Tuesday, March 31
Shadow
Kalli Bidiyon:Muna kiran da a saki Umar da ya yi aikata-aika a Chiranchi Dorayi, saboda ga masu laifi nan da yawa ana yafe musu>>Inji Wannan matashin

Kalli Bidiyon:Muna kiran da a saki Umar da ya yi aikata-aika a Chiranchi Dorayi, saboda ga masu laifi nan da yawa ana yafe musu>>Inji Wannan matashin

Duk Labarai
Wani matashi ya bayyana inda yayi kiran da a saki wanda ake zargi da yiwa uwa da 'ya'yanta aika-aika a Kano. Ya bayyana cewa dalilinsa shine Umar ya saduda kan abinda ya aikata. Sannan kuma akwai masu laifi da yawa da aka yafewa amma gashi shi an tsareshi. https://www.tiktok.com/@dandambu5/video/7598232906288450824?_r=1&_t=ZS-93JDKG19OUa
Gwamnatin tarayya ta kwace mukamin Jakadancin data baiwa Usman Nasamu Dakin Gari

Gwamnatin tarayya ta kwace mukamin Jakadancin data baiwa Usman Nasamu Dakin Gari

Duk Labarai
A daren jiyane dai gwamnatin tarayya ta bayyana Usman Nasamu Dakin gari a matsayin jakadan Najeriya a kasar Turkiyya. Saidai a yau da Safiyar Juma'a, Gwamnatin ta bayyana kwace wannan mukami. Zuwa yanzu dai ba'a bayyana dalilin Gwamnatin na kwace wannan mukami ba. Duka sanarwar nadashi da kwace mukamin ta fito ne daga bakin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga. Ana tsammanin nan ba da jimawa ba, shugaba Tinubu zai kai ziyara kasar ta Turkiyya.
Kalli Bidiyon: Allah ya min Kyau, da haka ba zan auri talaka ba, Talakawan ma neman tsari suke da Talauci>>Inji Wannan Matar

Kalli Bidiyon: Allah ya min Kyau, da haka ba zan auri talaka ba, Talakawan ma neman tsari suke da Talauci>>Inji Wannan Matar

Duk Labarai
Wannan budurwar ta bayyana cewa bata son Auren talaka. Ta bayyana cewa, Talakawan ma neman tsari suke da Talauci. Tace kuma Allah ya mata kyau dan haka ba zata auri talaka ba. Tace kuma duk wanda ya zageta to shima Talakane. https://www.tiktok.com/@aresheenty0/video/7597776741293149448?_r=1&_t=ZS-93J5MBjF889
Kalli Bidiyon: Yadda tasa Mijinta yakewa Uwar gidansa da iyayen uwargidan rashin Arziki ya jawo cece-kuce sosai

Kalli Bidiyon: Yadda tasa Mijinta yakewa Uwar gidansa da iyayen uwargidan rashin Arziki ya jawo cece-kuce sosai

Duk Labarai
Wani Bidiyo da aka ga wata mata tana sa mijinta cewa ya zagi surukansa na wajan uwargidansa ya dauki hankula sosai. A Bidiyon an ji matar tana cewa mijin nata yayi abubuwa na ban mamaki kuma yana ta yi. Da yawa dai sun yi Allah wadai da wannan Bidiyon inda suke zargin cewa ta Asirceshine. https://www.tiktok.com/@dan_sarkeey_kilishi/video/7598195809896664341?_t=ZS-93INw2rBzMG&_r=1 https://www.tiktok.com/@sankasanka6447/video/7598111682736557320?_t=ZS-93IOfNEEXyq&_r=1 Saidai tuni matar ta goge Bidiyon inda tace wasa ne suke. https://www.tiktok.com/@mami999993/video/7598285672629161236?_t=ZS-93IOxsNmINt&_r=1
Kalli Bidiyon: Yanda wata ‘yar kasar China ta yi wakar Hausa da Bilal Villa

Kalli Bidiyon: Yanda wata ‘yar kasar China ta yi wakar Hausa da Bilal Villa

Duk Labarai
'Yar kasar China me sunan SillyMusic ta yi wakar More tare da Bilal Villa. An ga Bidiyon su suna wakar tare inda suke kuma rawa a Studio. https://www.tiktok.com/@sillymusic_/video/7597943731903417608?_t=ZS-93IJJOuuZ29&_r=1 A wani Bidiyo kuma, An ga Bilal Villa na koya mata wakar dalla-dalla. Lamarin ya kayatar sosai. https://www.tiktok.com/@mahamman3/video/7598063960050421010?_t=ZS-93IMq1FCnuz&_r=1
Kudaden da Abubakar Malami ya sata sun fi wanda EFCC ta gano yawa>>Inji Abdurashid Maina

Kudaden da Abubakar Malami ya sata sun fi wanda EFCC ta gano yawa>>Inji Abdurashid Maina

Duk Labarai
Tsohon shugaban hukumar Fansho ta kasa, Abdulrashid Maina yayi zargin cewa kudaden da tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami ya sata sun fi Naira Biliyan 212 da EFCC ta gano yawa. Yace yasan hakane saboda shi aikinsa ne gano kudaden sata. Ya nemi a bashi aikin binciken Malami inda yace sai ya gano kudaden da ya sata duka. Yace amma Biliyan 212 ba komai bane cikin kudaden da Malami ya sace. https://twitter.com/i/status/2014358615449096320
An fara Magudun zaben shekarar 2027>>Atiku Abubakar ya koka

An fara Magudun zaben shekarar 2027>>Atiku Abubakar ya koka

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya koka da cewa, an fara magudin zaben shekarar 2027. Ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta inda yace an fara hakannne ta hanyar kaucewa gyaran dokar zabe. Ya zargi majalisar tarayya da kaucewa gyara dokar zabe wadda zata sa kada a maimaita kuskuren da aka tafka a zaben shekarar 2023. Atiku yace idan ba'a gyara dokar zaben ba ba lallai a samu sakamakon zabe sahihi a zaben shekarar 2027 ba.