Saturday, December 6
Shadow
Da Duminsa: Ministan Abuja, Wike ya hana ma’aikatan Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja amfani da wayar hannu bayan da Bidiyon rikicinsa da sojan ruwa ya yadu

Da Duminsa: Ministan Abuja, Wike ya hana ma’aikatan Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja amfani da wayar hannu bayan da Bidiyon rikicinsa da sojan ruwa ya yadu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya haramta amfani da wayar hannu bayan da Bidiyon rikicinsa da wani soja ya bayyana. A wata sanarwa da aka fitar a ma'aikatar ta kula da babban birnin tarayya Abuja, tace daga ma'aikaci na mataki na 14 zuwa kasa, kada a sake ganin wani ya je wajan aiki da wayarsa. Sahara Reporters tace lamarin ya kawo rudani a ma'aikatar inda da yawan ma'aikatan hukumar abin ya basu mamaki. Tuni dai kungiyoyin fafutuka dana kare hakkin bil'adama suka rika Allah wadai da wannan mataki da kuma fadin cewa dakile fadar albarkacin bakine.
Ta yiwa Dangin Tsohon Mijinta Gargadin kada su rabata da Diyarta a Tiktok, saidai da yawa na tambayar Dangin Tsohon Mijin nata na yin Tiktok ne?

Ta yiwa Dangin Tsohon Mijinta Gargadin kada su rabata da Diyarta a Tiktok, saidai da yawa na tambayar Dangin Tsohon Mijin nata na yin Tiktok ne?

Duk Labarai
Wannan matar ta wallafa Bidiyo inda take yiwa Dangin tsohon Mijinta gargadi a Tiktok cewa su kiyayi kokarin rabata da Diyarta. Saidai da yawa na ganin cewa ba ta hanyar Tiktok ne ba ya dace ta aika da irin wannan sakon ba. https://www.tiktok.com/@694418salma/video/7571400454135926023?_t=ZS-91Kq8Av4yzh&_r=1
Rahotanni sun ce, Donald Trump ya fasa kawowa Najeriya Khari, Takunkumi zai kakaba mata

Rahotanni sun ce, Donald Trump ya fasa kawowa Najeriya Khari, Takunkumi zai kakaba mata

Duk Labarai
Wani dan majalisar kasar Amurka, Bill Huizenga ya bayyana cewa, Shugaban kasarsu, Donald Trump da wuya ya kawowa Najeriya hari. Yace maganar da Trump yayi, ya yi tane cikin bacin rai da damuwar asarar rayukan da ake yi a Najeriya. Yace amma Trump takunkumi ne zai kakabawa kasar da masu mulkarta wanda hakan zai fi kawo hari amfani. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV. Yace Trump ba mutum ne me son tashin hankali ba saboda a baya ya baiwa sulhu da zaman lafiya muhimmanci fiye da tashin hankali dan haka ba zai kawo Hari Najeriya ba.
Zhagin da Wike yawa matashin soja cin fuska ne ga Sojan, dama shugaba Tinubu>>Inji Buratai

Zhagin da Wike yawa matashin soja cin fuska ne ga Sojan, dama shugaba Tinubu>>Inji Buratai

Duk Labarai
Tsohon Shugaban sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, zagin da Ministan Abuja, Nyesom Wike yawa matashin soja da ya hanashi shiga wani Fili dan ya rusashi cin fuskane. Buratai yace dolene a rika girmamawa da kuma sanya jami'an soji a gaba a kasarnan. Yace tsaro shine ke zuwa farko kuma zagin da Wike yawa matashin sojan cin fuskane da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sojan da hukumar sojojin Najeriya. Buratai yace dolene Wike ya fito ya baiwa matashin sojan hakuri, da shugaba Tinubu, dama Hukumar soji. Yayi kira ga shugaba Tinubu da ya dauki matakin da ya dace akan lamarin. Wike dai ya zagi wani matashin soja ne da ya hanashi shiga wani fili wanda na sojoji ne dan hana ci gaba da gini a filin, sojan yace an bashi umarnine.
Akwai Hanyoyin Shigowa Najeriya guda 1,978 amma guda 84 ne kawai jami’an tsaro ke gadi>>Majalisar Tarayya ta koka

Akwai Hanyoyin Shigowa Najeriya guda 1,978 amma guda 84 ne kawai jami’an tsaro ke gadi>>Majalisar Tarayya ta koka

Duk Labarai
Dan majalisar wakilai Hon. Isa Mohammed Anka wanda shine shugaban Kwamitin majalisar wakilai dake kula da iyakokin Najeriya ya koka da cewa akwai hanyoyin Shigowa Najeriya daga kasashen waje guda 1,978 amma guda 84 ne kadai jami'an tsaro ke kula dasu. Ya bayyana hakane ranar Talata a Abuja wajan kaddamar da kwamitin na wucin gadi. Ya kara da cewa, wannan matsalar itace tasa ake samun yawan safarar mutane da miyagun kwayoyi da makamai da sauran abubuwan laifi. Yace abinda yasa Gwamnati bata iya samar da tsaro sosai a wadannan hanyoyin shigowa Najeriya sun hada da karancin kudi, da sarkakkiyar hanyoyin da karancin ma'aikata. Ya jinjinawa jami'an Kwastam, dana Immigration wajan kokarin da suke na kare Najeriya akan iyakoki inda yace akwai bukatar hadin kan sauran jami'an tsaron N...
Yawancin Talakawan Najeriya basa samun Tallafin da Gwamnatin tarayya tace tana bayarwa>>Inji Bankin Duniya

Yawancin Talakawan Najeriya basa samun Tallafin da Gwamnatin tarayya tace tana bayarwa>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
Bankin Duniya ya fitar da rahoto kan yanda ake raba tallafin rage radadin Talauci ga talakawa. Bankin yace kaso 44 cikin 100 ne kacal na mutanen da aka ce ana baiwa tallafin ke samun sa. Bankin yace kuma ko abincin da ake ciyar da dalibai ya kamata a karashi. Hakan na zuwane bayan da ministan kudi Wale Edun yace sun raba naira 25,000 ga mutane Miliyan 8.5 inda ya kara da cewa akwai sauran mutane Miliyan 6.5 da zasu biya nan da karshen shekara. Bankin Ya nuna damuwa kan yanda Najeriya ke kasancewa tana dogaro da kasashen waje wajan samun kudin da zata tallafawa Talakawanta.
Sojan Najeriya da ya hana Ministan Abuja, Nyesom Wike shiga waja dake gini dan ya rusashi nata shan yabo wajan ‘yan Najeriya

Sojan Najeriya da ya hana Ministan Abuja, Nyesom Wike shiga waja dake gini dan ya rusashi nata shan yabo wajan ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Sojan Ruwan Najeriya, Lieutenant A.M. Yerima na shan yabo bayan Tirka-Tirkar da suka yi da ministan Abuja, Nyesom Wike kan sai ya shiga wajan wani gini ya hana amma sojan ya hanashi shiga. Wike ya kira har shugaban tsaro gaba daya na kasa amma Sojan yawa Shugaban bayanin cewa na sama dashi ne ya sashi wannan aiki. Saidai Wike ya koma yana zagin sojan da cewa, wawa ne amma sojan yace shi ba wawa bane. Wani daga cikin yaran Wike ya gayawa sojan cewa ba zaka yi shiru ba oga na magana kana magana, Shina Wike din yace masa yayi Shiru amma yace ba zai yi shiru ba. Lamarin ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta inda da dama suka yabawa sojan. Saidai wasu daga cikin yaran Wike sunce sojan ya sabawa ka'idar aiki inda suke cewa hakan daidai yake da yunkurin yin juyin mulki. ...
Kalli Bidiyon: Tauraron fina-finan Hausa, KB International ya fito yayi bayani bayan Bidiyonsa ya bayyana yana cewa, zai iya yin Tallar Ghiya akan Naira Miliyan 50

Kalli Bidiyon: Tauraron fina-finan Hausa, KB International ya fito yayi bayani bayan Bidiyonsa ya bayyana yana cewa, zai iya yin Tallar Ghiya akan Naira Miliyan 50

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, KB International ya fito yayi magana bayan da Bidiyonsa ya bayyana aka ga yana cewa zai iya yin tallar Giya akan Naira Miliyan 50. KB a Bidiyon jawabinsa yace datse Bidiyon aka yi inda yace suna maganane kuma wasa ake. Ga cikakken bayaninsa kamar haka: https://www.tiktok.com/@kb_international/video/7571074899826035976?_t=ZS-91JcALCMqkj&_r=1
Wasan cin kofin Kwallon kafa na Duniya na 2026 shine na karshe da zan buga>>Inji Cristiano Ronaldo

Wasan cin kofin Kwallon kafa na Duniya na 2026 shine na karshe da zan buga>>Inji Cristiano Ronaldo

Duk Labarai
Tauraron da kwallon kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa, wasan cin kofin kwallon kafa na Duniya na shekarar 2026 shine na karshe da zai buga. Ronaldo ya bayyana hakane a waa hira da aka yi dashi daga kasar Saudiyya a wajan wani taro na yawon bude ido da zuba hannun Jari. Hakanan Ronaldo ya sanar da cewa, nan da shekaru 2 zai daina buga kwallonnkafa.