Na bar Gidanmu ina da kananan Shekaru sosai kuma banda Ko Sisi amma yanzu Allah ya min daukaka da Arziki>>Inji Rahama Sadau
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta bayyana cewa tana da kananan shekaru sosai ta bar gidansu ta shiga harkar film a lokacin bata da ko sisi.
Tace Amma cikin Ikon Allah sai gata ta samu Daukaka da Arziki har ta dauki wasu aiki.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyo inda take karfafa 'ya'ya mata su bi burin zuciyarsu sannan su nuna jajircewa.
https://www.tiktok.com/@rahamasadaufanspage0/video/7570452687980907794?_t=ZS-91HlFZW2Ajp&_r=1








