Najeriya ta ƙara yawan man da take haƙowa – Rahoto
Najeriya ta ƙara yawan man fetur da take haƙowa zuwa ganga 70,000 a kowace rana fiye da adadin da ƙungiyar OPEC ta sanya mata, kamar yadda nazarin kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nuna.
A cewar nazarin, man da ƙasashe mambobin ƙungiyar OPEC - ta masu arzikin man fetur - su ka fitar a watan Fabrairu ya ƙaru, inda Iran ke kan gaba, duk da ƙoƙarin da Amurka ke yi na daƙile fitar da man.
Najeriya ta ƙara adadin man da take fitarwa da ya zarce adadin da ƙungiyar ta ware mata.
Ƙungiyar ta OPEC ta haƙo gangan miliyan 26 da 74,000 a kowace rana a watan da ya gabata, inda aka samu ƙarin ganga 170,000 a kullum idan aka kwantanta da watan Janairu, a cewar nazarin na Reuters.
Ƙungiyar OPEC+ - wadda ta haɗa da ƙasashen OPEC da Rasha da sauran ƙawaye - na son rage yawan man da suke h...







