tafi ya bar jiharsa da bashin Naira Biliyan 500 sannan akwai ayyukan da ake yi na jihar na Naira Biliyan 300 wanda bai biya ba sanan ana zargin yayi sama da fadi da naira Biliyan 700. Zuwa yanzu dai hukumar EFCC bata ce uffan kan w...
Farashin gangar man fetur a kasuwar Duniya ya fado kasa inda hakan kewa hanyar samun kudin Gwamnatin Najeriya barazana

Farashin gangar man fetur a kasuwar Duniya ya fado kasa inda hakan kewa hanyar samun kudin Gwamnatin Najeriya barazana

Duk Labarai
Farashin gangar man fetur na Bonny Light wanda Najeriya ke sayarwa a kasuwar Duniya ya fadi kasa zuwa Dala $73.53 akan kowace ganga. A baya, 15 ga watan Janairu ana sayar da gangar man akan dala $84.02 kowace ganga wanda hakan ya nuna an samu asarar dala $10.6 a farashin bayan fadduwarsa. Hakan zai iya zama barazana ga hanyar samun kudin gwamnatin Najeriya dan aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025. An shirya kasafin kudinne akan kiyasin farashin kowace gangar man fetur din za'a sayar da ita akan dala $75 inda ake tsammanin rika samun gangar man miliyan 2.06 kullun. Ana tsammanin samun kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan N36.35 wanda kuma kaso 56 na cikin kudin ana tsammanin su fito ne daga hadahadar man fetur. Hakan na nuna cewa farashin kasuwar man a yanzu yayi kasa d...
Ni da kwankwaso bama gaba, muna zama Inuwa daya mu tattaunawa batutuwa>>Malam Ibrahim Shekarau

Ni da kwankwaso bama gaba, muna zama Inuwa daya mu tattaunawa batutuwa>>Malam Ibrahim Shekarau

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shakarau ya bayyana cewa shi da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso basa gaba. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi ta kafafen sada zumunta. Malam Ibrahim Shekarau yace yawanci matsalolin da suka faru tsakaninsa da Kwankwaso ba laifin ko daya daga cikinsu. Yace misa a APC, NNPP ce ta kawo kaso 60 cikin 100 na wakilan Jam'iyyar daga Kano amma da aka tashi saboda Kwankwaso yana Gwamna sai aka bashi kaso mafi tsoka. Yace a PDP ma abinda ya faru kenan. https://www.tiktok.com/@usmansolo/video/7477899548837367045?_t=ZM-8uQDuHsBZji&_r=1 Ya kara da cewa, suna zama inuwa daya da Kwankwaso su tattauna batutuwa.